Hakika Allah (SWT) ya sani cewa dukkan Annabawa mutane ne masu tsananin imani da tsarkin zuciya da kuma madaukakan kyawawan halaye da dabi’a, don kuwa shine ya halicce su ya sanya su masu kakkarfan imani da iklasi. Sai dai kuma, duk da ya ke cewa Annabawa zababbun bayi ne wadanda Allah ya daukaka su birbishin sauran bayinsa, su suka fi kowa haduwa da mafi girman jarrabawa da fitintinu a rayuwarsu ta duniya. Kuma wadannan wahalhalu da suke sha sun kasance alamu da ke nuna tsananin gaskiya da karfiin imaninsu ta yadda mutane za su yi koyi da kyawawan halaye da dabi’u irin nasu, sannan kuma don ya kara kusanci da soyayyar su Annabawan ga Allah ubangiji, haka nan don ladansu ya ribanya a ranar lahira gwargwadon wahalarsu a duniya. Allah ya bayyana mana nau’in yanayin jarrabawar Annabawa ta hanyar hikayoyi a cikin Alkur’ani.
Yayin da Annabi Musa (as) da mutanensa suka sami kansu cikin tsaka-mai-wuya; wato gabansu kogi bayansu kuma rundunar fir’auna ce ke dab da cim masu, da yawa sun fid da rai da samun kubuta. Wadanda ba su da imanin sanin karfin Allah suka ce “An rutsa da mu,” to amma kamar yadda ya zo a ayoyin sai Musa (as) ya ce “A’a, Ubangijina yana tare da ni kuma zai ba ni mafita.” (Suratul Shu’ara, aya ta 62).
Annabi Yunuusa (as) kuwa a tsawon lokacin wahalhalun da ya sha yayin da ya ke cikin kifi, ya mika lamarinsa ne ga Ubangiji inda, kamar yadda ayar Kur’ani ta fada mana, “Ya yi kira (ga Ubangiji) a cikin halin tsanani." (Suratul Kalam, aya ta 47). A saboda kaskantar da kai da mika lamarinsa ga Allah da Yunus ya yi cikin mawuyacin halin da ya sami kansa, sai Ubangiji cikin rahamarsa da jinkansa ya kubutar da shi daga cikin kifin da ya hadiye shi, sannan ya aika shi ga wata al’umma a matsayin Annabi. Alkur’ani mai girma ya yi mana bayanin wannan jarrabawa da ta sami Annabi Yunus kamar haka:
“Yunus yana daga cikin ma’aikanmu. Yayin da ya gudu zuwa cikin babban jirgin ruwa. Suka yi kuri’a sai ta fada a kansa. Sai kifi ya hadiye shi alhalin ya kasance abin zargi. Ba don ya kasance yana daga cikin masu tasbihi ba, da ya zauna cikin sa har zuwa ranar da za a tashe su. Sai muka fito shi bisa doron kasa yana marar lafiya; kuma muka fitar da bishiyar duma a kansa. Sannan muka aika shi zuwa ga (al’umma mai yawan) dubu dari ko fiye da haka. Sai suka yi imani kuma muka jiyar da su dadi na wani lokaci.” (Suratua – Saffat, aya ta 139 – 148)
