1. Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari ba.
2. Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari.
3. Da mahaifi da abin da ya haifa.
4. Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala.
5. Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa?
6. Yana cẽwa "Na halakarda dũkiya mai yawa,"
7. Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba?
8. Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba?
9. Da harshe, da leɓɓa biyu.
10. Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi biyu ba?
11. To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba?
12. Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã?
13. Ita ce fansar wuyan bãwa.
14. Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma`abũcin yunwa.
15. Ga marãya ma`abũcin zumunta.
16. Ko kuwa wani matalauci ma`abũcin turɓãya.
17. Sa`an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi.
18. Waɗannan ne ma`abũta albarka
19. Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyinMu, sũ ne ma`abũta shu`umci
20. A kansu akwai wata wuta abar kullewa.