A wani lokaci guda ka kasance a matsayin ‘yar mitsitsiyar kwayar halitta da ido ba ya iya ganinta. Wannan kwayar halitta ita ce ta rabu biyu kuma ta ribanya kanta sannan ta zama tsokar nama. Daga bisani ta zama mutum mai ji da gani. Sannan ka girma…
Kowacce shekaru kamanninka su kan canja…
Shin ko ka taba gane cewa babbar mu’ujiza ce wannan?
Shin ko ka taba yin tunani kan cewa:
Kowane abu a sararin duniya an halicce shi ne a bias wata ka’ida sannan kuma akwai tsarin daidaito marar nakasa a cikin kowane abin halitta?
Ko kuma cewa kasar nan da ka ke tafiya a kanta cewa tana juyawa a bisa gudun kilomita 1,670 a cikin awa guda?
Shin ka taba tsammanin sanin…
Yadda a ka halicci tsirrai da bishiyoyin da ka ke gani suna kawata duniya?
Yadda ýa’yan itace ke fitowa daga kasa ssannan yanayin dandano, kamshi da kuma launukansu ke burge ‘yan Adam?
Yadda fatar ‘ya’yan itace ta kasance riga mai ban al’ajabin gaske…
Shin ko ka taba tunanin…
Cewa annobar da ke zuwa nan gaba tana iya afkawa birnin ku kuma ta tarwatsa gidanku cikin kiftawar ido, ka yi hasarar duk abin da ka mallaka a cikin kasa da minti guda?
Shin ka taba yin tunanin cewa…
Rayuwarka tana shudewa da sauri, kuma cewa wata rana tsufa zai zo maka ka rasa karfi da lafiya da kuma kyawun kamanninka?
Sannan ga mutuwa… ba ka san lokacin da za ta zo maka ba, sai dai kamar kowane mai rai, tabbas kai ma za ta zo maka!
Allah ya halicci mutum ya sanya masa ikon yin tunani.
Duk wadannan abubuwa kadan ne daga cikin al’amuran da ya kamata dan Adam ya rika yin tunani a kan su.
IKON YIN TUNANI GA DAN ADAM
Kowane mutum an sanya masa ikon yin tunani, duk da yake yana iya jahiltar hakan. Yayin da mutum ya fara amfani da wannan iko na yin tunani sannan zai fara ganin abubuwa wadanda a da bai lura da su ba.
Allah ya halicci duk abubuwan da mu ke gani a bisa wata manufa inda kuma ya nemi mutane da su yi tunani a kansu. A wata aya yana cewa:
Hakika a cikin halittar sammai da kasa, da sabawar dare da yini, da jiragen ruwa wadanda ke gudana a cikin teku (dauke) da abin da yake amfanin mutane, da abin da Allah ya saukar daga sama daga ruwa, sai ya rayar da kasa da shi bayan mutuwarta, kuma ya watsa a cikinta daga dukkan dabba, kuma da juyewar iskoki da girgije horarre a tsakanin sama da kasa; akwai ayoyi ga mutane masu hankalta. (Sura ta 2, aya 164)
Mutumin da yake lura da kuma yin tunani kan halittar duniya da sararin subhana mai yalwa shine zai fi gane kyawu da cikar daidaito a tsarin halittar duniya.
Dan Adam na rayuwa ne cikin wata ‘yar karamar duniya da ke sagale cikin wani faffadan sarari marar iyaka, sannan kuma ita wannan duniya tana cikin barazar hatsarin da ka iya fada mata daga sararin sama. Kuma babu abin da bil’adama za su iya yi don kare faruwar wannan hatsari.
Alal misali, akwai wasu guma guman duwatsu da nauyinsu ya kai miliyoyi a ma’aunin ton da ke ninkaya a cikin iska a sararin subhana.
Kowanne daga cikinsu yana iya cin karo da wannan duniya da mu ke ciki wanda hakan baraza ne ga rayuwar mutane da dabbobi a duniyar.
Wata barazar kuma da ka iya sanya rayuwar duniya cikin hatsari ita ce tartsatsi da fesowar zafin rana.
Taartsatsin yana iya karuwa inda hakan zai iya jawo karuwar yawan tsananin hasken rana da ke zuwa cikin duniya.
Akwai barazana mai yawa ga rayuwar mutum, ba kawai daga cikin sammai ba, har ma daga kasa.