Yayin da Manzan mu (saas) mushrikai suka yi masa zobe shi da al’ummarsa babu mai zaton tsira a garesu. Wannan ita ce ranar kunci, ranar jarraba imani. Sannan kuma wannan jarrabawa ce ta musamman wadda za ta sa cikakkun muminai masu karfin imani, wadanda suka hakikance a zukatansu cewa taimakon Allah zai zo kuma suka mika dukkanin lamarinsu gare shi, za su kasance tabbatattu bisa dugadugansu. Kuma kamar yadda Allah ya hukunta, wadanda suke da nakasa a cikin imaninsu da Allah da kuma munafukai sun fid da kaunar samun rahamar Allah a wannan hali inda suka kama dabarun kansu don neman mafita. Allah mabuwayi yana bayyana mana wannan mawuyacin hali a wata ayar kamar haka:
“Yayin da suka zo muku daga birbishi da kuma ta kasanku, yayin da idanunku suka juye kuma zukatanku suka zo makogoro, kuma kuka yi wa Allah mummunan zato, a wannan hali an jarrabi muminai aka girgiza su matukar girgizawa. Yayin da munafikai da wadanda suke da ciwo a zukatansu suka ce ‘ba abin da Allah da Manzansa suka alkawarta mana sai rudi.’ Kuma wata kungiya daga cikinsu ta ce ‘Ya ku mutanen Yathrib, babu matsayi gare ku don haka ku dawo!’ Wasu daga cikinsu suna neman izini daga Annabi suna cewa ‘Babu tsaro a gidajenmu,’ alhalin ba batun rashin tsaro ba ne; kawai dai suna nufin gudu ne.” (Suratul Ahzab, aya ta 10 – 13)
A cikin wannan matsanancin yanayi, Ma’aikinmu (saas) tare da sauran muminai da ke tare da shi sun kasance suna masu tsammanin taimako daga Allah mabuwayi yayin da suka mika lamuransu gare Shi tun da sun san dama ya yi alkawarin zai taimaki masu imani da dogaro gare Shi. A wannan ayar Allah yana fada:
“Yayin da muminai suka ga rundunar taron dangi sai suka ce: ‘Wannan shine abin da Allah da Manzonsa suka alkawarta mana. Allah da Manzonsa sun yi gaskiya. Wannan bai kara musu komai ba sai imani da sallamawa.” (Suratul Ahzab, aya ta 22).
Haka kuma kamar yadda a wata ayar Allah ya ke bayyana mana, “Allah ya dauke wa muminai yaki. Allah mai karfi ne, mabuwayi.” (Ahzab, aya ta 25)
Annabi Yusuf (as) shi ma ya hadu da manyan nau’o’i na jarraba a zamaninsa. Yadda a ka kulla masa kazafi sannan a ka wurga shi cikin kurkuku a ka mance da shi na tsawon shekaru, tabbas ba karamar jarraba ba ce wannan. Haka kuma tabbas daya daga cikin jarrabawar da ya tsallake cikin nasara da taimakon Allah ita ce yadda tun farko ‘yan uwansa suka jefa shi cikin rijiya inda ya zauna cikin duhun rijiyar yana mai tawakkali da tsammanin taimakon Allah. In da tawagar matafiyan nan ba ta biyo ta wajen rijiyar nan, kuma da mutanen cikin tawagar ba su nemi jawo ruwa a rijiyar ba, to da watakila nan zai shafe kwanaki ciki har shahada ta zo masa. Sai dai kuma ba makawa komai yana gudana ne da ikon Allah. Allah ya halicci Annabi Yusuf (as) ya sanya shi cikin madaukakan Annabawa masu girma sannan ya hukunta samun tsira da daukakarsa a bisa kyakkyawan tsari.
