Mafi yawan  mutane sun dauki wannan rayuwa ta dunya matabbata, wato tamkar ba za su mutu ba, don haka ma ba su damu da bin ka’idojin addini ko su yi tunanin mutuwa da ranar lahira ba. Amma kuma ita wannan rayuwa ta duniya da suke shantakewarsu a cikinta, takaitacciya ce ainun kuma mai shudewa. Duk irin tsawon kwanakin da mutum ya samu a duniya wata rana mutuwa sai ta riske shi. Kai ko ban da wannan, rayuwar duniya ta saba yadda duk muke tsammaninta. Allah ya  yi bayanin wannan al’amari ga bil-adama a wurare da dama a cikin Alkur’aninsa mai girma:

(Allah) zai ce, “Tsawon shekaru nawa kuka zauna a duniya?” Za su ce,  “Mun zauna ne tsawon rana guda ko yankin rana. Ka tambayi masu lissafi!” Zai ce, “Kun zauna ne na dan lokaci, in har kun san haka!” Shin kuna zaton mun halicce ku ne don wasa, sa’annan kuna zaton ba za ku dawo garemu ba? (Suratul Mu’minun, aya 112 – 115)

Ranar da Alkiyama za ta tsaya, masu laifi za su yi rantsuwa cewa ba su zauna (a duniya) daidai da awa guda ba. Kamar haka suka kasance ana rudar da su.” (Suratu Rum, aya ta 55)

Abin da ya gabata cikin wadannan ayoyi da aka kawo a sama wata muhawara ce da za ta gudana tsakanin mutane in an taru a ranar hisabi. Kuma kamar yadda muhawarorin suka nuna, bayan mutuwa mutane za su gane cewa sun zauna a duniya na dan lokaci kalilan. Wannan kuwa shi ne tsawon shekaru sittin ko saba’in na rayuwar mutum a dunya, wanda a gajartarsa kamar kwana daya ne kawai ya yi a cikin duniyar, ko kuma kasa da kwana daya. Wannan kuwa daidai yake da misalin mutumin da ya shafe watanni ko kuma shekaru a cikin mafarki, amma bayan ya farka sai ya fahimci ashe mafarkin nasa bai wuce ‘yan dakikoki ba ne kawai.

Da mutum zai yi dogon tunani da nazari, da zai iya gano cewa hakika rayuwar wannan duniya ba matabbata ba ce. Alal misali, kowane mutum yana da buri da manufofinsa na rayuwa da yake tsarawa kansa, kuma an san mutum da yawan burace buracen duniya marasa iyaka da ba sa karewa matukar mutum yana numfashi. Kamar yadda yake, mutum ya kan kammala karatun babbar sakandare, daga nan sai ya shiga jami’a, sannan bayan ya gama ya kama aiki a kamfani ko wata ma’aikata. Ka ga wadannan duk suna daga cikin burukan dan-adam. A rayuwar kuruciya, za ga yayin da ba a zaton matashi ya riski shekaru talatin a duniya, amma kafin wani lokaci sai a wayi gari ya kai shekaru arba’in.

Kasancewar rayuwar duniya takaitacciya al’amari ne da Allah Ubangiji ya yi bayaninsa ga bayinsa a cikin littafinsa mai hikima ta yadda kowane mai numfashi zai iya fahimtar al’amarin. Don haka, ga wadanda suka fahimci wannan gaskiyar lamari kan rayuwar duniya, sun san cewa muguwar dabara ce mutum ya shagalta da wannan rayuwa ta duniya mai yankewa, har ya mance da rayuwa ta hakika da dauwama, wato lahira. Daga cikin ayoyin Alkur’ani mai girma wadanda a cikinsu Allah ya gargadi mutane a kan rashin dauwama da kurewar rayuwar duniya sun hada da:

Ya ku mutanena! Rayuwar wannan duniya jin dadi ne kalilan. Gidan lahira shi ne gidan dauwama. (Suratul-Gaahafir, aya ta 39)

Wadannan mutane suna kaunar rayuwar wannan duniya, sai suka mance da (tunanin) mashahuriyar rana. (Suratul- Insan, aya ta 27)