Daga kasan murfin kasa ko duniya, akwai wani zirin wuta mai zafin gaske da a turance muke kira “magma.” Kuma shi murfin kasar ba shi da kauri. Ko don haka, amon wuta yana iya faruwa a kowane lokaci inda madin narkakkun duwatsu za su furzo zuwa doron kasa.
Ko kuma wata tsaga ko baraka a murfin kasa kan iya haddasa gagarumar girgizar kasa....
Dan Adam dole ne ya kasance yana sane da irin barazanar wadannan hatsarurruka da yake rayuwa cikin su.
Duniyarmu tana samun kariya daga barazar wadannan hadarurruka ne daga turakun daidaito na duniyar.
Mutumin da ya kasance yana tunani a kan wadannan abubuwa shi zai gane cewa dukkan halittu suna rayuwa ne a doron kasa bisa ikon Allah sakamakon tsarinsa na halitta marar nakasa a cikin sa.
MATSAYIN DUNIYARMU A SARARIN SUBHANA
.Yalwar fadin sararin subhana ya bambamta da irin rayuwar da muka saba da ita. A yanzu haka, nisan kilomita miliyan 560 sama daga inda ka ke zaune, akwai buraguzan tartsatsin rana da ke zagayawa a sararin sama a kan tafiyar kilomita 100,000 a cikin awa guda.
Yanayin sanyin da ke sama ya kai digiri 273 debewa a ma’auni.
Yanayin sanyin da ke cikin taurari kuwa ya kai miliyoyin digiri a ma’auni.
Manyan manyan duwatsu ke harbawa da karfin gaske suna tarwatsa cikin holokon sararin samaniya.
Ka yi tunanin naka muhallin a cikin wannan holokon sararin duniya marar iyaka...
Don gano haka, bari mu fara kwatanta yanayin nisan wurare a wannan duniya tamu da nisan wurare a sararin sama.
A cikin sararin sama, nisan da ke tsakanin taurari mafiya kusanci da juna shi ne kilomita tiriliyan 30. A gaba dayan taurarin da ke haskawa a sama, wadda ta fi kusa da kai ita ce mai nisan kilomita tiriliyan dubu biyar.
To yanzu bari mu dubi yadda matsayin duniyarmu ya ke a cikin gungun taurari da ke sararin sama.
Akwai kimanin taurari bilyan 250 da ke yawo a cikin gungun taurarin.
Daga cikin su akwai rana.
Akwai wasu duniyoyi guda tara da suke kewaya rana bisa kyakkyawan tsari. Wadannan gaba daya su a ke kira da kwambar duniyoyi majibinta rana. A cikin wannan kwambar, wadda fadinta ya kai murabba’in kilomita bilyan 12, za ka sami duniyarmu ‘yar mitsitsiyar gaske.
In za ka dauki duniyarmu a matsayin dan ludo, to rana za ta kasance kwatankwacin girman kwallon kafa da ke nisan mita 280 daga dan ludon...
Duk da yawan fadadan duniyoyin da ke cikin gungun taurarin, gaba dayan gungun karami ne a cikin sararin subhana mai gungun duniyoyi bilyan dari uku (300).
Ba ma abin mamaki da kayatarwa kamar yanayin motsi da tafiyar duniyoyi da taurari a sararin sama.
Wannan duniya da mu ke ciki tana mirginawa a cikin sasanninta a gudun kilomita 1,670 a kowace sa’a guda.
A lokaci guda kuma tana zagaya rana, wadda ta linka duniyar sau 103 a girma.
Duniyar tana wannan zagaye (na rana) ne a gudun kilomita dubu dari da takwas a sa’a guda. Wato gudunta yafi tafiyar harsashi da linki sittin.
A daidai haka kuma, duniyarmu da rana suna fuskantar tauraro “vega” a gudun kilomita 200 cikin dakika guda. Wannan yana nufin suna tafiyar kilomita dubu dari bakwai da ashirin a cikin sa’a guda.
Sannan kuma shi kan sa gungun duniyoyin yana tafiya.
Sannan kuma ko a jikinmu ba ma sanin irin wannan gagarumar tafiya da a ke yi da mu a kowane lokaci.
Ba ma sanin ana tafiyar ne, saboda lamarin yana tafiya ne bisa tabbataccen tsarin Allah mahalicci.
Shin ko ka taba tunani kan dalilin da ya sa ba ma taba sanin a na wannan tafiya?