Annabi Ludu (as) ya sha fama da mutane batattu a zamaninsa, Annabi Ayyub (as) ya nuna juriya a yayin tsananin rashin lafiyar da a ka jarrabe shi da ita, Annabi Haruna (as) ya sha wahala yayin wa’azi kan mushirikan mutane masu kin gaskiya, Annabi Yahya (as) kuma ya yi shahada a hannun masu adawa da kiran Allah ne a zamaninsa, yayin da kuma Annabi Isa (as) ya sha wahalar gwagwarmaya da kaidin munafukai. Gaba daya wadannan Annabawa an jarrabe su da bala’o’i makamantan juna. Haka nan kuma musulmi da suka bi hanyar Annabawan su ma sun hadu da irin wadannan nau’i na bala’i daban daban. Mutanen da suka yi imani bayan sun ga hujjojin da Allah ya baiwa Annabi Musa (as) sun yi hakan ne bisa yakini duk kuwa da sun san cewa fir’auna zai yanke hannaye da kafafunsu sannan ya kashe su. Sahabban Manzanmu (saas) sun sha gwagwarmaya da kafirai wadanda suka fitar da su daga gidaje da garuruwansu, suka azabtar da su har kuma suka kashe wasu daga cikinsu. Hakika muminai sun gamu da babbar jarrabawar imani yayin da suka shiga cikin ukubar kafirai. Allah madaukaki ya na yi mana bayanin halin da muminai suka sami kansu yayin da a ka wurga su cikin wutar da kafirai suka hura a cikin wadannan ayoyi kamar haka:
“An la’anci ma’abota rami. Wuta ce wadda a ke hura wa. Yayin da suke zaune a gefenta, suna kallon abin suke aikatawa a kan masu imani. Ba komai ba ne ya sa suke azabtar da su sai don cewa sun yi imani da Allah, mabuwayi, abin godiya. Wanda mulkin sammai da kasa ke gare Shi. Allah mai gani ne a kan kowane abu. Wadanda suke azabtar da muminai maza da mata, sannan ba su tuba ba, suna da azabar wuta kuma suna da azabar gabara.” (Suratul Buruj, aya ta, 4 – 10)
Tabbas Allah mabuwayi shi ne mai yin halitta, da halitta ta musamman, ya halicci Annabawa da muminai da masu wa’azi, wadanda ke mika wuya gare Shi, kuma suke daukaka son Sa fiye da komai, rayuwarsu da mutuwarsu don shi suke yi. Ya haliccesu don aljannarsa, amma a na jarrabarsu a rayuwar duniya. Akwai hikima a cikin wannan; jarraba da wahalhalun da suke fuskanta alamu ne na daukaka, da sadaukarwa da kuma iklasi da tsananin soyayyar Allah mai girma. Annanbawa da tsananin juriya da gaskiyarsu, da sadaukar da kansu, da mika wuya da kuma tsananin iklasi da kyawawan dabi’unsu, suka kara girman matsayinsu. Wadannan kyawawan dabi’u na su wadanda saboda su suka zama mafi daraja da daukaka a cikin ‘yan aljanna, su ne juriya da dogewarsu a bisa bin tafarkin Allah. Kuma Allah mahalicci ya shirya wannan yanayi na wahalar jarrabawa ne don mu da su mu gane muhimmancin sallamawa da mika wuya gare Shi. Babu kokwanto cewa Allah yana bada kariya da tallafawa muminai yayin da kuma yake tare da su a kowane hali. Don haka yana da muhimmanci muminai su san haka don su rika nuna juriya da hakuri a halayen wahalhalu da suka sami kansu a cikin a kan tafarkin Allah. Annabawa da wadanda suka yi imani tare da su kuma suka bi su za su tarar da kyakkyawan sakamako da kyakkyawar rayuwa a ranar alkiyama saboda hakuri da suka nuna. A wasu ayoyi Allah yana cewa:
“Wadannan za a saka musu da madaukakiyar aljanna saboda hakurin da suka yi, kuma za a tarbe su a cikinta da gaisuwa da aminci. Za su dauwama a cikinta har abada. Makoma da mazauni sun kyautata.” (Suratul Furqan, aya ta 75 – 760
Jarrabawar duniya babbar rahama ce ga musulmi masu imani
Samuwar Allah abu ne da babu tantama a cikinsa. Duk mai inkarin samuwar Allah makaryaci ne, kuma mayaudarin kai, domin hujjoji da alamomin samuwar Allah bayyane suke a ko’ina. Kuma abu ne mai wuya mutum, bayan sanin wadannan alamomi bayyanannu, a ce ya kasa gane samuwar Allah mabuwayi.
