Sa’an nan kuma ya kasance daga wadanda suka yi imani ,kuma suka yi wa juna wasiyya da yin hakuri, kuma suka yi wa juna wasiyya da tausayi.Wadannan ne ma’abuta albarka. (Surat al-Balad: 17-18)

Marar mutunci ba zai tausayawa kowa ba,saboda baya tunanin kowa sai kansa, kuma yana bada muhimmanci ne kawai akan abinda zai amfane shi da son zuciyar sa,shiyasa baya damuwa da halin kunci da wasu jama’ar musulmi suke ciki,bugu da kari ba su tausaya yan uwansu a duk hallin da suke ciki na damuwa.
Dalilin da yasa Bayin Allah(swt) suke sadaukar da kansu wajen taimako da tausayin juna saboda bin umurni Allah (swt).Kamar yadda aka bayyana a cikin Ayoyi masu yawa.’’ Allah ne mafi tausayin masu tausayi".Saboda wannan dalili bayin Allah (swt)masu Imani suke daurewa akan duk halin da suka samu kansu a ciki na kunci ko jin dadi.
Kamar yadda Allah ya saukar a cikin Alkur’ani maigirma , "Kuma ba domin falalar Allah ba a kanku da rahamar sa … Kuma lalle ne Allah Mai tausayi ne,Mai jinkai)." (Surat an-Nur: 20). Aya ta sama tana nuna yadda Allah yake tausaya wa bayinsa ,kuma yadda yake umurtar su dasu tausaya wa junansu,ta haka suma zasu samu yardar Allah(swt) da tausayin sa.Shiyasa masu Imani suka dauki matsayin tausayi da muhimmanci,kuma suna fatan samun rahmar Allah(swt),kuma suna tausaya wa al’umma,suna kokarin wajen umurtar al’umma dasu tausaya wa juna domin ta haka ne za’a samu rahmar Allah (SWT).
Gaskiya Alkur’ani maigirma yayi bayani akan dukkan al’amari da ya shafi tausayi da yadda za’a tausaya wa juna .Matsayin bayin Allah nagari sune masu tausaya wa da tabbatar da adalci a lokacin daya dace cikin al’umma kamar yadda Allah (swt)yayi umurni.
Kamar yadda aka bayyana tausayi a Alkur’ani maigirma,Tausayi yana da babban matsayi da girman gaske fiye da dukkan sauran al’amura.Jama’ar da yawa basu fahinci manufa da muhimmancin tausayi ba saboda rashin fahimta addini,shiyasa basu san yadda zasu tausaya wa al’umma ba tare da girmama su,kuma basu iya bambanta aiki maikyau da marar kyau, kuma basu tunani akan muhimmancin tausayi tare da duba menene Alkur’ani ya fada akan tausayi.,koda yaushe suna nuna halayen da zasu cutar da kansu da al’umma.;suna yin kuskure wajen magance wasu al’amura da suka taso ,saboda fahimtar su game da tausayi yan a cin karo da yadda Alkur’ani maigirma ya bayyana tausayi da danganta karsa da muhimmancin tausayi ga al’umma.Wani lokacin mutane sukan kai da komo wajen fahimtar tausayi, wanda daga karshe yakan zama kuskure tare da sabawa karantar war Alkur’ani maigirma.Irin wannan mummunar fahimta ga tausayi yakan zama cutarwa ga al’umma. Alummar da addini yasa ta rarraba zuwa kungiya kungiya,za kaga shugabanni suna barin wasu mutane suna aikata wasu aiyuka batare da tunani da kuma kallon riban da zasu samu a ranar gobe (kiyama).Misali ,shugabanni sukan kauda kai daga aikin haramun da al’umma suke aikatawa,kuma ba tsawatar wa a lokacin ake aikata laifi da Allah (SWT) ya hana ko ya umurci al’umma dashi.

A bisa wannan dalili ,bayin Allah magari suke bin koyarwar Manzon tsira Muhammad (SAW) da halayen sa wanda Alkur’ani maigirma ya bayyana mana.’’Kuma, lalle ,hakika kana a kan halayen kirki,manya". (Surat al-Qalam: 4)
A wata Ayar Allah (SWT)ya yabi manzon tsira (SAW) da halaye nagari: "Lalle ne,hakika ,Manzo daga cikinku yaje muku .Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa .Mai kwadayin ne saboda ku.Ga muminai Mai tausayi ne,Mai jin kai." (Surat at-Tawba: 128) A saboda wannan dalili bayin Allah (SWT) nagari da suka riki wannan umurni da koyarwar Manzo (SAW) suna masu nuna wa juna adalci da tausayi,tare da umartar al’umma su da aikata aiki nagari saboda kwadaitar dasu samun tausayi da rahmar ubangijin su a gobe kiyama(lahira).