A yanzu, daidai wannan lokaci da ka ke kallon wannan shiri, ba ka jin wata girgizza ko tangal tangal. Yayin da ka ke zaune a lambun shakatawa ko kuma kana tafiya ne a kan titi, ba ka da masaniyar cewa duniya tana juyawa... Amma duniyar nan wata katuwar shigifa ce da take fesa gudu a sararin subhana a kan gudun kilomita 200 a kowace dakika. Motsi guda kawai, mun ci gudun kilomita 200, a wani motsin mun ci 400, sai 600...
DARASI DAGA GANGAR JIKIN MUTUM
Yayin da rana ta fito, to gari ya waye kenan, an shiga wata ranar.
Hakika ba karamar mu’ujiza ba ce yadda mutum ya ke tashi lafiyayye a kowace safiyar Allah.
Duk da ya ke cewa yayin barci mutum yana fita daga hayyacinsa, amma ya kan tashi washe gari cikin hayyaci da sururi kamar yadda ya ke kafin ya kwanta barcin.
Sa’annan kuma ya kan iya tunani, da magana, da gani.
Sai dai yayin da ya ke barci da dare, ba shi da tabbas cewa zai sake samun irin waccan rahama washe gari.
Wajibi ne ga mutane su yi nazari kan wannan, su gane irin falala da kariyar da Allah ya yi musu don su kara gode masa.
Wajibi ne ga mutane su yi tunani kan raunin halittarsu: Kamar yadda Allah ya fada a cikin Alkur’ani sura ta 4 aya ta 28 cewa: “An halicci mutum yana mai rauni.”
Idan mutane ba sa lura da abinda suke ci, da abinda suke sha ko tufafin da suke sanyawa a jikinsu, suna iya kamuwa da rashin lafiya...
Kwayar cuta daya tak wadda ido ba ya iya gani ita kadai ta isa ta kwantar da mutum mai nauyin kilo 60 zuwa 70. Marar lafiya kuwa ba abin da ya ke iya yi ban da kwanciya a gado.
A yayin wannan hali kuwa marar lafiyar ba shi da ikon komai, jidali ne ke afkuwa a cikin jikin.
Duk irin tsananin kiyayewarsa da ka’idojin da likita ya sanya masa, Allah mahalicci shi ne kadai zai iya dawo masa da lafiya da kuma karfin jikinsa. Don haka, zai yi kyau mu tuna abin da Ibrahim (AS) ya fada a cikin Alkur’ani cewa: “(Allah) Shi ne wanda ya ke ciyarwa ya shayar da ni, kuma yayin da na kamu da rashin lafiya, shi ne ke warkar da ni.” (Sura ta 16, aya ta 79 – 80).
An gina gangar jikin mutum bisa tsarin ilimin Allah mabuwayi. Hatta gashin kansa. Hatta gashin gira da na idanun mutum a kayyade suke. Rashin tofon su fiye da kima amfani ne gare mu. Amma kuwa gashin kan mutum, wanda ke taimakawa wajen fitar kyawun sigar mutum, ya kan ci gaba da tofo a tsawon rayuwarmu, kuma mu kan iya yin ado da shi ta sigar da muke so. Yanzu ka yi tunani kan wannan: idan gashin idanunka zai yi tofo ya girma kamar gashin kanka, me ka ke tsammanin zai faru? Wa ye ya hana gashin girar idonka ci gaba ta tofo, ya dakatar da shi a wani ma’auni? Mutumin da ya ke lura da irin wadannan al’amuran baiwa to shi zai fi saurin gane cewa kowane sashe na jikin mutum, kowace gaba da tsoka ta jikin an halicce ta ne bisa kwarewa da kyakyawan tsari.
Akwai matukar tsari da gayar hikima a yadda kasusuwan mutum ke tofo suna kara girma.
Kwakwalwar dan Adam tana fara habaka ne tun daga kuruciyarsa. A lokaci guda kuma kokon kansa shi ma yana kara girma da fadada. Idan girman kokon kai da na kwakwalwa ba sa tafiya tare, in har kokon kan ya yi kankanta ya matse kwakwalwar to tana iya yin bindiga ta fashe. Amma hakan ba ya faruwa. Kokon kai da kwakwalwa girman su tare ya ke tafiya har zuwa wani mataki inda kokon kan kan rufe kwakwalwar ruf kamar keji.