Halittar mutum da kwayar halittar rai, da haske, da kwayar zarra, da halittar wannan duniya da sauran duniyoyi daban da ta mu, duk hujjoji ne da suke nuna girman daukaka da gwanintar Allah a halitta. Babu mai musun wannan. Dalilin da ke sa wasu mutane fada wa a cikin rudu na samuwar Allah ba wai don suna musun samuwarsa ba ne. A’a, sai dai abin kawai da yake nauyaya zukatan wadannan mutane wajen mika wuya ga Allah shine kasawarsu wajen fahimtar jarrabawar da Allah ya ke yiwa bayinsa da kuma hikimarsa ta y in hakan. Jarrabawar duniya ta kan firgita su su dimauce, yayin da wahalhalun da ke cikinta suke kara nisanta su daga Allah Ubangiji. Tun da yake dama ai kowa yansan umarnin da a ka yi masa na bautar Allah mahalicci. A wata aya Allah mai girma yana cewa:
“Suka yi musun ayoyinmu bisa zalunci da dagawa, alhalin suna da yakini a kansu. Dubi yadda karshen masu barna yake.” (Suratul Namli, aya ta 14)
Dukkan mutane a cikin zukatansu sun san da samuwar Allah da kuma wajibcin rayuwa a bisa umarninsa, amma duk da haka wasunsu sun kasance suna kidimewa da sanya kokwanto a duk lokacin da a ka jarrabe su. Abin da ya sa mutanen Annabi Musa (as) suka ce da shi “Ka je kai da ubangijinka ku yi yakin, mu muna nan zaune” (Suratul Ma’ida, aya ta 24), a yayin da suka fuskanci jarrabawa, shine saboda zukatansu sun fifita son duniya a kan yaki don daukaka addinin Allah.
Hakikanin lamarin shine kyakkyawar dabi’a da musulmi suka nuna a yayin hadin guiwar kafirai suna caccakar Alkur’ani, shine kamar haka:
“Wadannan da mutane suka ce da su ‘hakika mutane (kafirai) sun yi taron dangi a kanki, ku tsorace su.’ Amma sai wannan ya kara musu imani inda suka ce ‘Allah ya isar mana, madalla da (Allah) majibincin lamari.” (Suratu Al’Imrana, aya ta 173)
Musulmi wadanda suka mika wuya suka dogara ga Allah a halin kunci, an bayyana su da cewa:
“Wadanda in musiba ta same su sai su ce ‘Daga Allah mu ke kuma zuwa gare shi za mu koma.’” (Suratul Bakara, aya ta 156)
Allah mai girma da buwaya yana fada mana a wata ayar cewa riskar kyakkyawan sakamako da samun babban matsayi ya kan samu ne ta hanyar cin jarrabawa da kyakkyawar dabi’a da mika wuya tare da hakuri da sadaukarwa:
“Kyautata aiki (bauta) ba shine juya fuska sashen gabas ko yamma ba. Sai dai kyakkyawan aiki shine wanda ya yi imani da Allah, da ranar lahira, da mala’iku, da littafi, da Annabawa, da wanda kuma ya bayar da dukiya, da matafiya, da mabarata, da wadanda ke cikin kangi (na bauta) , sannan ya tsaida sallah ya bada zakkah, da wadanda suke cika alkawari in sun dauka, da masu hakuri a halin tsananin talauci da ciwo da halin yaki. Wadannan sune wadanda suka mika wuya da gaskiya. Wadannan sune masu takawa (tsoron Allah).” (Suratul Bakara, aya ta 177)
Allah kan sanya halin kunci ga al’ummun da suka bar hanyarsa a bisa wata hikima da kuma manufa. Yawancin mutane suna da halayyar nan ta maida hankulansu kan al’amuransu na rayuwar duniya, su mance da Allah yayin da suke cikin ni’ima da jin dadi. Irin wadannan mutane zatonsu idan suna da hali da wadata shikenan ba su ba samun matsala, har ma suna ganin su ma masu iko ne. Sai dai Ubangiji ya jarrabi al’ummu wadanda suka fada cikin rudun shagala da rafkanuwa saboda wadata da arzikin da Allah ya ba su, duk kuwa da an gargade su cewa su guji girman kai da dagawa. Amma sai suka yi wa Allah tsaurin kai suka fandare, a maimakon jarrabawar da suka sami kansu ciki ta sa su gane su komo kan tafarki don Allah ya yafe kurakuransu. A wata aya Allah ya na cewa:
