Daya daga cikin manyan alamu ga musilmi da ya sami yardar Allah shine kwanciyar hankali. Hakika, Allah ya halicci dalilai da albarkoki da dama da suke sa musulmi walwala da farin ciki.
Jin cewa Allah wanzajje kuma Mai iko ne yakan sa mutum farin ciki mai dorewa. Duk mai la’akari da ikon Alllah maras iyaka, ilimi da ikon da ya buwayi sama da kasa, to hakika, ya mallaki tunani mai zurfi kamar yadda imanin kwanrai ya tanada. Ikon Allah maras iyaka shi ke raya ruhin dan Adam. Domin Allah Ubangiji tare da iko da kuma gwanintarsa wajen tsara halittatu iri-iri, shi yasa yake tsara halittar kome a mafiya kyawawan siffofi. Duk wqanda yake la’akari da hallitun Allah mabanbanta juna, hakan zai albarkaci tare da fadakarwa gameda nuna halaye na gari wadanda suka dace da Alkurani ta hanyar gabatar da kyawawan ayyuka wadanda Allah yake so. Gushewar tsoro da bakin ciki ga musulmi shine tushen farin cikinsa.
A ayata 69 ta suratul Ma’ida, Allah ya kore tsoro da bakin ciki ga siffar muninai: “Lalle ne wadanda suka yi imani da wadanda suka tuba (Yahudu) da karkatattu da Nasara, wanda yayi imani da Allah da ranar Lahira, kuma ya aikata aiki na kwarai, to babu tsoro a kansu, kuma ba su zamo suna bakin ciki ba”.
Ga musulmi, duk abinda ya ya faru Alheri ne gareshi. Abu mafi mahimmanci kawai shine ya zamo mai mika wuya ga Allah. Babu abinda zai faru ya cutar da mumini a sarari ko a boye. Koda ya cutu a zahiri, to sakamakon karshe zai zama Alheri a gareshi. Alkurani yana nuni da cewa a koda yaushe masu karyatawa suna gwagwarmaya ne da musulmi kuma kullum suna dana tarko ga muninai. An sha kulle musulmai ba dalili, an sha raunatawa ko ma kashe su. To amma duk da matsannancin yanayin da suka sami kansu a ciki, muddin suna sane cewa haka Allah ya kaddara musu, daga Alheri zuwa sharri, hakan yana nuni da cewa muninai suna cikin hayyaci, walwala da kuma sadaukar da kai. Mika wuya ta hanyar biyayya ga Allah dalili ne na kwnaciyar hankalin muninai.
Kamar yadda ya sauka a wannan ayar, “Kuma rayuwar duniya, bata zama ba, face wasa da shagala, kuma lalle ne lahira ce mafi Alheri ga wandanda suka yi takawa. Shin ba zakuyi hankali ba? (Suratul An’am, 32). Muminai suna fadake cewa rayuwar duniya ta wucin gadi ice kawai; kuma cewa a lahira ne rayuwar gaske take. Wannan tsagwaron gaskiya da Allah ya saukar a Alkur’ani shine tushen farin cikin musulmi. Wannan karfin imani shi ke karawa musulmi son lahira. Hakan kuma shi ke karfafa fafutukar nemen aljanna ta hanyar samun yardar Allah.
Yin tanadi ga rayuwar lahira, muhimmin al’amari ne wajen karawa mumini himma. Domin duk wanda a ko da yaushe yake cikin tanadi ga rayuwa ta har abada, zai zama fadakakke, kuma yadda yake nazartar al’amura zai dace da abinda ubangiji ya saukar a Alhur’ani.
A Alkurani Allah yana bawa muminai dadadan labaru na duniya da lahira. Da yardar Allah, muminin mutum ne wanda kome yake gudana domin shi kuma wanda ko wane Alheri yake riskarsa. Akan jarrabe shi a takaitacciyar rayuwar duniyan nan, ta haka kuma yake kusantar lahira. Da’a ta gaskiya ga Allah, matsananciyar kauna, kwadayin lahira, tsoron wuta da kuma neman yardar Allah da son Aljanna duk suna gwada cewa musulmi mai fatar alheri da zautuwa ne.