Ta ya ya kasusuwa, wadanda ke girma suna habaka tare, su ke sanin sun kai matakin karshen girmansu? Me zai faru in har kasusuwan suka ci gaba da girma?
Misali, da kasusuwan kirjin mutum za su ci gaba da girma har su wuce ka’idarsu, da sai a ga sun tsaga nama sun fito waje.
Amma saboda cikar tsarin halittar kasusuwan, hakan ba ya taba faruwa.
Kwayoyin halittar kashi su ke suranta kowane kashi kamar yadda masassaki ke suranta itace. Su ke fitar da sigar kowane kashi da mulmula shi sannan su dakatar da girmansa a daidai inda ya dace.
Ya kamata mu yi tunanni a kan wannan.
Shin kwayar halittar kashi tana da sani ne da hankali da kuma tsari da lura na yin duk wadannan abubuwa da muka zana?
Ta ya ya ta ke sanin inda za ta tsaya da kuma daga inda za ta ci gaba?
Koda ya ke dukkan kasusuwan da ke jikinmu sun samu ne daga tushen kwayar halittar kashi daya, amma ta ya ya a ke samun wasu sandararru da kuma wadanda a ke iya lankwasawa?
Shin wa ya tsara wa kasusuwa aikinsu a gangar jiki?
Ta ya ya nau’in kananan kasusuwa da ke hannayenmu suka san yadda za su sarrafa hannayen?
Ta ya ya kasusuwan hannaye, da kafafuwa da kuma na yatsunmu suke isa matsayin da a ke bukata kafin tsarin jiki ya daidaita?
Wadannan tambayoyi ne da ya kamata mu tambayi kanmu don mu iya fahimtar yadda tsarin tafiyar da halittar jkin mutum ya ke.
Sai dai abu ne mai wuya a dauka cewa duk wadannan abubuwa sun samu ne a bisa katari ko dace; ba shi yiwuwa a ce kwayoyin halitta wadanda su ne tushen samuwar mutum da kuma sassan da suka hadu suka gina kwayoyin halittar suna da ikon haifar da abu a radin kan su. Kowane daya daga cikin wadannan abubuwan halitta alama ne da ke nuna fasahar Allah wanda ya halicci mutum kuma ya tsara halittarsa. A wata ayar Alkur’ani Allah yana cewa:
.. Kuma ka duba zuwa ga ƙasũsuwa yadda Muke mõtsarda su sa´an nan kuma Mu tufãtar da su, da nãma... (Sura ta 2 aya 159).
DARASIN DA ZA MU KOYA A CIKIN ABINCI
Allah, a rahamarsa, ya halicci abubuwa mabambantan dandano ga bayinsa don su ci su sha daga gare su. Wannan rahama tana nuna matsayin Allah mai kyautar baiwa ne ga bayinsa:
Allah ne... Ya azurta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Wancan Shĩne Allah Ubangijinku. To, albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana. (Sura 40 aya 64).
Da Allah ya ga dama da sai ya kasance abinci kala daya kawai a duniya. Amma saboda ‘yan Adam su gode masa, sai ya halitta musu nau’in abubuwa don rahamarsa.
Wannan rahamar Allah ce da ludufinsa ga bayinsa.
A cikin kowane nau’in abinci da abin sha akwai abubuwan lura da ke tunatar da mu dimbin ni’imomin Allah gare mu.
Ga misali, mafi yawan ‘ya’yan itace an halicce su ne da bawonsu. Wadannan bawo ko fata su kan kare su daga lalacewa ko rubewa, sannan suna kare su daga datti inda hakan ke kara musu kyau da kamshi.
‘Ya’yan itace irin su lemon zaki, da sauran nau’in ‘ya’yan itace masu kunshe da sinadarin vitamin C mai yawa a cikinsu, an tsara su ne don saukin ci. Irin wadannan ‘ya’yan itace suna yin ýaýa ne a lokacin yanayin sanyi lokacin da mutane suka fi bukatar sinadarin vitamin C...
A lokacin zafi a na matukar bukatar ruwa. Don haka, a wannan yanayi a ke samun ‘ya’yan itace kamar su kankana da tufa da sauran ire irensu a wadace.
Duk wannan yana nuna cewa Allah ya halicci ‘ya’yan itace ne don amfanin bani-Adama...
Ganin yadda dan itace ke habaka a gan shi ya nuna yana lilo a jikin rassan bishiyoyinsa shi ma wata kyakkyawar baiwa ce ta Allah ga ‘yan Adam.