“Hakika mun aika da manzanni zuwa ga al’ummu kafin zuwanka, sai muka kama su da tsanani da wahalhalu domin cewa ko za su kaskantar da kan su.” (Suratul An’am, aya ta 42)
Tabbas jarraba ta hanyar kunci da tsanani ta kasance babban hanyar tunatarwa ga fandararrun al’ummu. Allah ya bamu labarin halin wata fandararriyar al’umma da mutanen ta suka kasance cikin jirgin ruwa wadda kuma ke fuskatar igiyar ruwa ta kowane bangare a tsakiyar teku, kamar haka:
“Shine wanda ke tafiyar da ku a doron kasa da cikin kogi, har yayin da kuka kasance a cikin jirgin ruwa, kuna tafiya da iska mai dadi kuna farin ciki da ita, sai kakkarfar iska (mummuna) ta zo musu, inda igiyar ruwa ta taso musu ta kowane bangare, suka yi zaton za a halakar da su, sai suka roki Allah suna masu tsarkake bauta gare Shi suna cewa ‘in har ka tserar da mu daga wannan za mu kasance cikin masu godiya.” (Sura Yunus aya ta 22)
Ga hikimar wannan jarrabawa. Wadannan mutane, bayan sun fahimci cewa rayuwar wannan duniya ba mai dauwama ba ce, kuma suka tuna cewa duk wani iko da karfi yana ga Allah shi kadai sannan sun san a wannan hali da suke fuskantar halaka daga igiyar ruwa ba su da wata mafita sai komawa ga Allah mai komai da ikon komai. Amma bayan sun kubuta daga wancan hatsari sai suka koma ga halinsu na rafkana.A aya ta gaba Allah yana bayyana mana kamar haka:
“Amma yayin da ya kubutar da su sai ga su suna dagawa a bayan kasa ba tare da hujja ba. Ya ku mutane! Hakika dagawarku kuna yi wa kanku ne. Dan dadi ne na rayuwar duniya, sannan gare mu za ku dawo kuma mu ba ku labarin abin da kuka aikata.” (Sura Yunus, aya ta 23)
Mutane a hankalin kansu sun san abin da ya kamata su yi na daidai. Domin kowane mutum ya san yakamata ya zama cikakken bawan Allah kuma ya dage wajen neman yardarsa. Abin da ke sa wa wasu mutane ba su damu su san girma da karfin Ubangiji ba shine saboda rudin zuciya da shaidan wanda ke fifita musu son rayuwar duniya marar dauwama har su mance da tunanin Allah da lahira. Sai dai kuma duk irin kokarin mutane na ganin sun yi watsi da hikimar Allah ta jarrabawa a duniya, hakan ba zai hana a jarrabe su ba. Ruduwa da shagala da rayuwar duniya ba zai ba su nutsuwa da salama ba matukar sun yi watsi da al’amarin gaskiyar da zukatansu suka sani amma suka take. Farin ciki da jin dadin da suke hankoron samu a wannan rayuwa duk rudu ne da karya. Tun da sun kasa fahimtar cewa farin ciki da nutsuwa Allah ne ya ke saukar da su ga bayinsa, to yana da matukar wuya su iya samun kwanciyar rai da rayuwar farin ciki kamar yadda suke fata. Wanda ma bai yarda da cewa rayuwar duniya jarrabawa ce ba, to ya ya zai iya gane haka!
Me zai faru a duniya in babu jarrabawa?
Duk wasu abubuwa wadanda saboda su ne mutum ya cika mutum, in babu jarrabawa duk za su gushe. Darajoji da suke samuwa daga kyawawan dabi’u kamar sadaukar da kai, biyayya, hakuri da juriya, soyayya, tausayi, girmamawa, taimako da zumunta duk za su rasa ma’ana. Rigengeton aikata alheri da kuma son kyautatawa sauran mutane shi ma zai zama ya rasa muhimmanci ko daraja. Ka ga kuwa duk wanda rayuwarsa ta zama babu wani abu da ke da kima ko daraja a cikinta, to rayuwar nan ba ta da amfani.
