1. Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.
2. Da Dũr Sĩnĩna.
3. Da wannan gari amintacce.
4. Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
5. Sa`an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
6. Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
7. To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?
8. Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?