Dandazon ‘ya’yan itacen tufa masu launin kore ko ja da kuma sauran ‘ya’yan itace nau’inta...
Idan ka bara dan itacen kiwi zuwa bari biyu, za ka ga kyakkyawan tsarin halittarsa mai burgewa. Wani kuma dan itacen da a ka sani wajen kyawun tsarin halittar sa shi ne garahuni, za ka gan shi jawur a tsakiyar koren ganyensa. Duk da yake cewa duk wadannan ‘ya’yan itace sun fito ne daga kasa wadda ta ke mai duhu, amma kowannensu ya sha bamban da irin dandano da kamshinsa, da kuma launin jikinsa mai kyau. Har ila yau, suna kara nuna mana gwanintar halittar Ubangiji, iliminsa mayalwaci da kuma hikimarsa a cikin ayyukansa.
A cikin wata ayar Alkur’ani, Allah yana umartar bani-Adama da su yi tunani a kan wannan baiwa da ya yi musu:
Kuma Shi ne Ya saukar da ruwa daga sama, Muka fitar da tsiron dukkan kõme game dã shi, sa´an nan Muka fitar da kõre daga gare shi, Muna fitar da kwãya ɗamfararriya daga gare shi (kõren),kuma daga dabĩno daga hirtsinta akwai dumbuje-dumbuje makusanta, kuma (Muka fitar) da gõnaki na inabõbi da zãitũn da ruman, mãsu kamã da jũna da wasun mãsu kama da jũna. Ku yi dũba zuwa ´ya´yan itãcensa idan ya yi ´ya´yan, da nunarsa. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga waɗanda suke yin ĩmãni.
ABUBUWAN IZNA A CIKIN YANAYI DUNIYA
Da za ka fita waje ka dan zagaya a cikin sarari, za ka ga wasu abubuwa masu kyau da ka iya daukar idonka: kamar kyawun furanni masu launi, ko koriyar ciyawa ko gona, ko kuma ‘yar karamar tururuwa...
Hatta ‘yar karamar tururuwa da ka ke gani, an halicce ta da siffofi masu ban al’ajabi. Wannan mitsitsiyar kwaruwa ta kan iya gutsuttsura ganye da bakinta, ko ta dauki abubuwan da suka fi girman jikinta kuma har ta kai su cikin gidanta a saukake.
Ta kan iya doguwar tafiya mai nisa duk kuwa da kankantar ta. Kuma duk inda ta je ba ta mance hanyar komawa gidanta. Tabbas, wannan ‘yar karamar halitta a radin kanta ba za ta iya kididdige wadannan abubuwa ba. Allah ne mahalicci ke kimsa mata yin hakan da ludufin sunansa mai jinkai.
Yadda garahuni ke yado a jikin rassan bishiyoyi ko kuma a jikin bango ko wani abu, al’amari ne da ya kamata mu yi tunani da lura a kan sa. Da za a yi rikodin din wannan yado a faifan bidiyo sannan daga bisani a kalle shi a yanayin saurin hoton bidiyon, za ka ga yadda garahunin ke motsi kamar wanda ke da rai. Kai ka ce ya hango wani reshe ne a nan kusa inda ya kan cafko shi ya hade da shi. Wani sa’ilin ma ya kan kanannade jikin reshen ne. A haka ya ke bazuwa cikin sauri, sannan bayan ya gama yadon ta fuska guda, sai kuma ya koma kasan sannan ya sake daukar wani bangaren daban.
Wani kuma abu daga cikin kyawun halittar Allah shi ne kamshin da furanni ke fitarwa. Misali, akwai irin filawar da ke fitar da wani yanayin kamshi mai karfin gaske da ke dume guri. Hatta irin turaren kamfani da a ke yi ya gaza kai kamshinta. Lokacin da masu gwaje gwajen kimiyya suka yi kokarin kirkiro kwatankwacin kamshinta, karshe abin ya faskara. Yawancin irin turaren kamshin da suka samar su kan kasance masu karfi da duma kai. Ko kuma kamshin kan gushe cikin dan lokaci kadan.
Amma shi kamshin fure ba ya dimautar da mutum. Koda ka tsinke furen daga jikin filawa to zai ci gaba da fitar da kamshinsa har sai lokacin da ya bushe.