Soyayyar Allah ce dalilin mika wuyan muminai da juriyarsu a yayin da suka sami kansu cikin halin kunci. Domin in za a kyale mutum sakaka ba a jarrabarsa, to zai koma ne kamar dabba wadda manufar rayuwarta bai wuce ci da sha da yin barci ba. Hakan ne ya kan sa mutum ya rasa sinadarin jin dadin rayuwa. Irin wannan yanayin rayuwa na karya shine masu da’awar akidar Darwiniyanci suke ta kokarin tunkuda mutane cikinta a tsawon shekaru. A rayuwar da ba a jarrabar mutum, wadda kuma babu kyakkyawar dabi’a da sanin yakamata a cikinta, wadda rayuwa ce kawai marar manufa, a nan ba ka iya bambance rayuwar mutum da ta dabba tun da duk suna rayuwa ne, kamar yadda Darwiniyawa ke riya wa, a bisa hanyar dabi’a guda marar bambanci. Duk lokacin da halitta ta yi watsi da tsarin Allah a doron kasa, daga nan rayuwa ta zama ta karfinka-ya-kwace-ka kenan.
Zai yi kyau a nan mu kawo wani al’amari: Hatta dabbobi an halicce su da ruhin so da kauna, biyayya, sadaukar da kai da kuma tallafawa juna. Saboda haka a yanayin da mutane suka kasance kara-zube ba a jarrabar su da komai, za su zama ba su da manufa ko kyakkyawar dabi’a wanda hakan zai sanya su kasan dabbobi wajen kaskanci. Allah mai girma yana fada mana cewa kafirai wadanda suke bautar son zuciyarsu dabbobi ma sun fi su:
“Shin kana zaton mafi yawansu suna ji ko lura (su hankalta)? Su fa kamar dabbobi su ke. Kai sun fi (dabbobi) bacewa daga hanya!” (Suratul Furqan, aya ta 44)
Abin da wasu mutane suka kasa fahimta shine: jarrabawa ta na kara wa mutane daraja. Mu kan so wani bawan Allah da ya gabata saboda irin hakuri da juriyar da ya nuna don neman yardar Allah. Annabawa sun sami mafi girman daukaka ne saboda sun bi Allah da hakuri a kan duk abin da ya same su a tafarkinsa. Wanda kuwa ya yi hakuri kan bin Allah, Allah zai daukaka shi ya girmama shi. Su ne mutane masu kauna da son bayin Allah, wadanda kuma, duk da yake cewa an halicci mutum da dabi’ar son kai da hassada, amma ba su nuna haka ba saboda Allah, suka danne zuciyoyinsu a kan kyasi da hassada, suke daukaka sauran musulmi a kan kawukansu kuma suke rokon gafarar Allah a kan kurakuransu. To masu irin wannan siffa dole su kasance ababen ambato da girmamawa a gobe kiyama.
Ubangiji ya kan daukaka mutum mai juriya da hakuri a bisa jarrabar da Allah ya yi masa. A sakamakon dauriyar da mutum ya nuna saboda Allah duk kuwa da bakar wuya da tsananin ciwo da wasiwasin zuciya, amma ya jure ya mika lamari da fatansa ga Allah, to Allah yana kallonsa da girma da tausayawarsa.
