Babban dalilin samun rarraba a tsakanin musulmi a tsawon shekaru da kuma irin tashin hankali da zaluncin da a ke wa musulmi a sassan duniya daban daban, shi ne cewa wasu musulmin sun dauka rike sallah kadai da azumi da zuwa hajji sun ishe su addini, don haka ba ruwansu da al’amuran da ke da bukatar mika wuya da sadaukarwa domin ba abin da ya dame su kamar holewa da jin dadin rayuwar ni’ima da suke ciki, ba sa ko tunani game da matsalolin da ‘yan uwansu musulmi suke fuskanta a sassan duniya.
Musulmi mutane ne masu tsarkin zuciya da kyakkyawan tunani. Daya daga cikin halayen musulmi shine ba sa kallon sauran mutane ta mahangar jinsi ko al’ada, ko matsayin mutum a cikin al’umma ko kuma kowane irin ma’aunin bambanci na duniya. Allah ne kadai ya san matsayin kowane mutum ta fuskar takawa, imani da kuma kusancinsa ga Allah mahalicci. Don haka Allah ya haramta wa muminai masu imani yin maganganu sabanin haka. Don mutumin da ya ce “Na yi imani” to ya zama lalle mu kyautata zato a gareshi tare da taimako da karfafarsa a duk lokacin da yake bukatar hakan.
“Muminai maza da muminai mata mataimakan juna ne. Suna umarni da kyakkyawa kuma suna hani da mummuna, sannan suna tsaida sallah, da bada zakka kuma suna bin umarnin Allah da manzonSa. Wadannan Allah zai yi musu rahama. Allah mabuwayi ne, mai hikima.” (Sura Tauba, aya ta 71)
“Kafirai mataimakan juna ne. In ba ku aikata ba fitina za ta afku a bayan kasa da barna mai yawa.” (Suratul Anfal, aya ta 73)
Musulmi a musulunci cike suke da shu’urin soyayya, da aminci inda suke zaune cikin fahimta da son juna. Duk al’ummar da ke da irin wadannan dabi’u ta fi saurin habaka da samun ci gaba. Har ila yau, wani babban abu shine wadanda ke kokari tare da karfafa hadin kai da son juna Allah ya yi musu alkawarin taimako da karfafawa. Shi ya sa a ayoyi da dama na Alkur’ani Allah ya ke gaya musu kada su rarraba, in suka yi haka sai karfinsu ya tafi kuma rauni ya mamaye su. Daya daga cikin ayoyin ita ce:
“Ku bi Allah da ManzonSa kuma kada ku yi jayayya a junanku sai ku tarwatse karfinku ya tafi. Ku yi hakuri. Allah yana tare da masu hakuri.” (Suratul Anfal, aya ta 46)
“Wadannan suna rigengeto zuwa ga alhairai, kuma za su tarar da su. Ba ma dora wa rai sai abin da za ta iya. A gurinmu akwai littafi wanda yake furuci da gaskiya. Su ba za a zalunce su ba.” (Suratul Mu’minun, aya ta 61 – 62).
“Ya ku wadanda suka yi imani idan kun fita zuwa yaki a tafarkin Allah to ku bambance. Kada ku ce da wanda ya zo muku a musulmi ‘Kai ba mumini ba ne’ saboda kwadayin samun duniya. Allah a wajensa akwai ganima mai yawa. Kamar haka ku ka kasance a baya amma Allah ya yi muku tagomashi. Saboda haka ku bambance. Allah yana sane da abin da ku ke aikatawa.” (Suratun Nisa, aya ta 94)