Wata mu’ujizar ta Allah kuma ita ce ta bishiyoyi da ke daukar ruwa su kai shi sama har na nisan mitoci. Shin ka taba tsayawa ka yi tunani kan yadda ruwa kan isa can saman rassa da ganyen dogayen bishiyoyin da ka ke gani?
Bishiyoyi suna tsotso ruwa daga cikin zurfin kasa zuwa saman rassan su. Su kan yi hakan ne ba tare da wani famfo ko inji ba.
Domin fahimtar wannan kyakkyawar hikimar halitta, bari mu duba wani misali: A kan yi amfani da famfo don turo ruwa zuwa saman bene. Ba don wannan famfo ko wani abu makamancinsa ba, ba yadda za iya tura ruwa koda zuwa hawa daya na bene.
Sai dai kuma bishiyoyi su kan yi wannan aikin ba tare da famfo ko wani inji ba. Amma su kan iya jawo ruwa su shayar da rassa da ganyensu na can sama.
Saiwoyi masu kamar bututu da ke cikin jijiya da gangar jikin bishiya an yi su ne ta yadda ruwa zai iya wucewa ta cikinsu. Yayin da ruwa ya taso sama, jijiyoyin su kan tsuke don ruwan ya sami damar wucewa. ‘Ya’yan halittar da ke cikin ruwa suna yin gogoriyo da juna yayin da a ke tunkuda ruwan zuwa kololuwar saman ganye.
Allah Ubangiji shi ne ya halicci tsarin saiwoyi (ko hanyoyin ruwa) a jikin kowane ganye tare da tsarin ruwa don lamarin ya tafi daidai. Kamar yadda ya zo a wannan aya ta Alkur’ani, Allah wanda tausayi da rahamarsa ba su da iyaka, ya halicci bishiyoyi da sauran tsirrai don amfanin mutane da sauran abubuwa masu rai:
Allah ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa´an nan Ya fitar game da shi, daga ´ya´yan itãce arziki dõminku... (Sura ta 14 aya 32)
ABABEN LURA A RAYUWAR YAU DA KULLUM
Kullum a akwatunan talbijin din mu mu kan ga labaran ta’addanci da sauran nau’in mugayen ayyuka. Babban abin da ke haddasa wadannan abubuwa shine saboda cewa wadansu mutane suna gudanar da rayuwarsu ba a kan kyakkyawan tsarin rayuwa wanda Allah mahalicci ya dora mu a kai ba. Mafi yawan mutanen da ke gudanar da rayuwarsu sabanin yadda addini ya tsara su ne kan iya aikata ta’addanci a kan sauran mutane ba tare da jin komai a ran su ba, tun da ba su da imani.
Rashin jin tsoron Allah yadda ya kamata a tsorace shi shine babban dalilin da ke sa mutane su fada cikin ayyukan ta’addanci da barna; alhali suna sane ne ko kuma saboda jahlci sun kasa sanin cewa Allah zai tambaye su a kan rayuwarsu a duniya.
Amma kuma kyakkyawar niyya, da amana, da tausayi, gaskiya sadaukar da kai da sauran kyawawan dabi’u wadanda addini ya koyar su ne ke bude hanyar zaman lafiya, da tsaro da kuma adalci a cikin al’umma.
Sau da yawa mu kan ji labaran annoba iri iri a kafafen watsa labarai. Mutum kan iya gamuwa annoba ko hatsari a wannan duniya. Wani lokacin, ba zato ba tsammani, mu kan ga wata gagarumar girgizar kasa ta afku, ko kuwa gobara ko ambaliyar ruwa su faru.
Annobar yanayi, cikin kankanin lokaci ta kan iya shafe duk wani gini ko kayan kere kere da ke baiwa mutane kariya. Cikin dakika daya kawai, abubuwan da mutane suka mallaka kamar gidaje da motoci, har ma da su kan su mutanen suna iya salwanta.
Mutumin da ke sauraron irin wadannan labarai na annoba zai san cewa ba shi da wata mafita face ya koma ga Allah mai ikon komai. Ga abin da Allah ya ke fada mana a cikin Alkur’ani:
15; Yã kũ mutãne! Kũ ne mãsu bukãta zuwa ga Allah, kuma Allah, Shĩ ne Mawadãci, Abin godewa (Sura ta 35 aya 15)
ABIN DA ALKUR’ANI YA KE FADA
118.Allah ya saukar da Alkur’ani don ya zama shiriya ga mutane. Don haka, abin da ya kamaci mutum shine ya tsaya ya yi tunani da nazari a kan kowace aya ta Alkur’ani. A cikin Alkur’anin, Allah yana kira gare mu da mu yi nazari a kan abubuwa masu yawa. Misali, yana kiran mu da yin tunani kan halittar jikinmu...