Hakurinsa zai zama ado gareshi a cikin aljanna, saboda cewa ita aljanna a na samunta ne ta hanyar nuna hakuri da juriya yayin jarraba a tafarkin Allah, wanda a ka yi don neman yardar Allah kadai. A wannan aya ta Alkur’ani Allah yana cewa:
“Ko kuna zaton za ku shiga aljanna ba tare da Allah ya san wadanda suka yi kokari a cikinu da kuma masu hakuri ba?” (Sura Al’Imrana, aya ta 142)
Bai kamata a mance da wannan batu na gaskiya ba: Allah mai ikon halitta wanda ya sanya kunci a matsayin jarrabawa musamman don ya jarrabi bayinsa, kuma shine ya nuna hanyoyin magance su. Daya daga wadannnan hikimomi wadanda Allah ya sanar da muminai su a cikin Alkur’ani shine cewa babu wanda za a dora wa abin da ya fi karfinsa:
“Allah ba ya dora wa rai face abin da za ta iya dauka. Abin da ta aikata yana gare ta; kuma abin da ya cancanceta yana kanta.’Ya Ubanfijinmu, kada ka kama mu da laifin abinda muka manta ko muka yi kuskure a kai! Ya Ubanhijinmu, kada ka dora mana nauyi kamar yadda ka dora a kan wadanda suka gabace mu! Ya Ubangijinmu, kada ka dora mana abin da ba za mu iya daukarsa ba! Ka yi mana rangwame, ka gafarta mana, kuma ka yi mana rahama. Kai ne majibincin lamarinmu, ka taimake mu a kan kafiran mutane.” (Suratul Bakara, aya ta 286)
Musulmin da ya fuskatar da lamarinsa ga Allah a cikin kowane irin hali shine cikakken bawan Allah mai biyayya gareshi. Kuma duk irin tsananin kuncin da mutum zai gamu da shi a halin jarrabawa, to ba za a jarrabe shi da abin da ba zai iya dauka ba. Halin kunci da wahala ya kan zama hanyar gyara halin bayi, a jawo su don su kusanci Ubangijinsu, kuma don a kare su daga shagala domin su dace da rahamar Allah madauwamiya ta aljanna.
![]() |
Bugu da kari kuma, mutumin da ke gamuwa da kunci da wahala zai fi ganin darajar aljanna da tarin ni’imominta. Mutumin da a ka jarrabe shi da talauci da yunwa a wannan rayuwa ta duniya zai fi nuna godiya ga Allah da kara bauta da mika wuya gareshi yayin da ya sami kansa cikin aljanna inda yake samun abin da duk zuciyarsa ta ke bukata cikin sauki ba tare da wata wahala ba. Wanda ya yi hakuri da juriya a bisa tsananin rashin lafiya a duniya, ka san ba karamin farin ciki zai yi ba in ya ga cewa a aljanna babu sauran rashin lafiya ko wahala. Wanda a ka cuta bisa rashin adalci a wannan rayuwa to zai sami kyakkyawar sakayya a lahira inda zai shiga aljanna ya dauwama cikin halin farin ciki da jin dadi, da kuma uwa uba, samun kusancin Ubangijinsa, babu wata tawaya ko nakasa. Misali, musulmi wanda ya kasance gurgu a wannan duniya zai zama mai kafa a cikin aljanna kamar bai taba yin nakasa ba. Haka nan idan mutum makaho ne a duniya to a aljanna ganinsa zai kasance ya ma fi na masu idanun a wannan duniya, inda zai kalli halittu ya gane hikima da kudirar Allah a cikin sha’anin halittar. Idan kuma mutum a na ganinsa mummuna a duniya, to idan ya shiga aljanna za a maida shi kyakkyawa. Haka kuma ba karamin abin daraja da godewa ba ne ga mumini wanda ya san yadda rayuwarsa ta kasance a duniya inda ya gudanar da ita cikin juriya da hakuri.
Musulmi zai gane rahamar Allah a kansa in ya kwatanta rayuwar wannan duniya da kuma madauwamiyar rayuwar lahira. Don kuwa rayuwar duniya takaitacciya ce da a ke jarrabar mutum a cikinta, jin dadi ne na dan lokaci. Su kuwa wadanda suka yi hakuri a yayin kunci da wahala saboda Allah, wadanda kuma rayuwarsu gaba daya suka tafiyar da ita a hanyarsa yayin da tunaninsu da ayyukansu gaba daya Allah suka fuskanta, to su ne ke samun mafita a gobe kiyama.
“Wadanda kuma suka yi imani kuma suka yi ayyuka masu kyau, za su kasance masu jin dadi a cikin lambu (na aljanna).” (Suratur Rum, aya ta 15)