“Rayuwar duniya ba komai ba ce sai wasa da wargi. Lahira – wannan ita ce rayuwa ta hakika, in da sun san haka. (Suratul – Ankabut, aya ta 64)
“Ya ku mutane! Alkawarin Allah gaskiya ne. Kada rayuwar duniya ta rude ku kuma kar mai rudi ya rude ku a cikin al’amarin (bin) Allah.” (Sura Fatir, aya ta 5)
“Ku sani cewa rayuwar duniya wasa ce, da shantakewa, da ado, da alfahari a tsakaninku da kuma gasar tara dukiya da ‘ya’ya. Kamar misalin ruwan sama ne (wanda a sakamakonsa) yabanya ta fita kyawunta ya burge manoma, sannan sai ta bushe ka ganta ta koma ruwan dorawa sannan ta zama karmami (a warwatse). A ranar lahira akwai azaba mai tsanani da kuma gafara daga Allah da kuma yardarSa. Rayuwar wannan duniya ba komai ba ce face jin dadi na rudi.” (Suratul Hadid, aya ta 20)
“An kawata wa mutum tsananin sha’awa ga mata da ‘ya’ya, da tarin (dukiya ta) zinare da azurfa, da dawakai na kawa, da dabbobi da gonaki. Wadannan jin dadi ne na rayuwar duniya. Amma ga Allah kyawun makoma yake.” (Sura Al’Imrana, aya ta 14)
“Daga cikinsu kuma akwai masu cewa ‘Ya Ubangijinmu, ka ba mu kyakkyawa a duniya da kuma kyakkyawa a lahira, kuma ka tsare mu daga azabar wuta.” (Suratul Bakara, aya ta 201)
“Saboda haka Allah ya ba su sakamako na duniya da kuma mafi kyawon sakamakon lahira. Allah yana son masu kyautatawa.” (Sura Al’Imrana, aya ta 148)
“Akwai bushara gare su a rayuwar duniya da kuma a lahira. Babu sauyi a maganar Allah. Wannan shine rabo mai girma.” (Sura Yunus, aya ta 64)