To, mutum ya yi dũba, daga me aka halicce shi? An halicce shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna. (Sura ta 86 aya 5 – 6)
Allah yana so mu yi tunani a kan halittar sammai da kasa...
Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa da sãɓãwar dare da yini akwai ãyõyi ga ma´abota hankali.Waɗanda suke ambatar Allah a tsaye da zaune da kuma a kan sãsanninsu, kuma suna tunãni a kan halittar sammai da ƙasa: "Yã Ubangijinmu! Ba Ka halitta wannan a banza ba. Tsarki ya tabbata gareKa! Ka tsare mu daga azãbar wuta. (Sura ta 3 aya 190 – 191)
Allah yana kiranmu da mu yi tunani kan rayuwar duniya wadda ba ta dauwama...
Kuma wannan rãyuwa ta dũniya ba ta zamo ba, fãce abar shagala da wãsã kuma lalle Lãhira tabbas, ita ce rãyuwa, dã sun kasance sunã sani. (Sura 29 aya 64)
Sabõda haka abin da aka bã ku, kõ mene ne, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne, kuma abin da ke a wurin Allah Shĩ ne mafĩfĩci,kuma Shĩ ne mafi wanzuwa ga waɗanda suka yi ĩmãni kuma suke dõgara ga Ubangijinsu kawai. (Sura ta 42 aya 36)
Allah yana sanar da mu don mu hankalta mu lura cewa duniya baki dayanta ya halicce ta ne don bil-Adama...
13; Kuma Ya hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasa, gabã ɗaya daga gare Shi yake. Lalle ne, a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni. (Sura 45 aya ta 13)
Allah yana kiranmu da mu yi tunani kan sauran abubuwa masu rai da ya halitta...
Lalle kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni´ima; Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikin cikunansu, daga tsakãnin tukar tumbi da jini, nõno tsantsa mai sauƙin haɗiya ga mãsu shã. (Sura ta 16 aya 66)
Haka nan kuma Allah yana kiranmu don mu yi tunanin ranar lahira, ranar tashi kuma ranar sakamako...
30; A Rãnar da kõwane rai yake sãmun abin da ya aikata na alheri da kuma na sharri, a halarce, alhãli yana gũrin dã ace akwai fage mai nĩsa a tsakãninsa da abin daya aikata na sharrin! Allah Yanã tsõratar da kũ kanSa. Kuma Allah Mai tausayi ne ga bãyinSa. (Sura ta 3 aya 30)
KAMMALAWA
131.Mutumin da ke yin tunani da tafakkuri shi ke fahimtar sirrin halittar Allah da kuma yadda hakikanin rayuwar wannan duniya ta ke. Zai gane alamomin Allah a cikin kowane abu. Sabanin mafi yawan mutane, zai kasance a tsawon rayuwar sa yana tunanin yadda ya zo duniya da yadda ya ke rayuwa. Ta hanyar ilimin da Ubangiji ya sanar da shi ya ke yin tunani daidai yadda Ubangiji ya umarta.
Saboda haka shine zai fi kowa ni’imta da rahamar Allah da tagomashinsa, haka kuma ba abin da zai dame shi na daga al’amuran duniya masu sanya damuwa a zukatan mutane.
Wadannan kadan ne daga cikin manyan abubuwan daukaka da irin wannan mutum mai tunani zai samu a rayuwar duniya. Ta hanyar tunani da kuma gane gaskiya a rayuwarsa, a ranar lahira, wannan mutum zai sami soyayyar Allah, da yardarsa, da rahamarsa da kuma aljannarsa.
Allah madaukakin sarki yana kira ga mu bayinsa zuwa ga hanya mafita don mu rabauta:
43; Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini madaidaici tun kafin wani yini ya zo, bãbu makawa gare Shi daga Allah, a rãnar nan mutãne sunã tsãgewa (su rabu biyu).Wanda ya kãfirta,to,kãfircinsa na kansa, kuma wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, sabõda kansu suke yin shimfiɗa. Dõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga falalarSa. Lalle Allah bã Ya son kafirai. (Sura ta 30 aya 43 – 45)