ADNAN OKTAR: Haka yake, Yakamata abi Hanya da ta dace wajen kiran kiristoci da yahudawa zuwa ga yarda da karban Addinin musulunci, Ina tsammanin wadanda da suke nuna Kyama da Wulakanta Kiristoci da Yahudawa,basu son Addinin Musulunci ya yadu ya cigaba, ko kuma basu da Ilmin ta Da’awah. Akwai Kiristoci da Yahudawa Musulmai masu yawa a Wannan Kasa tamu ta Turkey, amma suna boye Musuluncin su.Kuma akwai wasu jama’a masu yawa wanda ba kirista ba ba kuma yahudu ba musulmai, wanda suma suna boye musuluncin su a wannan kasa. Haka idan da zan kirga maka wanda na hadu dasu da wanda Na sani Musulmai, zakayi mamaki saboda yawan su. Amma suna boye Musuluncin su saboda suna fama da matsi da fitintinu daga cikin gida. Ya Kamata su bayyana kansu, kuma kada su ja da baya.Yana daga Cikin halin dan Adam na Rashin Dauriya da Hakuri akan Jarrabawa Musamman jarrabawa marar kyau.Kuma suna tsammanin zasu iya kare kansu tare da boye musuluncin ba tare da ansani ba.Musuluntar Kiristoci da Yahudawa yana nuna Tabbatacin Yaduwar Addinin Musulunci da Cigaban sa , Kuma Alama ce mai nuna Cewa Lokaci yayi da Addinin Musulunci zai mamaye Duniya baki daya.