(Allah) zai ce, “Tsawon shekaru nawa kuka zauna a duniya?” Za su ce, “Mun zauna ne tsawon rana guda ko yankin rana. Ka tambayi masu lissafi!” Zai ce, “Kun zauna ne na dan lokaci, in har kun san haka!” Shin kuna zaton mun halicce ku ne don wasa, sa’annan kuna zaton ba za ku dawo garemu ba? (Suratul Mu’minun, aya 112 – 115)
Ranar da Alkiyama za ta tsaya, masu laifi za su yi rantsuwa cewa ba su zauna (a duniya) daidai da awa guda ba. Kamar haka suka kasance ana rudar da su.” (Suratu Rum, aya ta 55)
Ya ku mutanena! Rayuwar wannan duniya jin dadi ne kalilan. Gidan lahira shi ne gidan dauwama. (Suratul-Gaahafir, aya ta 39)
Wadannan mutane suna kaunar rayuwar wannan duniya, sai suka mance da (tunanin) mashahuriyar rana. (Suratul- Insan, aya ta 27)