1. Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta.
2. Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi.
3. Kuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta?"
4. A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta.
5. cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta.
6. A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu.
7. To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi.
8. Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.