(Allah) wanda ya halicci dukkan abu ya kyautata halittarsa, kuma ya fari halittar mutum daga yunbu (tabo). Sannan ya sanya asalinsa daga wulakantaccen ruwa da aka fitar; sannan ya siffanta shi, ya busa masa rai daga ruhinsa, kuma ya sanya muku ji da gani da zuciya (tunani). Kadan ne ku ke godewa! (Sura Sajda, aya 7 – 9)