A rayuwar bil – adama mutane suna ganin tasirin hikimar Allah ta irin baiwar daya sanya a kwakwalensu. Wannan kuwa wasu maganadison sadarwa ne da ke da ke isarwa da tara bayanai a zuciyar Dan-adam. Kuma koda yake akwai irin wannan al’amari na baiwa a zahirance, mutane kan lura ne kawai da wadanda aka sanya musu cikin kakwalensu. Don haka, a bisa tsarin Allah mai hikima, halayyarmu ta zahiri ta kasance fassarar abin da yake boye cikin kwakwalenmu ne, kuma muna fahimtar duk wadannan abubuwa da ruhin da Allah ya sanya mana; wato ta hanyar gain, da ji, da kuma tabawa da fahimtar su.

Idan mutum ya dubi duk wadannan dalilai na fahimta da Allah ya sanya a cikin ruhin mutum, to lalle zai san cewa muhimmanci ko sirrin hikimar kowane abin halitta yana ga ruhi ne amma ba abubuwan zahiri ba, domin hakan dalili ne da ke nuna ruhi shi ke tafiyarwa tare da sarrafa jiki. Ruhi ko rai shi ke ji da fahimta, yayin da gangar jiki da sauran abubuwan da ke kewaye da mu an tsara su ne a sakamakon abin da ruhi ya fahimta. A bisa dabi’a, naman jiki ko kasusuwa ba sa yin bakin ciki, murna, alfahari, yanke hukunci  kan abu ko yin tunani ba. Ruhi ko rai ne kadai ke iya ji, yin tunani, zabi da kuma yin amfani da hankali wajen yanke hukunci ko bayyana farin ciki da annashuwa. Shi wannan rai ko ruhi da mutum kan ce “rai na,” to a hakikanin gaskiya ruhin Allah ne, kamar yadda ya zo a wannan aya cewa:

(Allah) wanda ya halicci dukkan abu ya kyautata halittarsa, kuma ya fari halittar mutum daga yunbu (tabo). Sannan ya sanya asalinsa daga wulakantaccen ruwa da aka fitar; sannan ya siffanta shi, ya busa masa rai daga ruhinsa, kuma ya sanya muku ji da gani da zuciya (tunani).  Kadan ne ku ke godewa! (Sura Sajda, aya 7 – 9)

Allah ya busa daga ruhinsa, ya sanya idanuwa da zuciya ga mutum wanda ya yi wa baiwa da mafi daukakar halitta kuma ya sanya masa tunani da hankali. Don haka shi wannan ran da mutane suke  ta tutiyar nasu ne, mallakar Allah ne kuma daga ruhinsa ne. Allah, da faffadan iliminsa da ya game komai da kuma karfin kudirarsa mayalwaciya, ya halicci ruhi a mafi kyawun siga da ban al’ajabi don ya kasance a matsayin jarrabawa ga mutane, wadanda bayan mallakar wannan baiwa a gare su kan bugi kirji su ce “nawa.”

An baiwa bil-adama kwakwalwa da ta tattara komai da komai na bayanai da ilmuka. A hankali, mataki mataki, Allah ya ke gina tunani da sanya bayanai a kwakwalen mutane, kuma yana ci gaba da sabunta kaifin tunani da ingancin kwakwalen nasu a tsawon rayuwar kowannensu. Misali, yanzu ga shi kana karanta wannan bayani, kuma nan da ‘yan mintuna abin da ka karanta zai sami gurbin zama a cikin kwakwalwarka (kamar rikoda). Zai kuma ci gaba da kasancewa cikinta na tsawon kwanaki, ko watanni ko kuma na tsawon shekaru ma (ya danganta da karfin hardar kwakwalwarka) inda za ka rika tuno shi daga lokaci zuwa lokaci. Duk lokacin da ka yi amfani da baiwarka ta tunani za ka iya tuno al’amura masu yawan gaske da ke dankare a cikin kwakwalwarka. Wadannan al’amura kuwa sun hada da muhimmai da wadanda ma ba su da muhimmanci ko girma sosai, wadanda kuma ba su kirguwa. Misali, duk da shudewar shekaru masu yawan gaske, amma har yanzu ka kan iya tuno ranar farko da ka fara zuwa makaranta a rayuwarka; ta irin wasannin da ku ka rinka yi da abokanka, da kuma irin farin cikin da ka dinga yi a waccan  rana muhimmiya, duk yana nan daram a kwakwalwarka. Wannan kundin bayanai da ke cikin kwakwalwarka zai ci gaba da kasancewa tare da kai  har ranar da rayuwarka ta kare. Mutane, wadanda Allah ya halicci ruhi kuma ya sanya a jikinsu, sai suka dauka mallakar wannan ruhi a gare su kamar su ne suka kage shi da kansu, wanda kuma wannan babban kuskure ne. Duk yayin da suka tuno da wani al’amari a rayuwarsu, lokacin da za ka ji sun ce “Na yi farin ciki a waccan rana,” “Na yi matukar murna da annashuwa a waccan rana,”su kan yi zaton ikonsu ne ba ikon Allah ba ne ya sa suka iya tuno wa da lamarin.

Kamar yadda aka bayyana a sama, Allah ne ya halicci kwakwalwa da tunani ya sanya wa Dan-adam a matsayin jarrabawa a gare shi a cikin wannan rayuwa ta duniya. Kuma, bisa yalwar sani da iliminsa ya tsara wannan  jarrabawa cikin mafi kyawun tsari da hikima. Mutanen da ke fuskantar al’amura ta mahangar Alkur’ani su ne suke fahimtar sirri da hikimar Allah a halitta kuma suke la’akari da al’amuran rayuwa da a ke jarrabar mutane da su. Amma su kuwa irin mutanen da suka nisanta daga hasken koyarwar Alkur’ani suna rayuwa ne cikin duhun jahilci a kan hakikar wannan al’amari na halittar Allah.

Saboda haka, shi dai wannan rai da mu  ke jin namu ne to cewa ruhi ne na Allah. Sai dai kuma hatta yadda mu ke ji da da’awar cewa ran namu ne, to yana daga cikin al’amuran ban mamaki da ke nuna hikimar Allah a cikin halitta da tafiyar da al’amuran halittar, amma wanda ya ke da hankalin fahimtar hakikanin hikimar halittar shi ke iya gane hakan.

Duk lokacin da wani al’amarin dadi da farin ciki ya fado mana a rai, duk da yake mu kan ji kamar yin kanmu ne, bai kamata mu manta da cewa Allah ne ya sanya mana shi saboda son Sa gare mu ba. Duk wani tunani ko al’amari da ya darsu a zukatanmu to ya samo asali ne daga ruhin Allah wanda ya sanya a jikinmu. Allah ne ya so kuma ya hore mana har mu ke jin cewa mu ne ke da ikon rayukanmu. Mu kan yi kura kurai wajen fahimtar hakikanin al’amuran da ke kundin kwakwalenmu. Amma dai gaskiyar lamari shi ne, ruhi ko rai da Allah ya hura wa mutum shi ne tushen soyayya, tunani, jin tausayi, nuna kauna da son juna, son abu mai kyau da kuma gane kyakkyawar dabi’a da mu ke yi a halin rayuwarmu.