ADNAN OKTAR: A Halin Gaskiya Kungiyar Matsafa ta Freemasonry zasu ga Canje Canje a cikin Shekaru Kadan Masu zuwa,Kungiyar su zata yi Rauni sosai,Ina Nufin zasu Musulunta ,bugu da kari Zamu Mayar da Gidajen Tsafin su Zuwa Masallatai in Allah ya Yarda. Kuma za’a samu Kyakyawar Zamantake wa.Kuma wannan Manyan Kyawawan Gidaje da suka gina na Tsafi zamu mayar dasu Wurin Ibada wato zasu zamo masallaci da yardan Allah.Kuma zasu zama Yan’uwan mu, za’a zauna lafiya dasu da kwanciyar hankali, saboda gane gaskiya da sukayi da kubuta daga hannun shaidan mai hallakarwa,Kuma zasu Tabbata cikin Natsuwa da Fahimta. Misalin a Wannan lokacin Manyan Matsafan,Masu Girma da Mabiyan su zasu zo su Ziyarace ni, In Allah ya yarda. Kuma zasuyi Farin Ciki Ma’ana Zasuyi Murna da Wannan Ziyarar ‘’kuma Za suce’’Zamu yi taka tsantsan da duk abinda ya sabawa koyarwar Addinin musulunci, Kuma zamu Tabbatar da cewa sun Fahimci Addini, zasu nemi taimakon mu wajen neman Ilmin Addini Musulunci, kuma zasu koyi Karatun Alkur’ani lalle zamu Taimaka masu akan haka ,Saboda guje masu bazai amfane mu ba. Misali Annabi Musa (AS) bai gudu ba, zuwa yayi Fadan Fir’auna ya Fada mashi Kalmomin Ubangiji. ya kuma Bayyana mashi Hukuncin Addini. Shima Annabi Ibrahim (AS) yaje wajen Nimrud yayi mashi wa’azi akan Musulunci. I dan muka dawo kan Maganar Kungiyar Matsafa ta Masonic,Duk yaram mu ne ,kuma yan kasar mu, kuma suma halittar Allah ne a bayan kasa,kuma suna daga cikin zuriyar Annabi Adam (AS).Muna masu fatan Alheri tare da samun Shiriya ta Gari. Duk Lokacin da Yan Kungiyar Matsafa ta Masonic suka Shiga Musulunci to Daga Ran nan Addinin Musulunci ya cimma burin sa na mamaye duniya baki daya in Alllah ya Yarda.