1. Suna tambayar ka ga ganĩma. ka ce: "Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã`a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance mũminai."
2. Abin sani kawai, nũminai sũ ne waɗanda suke idan an ambaci, Allah, zukãtansu su firgita, kuma idan an karanta ãyõyinSa a kansu, su ƙãrã musu wani ĩmãni, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara.
3. Waɗanda suke tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azũrtã su sunã ciyarwa.
4. Waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya. Sunã da darajõji a wurin Ubangijinsu, da wata gãfara da arziki na karimci.
5. Kamar yadda Ubangijinka Ya fitar da kai daga gidanka da gaskiya, alhãli kuwa lalle wani ɓangare na mũminai, haƙĩƙa, sunã ƙyãma.
6. Sunã jãyayya da kai a cikin (sha`anin) gaskiya a bãyan tã bayYanã, kamar dai lalle anã kõra su zuwa ga mutuwa ne alhãli kuwa sunã kallo.
7. Kuma a lõkacin da Allah Yake yi muku alkawari da ɗayan ƙungiya biyu, cẽwa lalle ita tãku ce: kuma kunã gũrin cẽwa lalle ƙungiya wadda bã ta da ƙaya ta kasance gare ku, kuma Allah Yanã nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kuma Ya kãtse ƙarshen kãfirai;
8. Dõmin Ya tabbatar da gaskiya, kuma Ya ɓãta ƙarya, kuma kõdã mãsu laifi sun ƙi.
9. A lõkacin da kuke nẽman Ubangijinku tairnako, sai Ya karɓa muku cẽwa: "Lalle ne Nĩ, Mai taimakon ku ne da dubu daga malã`iku, jẽre."
10. Kuma Allah bai sanya shi ba fãce Dõmin bishãra, kuma dõmin zukãtanku su natsu da shi, kuma taimakon, bai zama ba fãce daga wurin Allah; Lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.
11. A lõkacin da (Allah) Yake rufe ku da gyangyaɗi, ɗõmin aminci daga gare Shi, kuma Yanã saukar da ruwa daga sama, a kanku, dõmin Ya tsarkake ku da shi, kuma Ya tafiyar da ƙazantar Shaiɗan daga barinku, kuma dõmin Ya ɗaure a kan zukãtanku, kuma Ya tabbatar da ƙafãfu da shi.
12. A lõkacin da Ubangijinka Yake yin wahayi zuwa ga Malã`iku cẽwa: "Lalle ne Ni, Inã tãre da ku, sai ku tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni: Zã Ni jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta, sai ku yi dũka bisa ga wuyõyi kuma ku yi dũka daga gare su ga dukkan yãtsu.
13. Wancan ne, dõmin lalle ne sũ, sunã sãɓa wa Allah da ManzonSa. Kuma wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, to, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.
14. Wancan ne: "Ku ɗanɗane shi, kuma lalle ne akwai azãbar wuta ga kãfirai."
15. Yã kũ wacɗanda suka yiĩmãni! Idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta ga yãƙi, to, kada ku jũya musu bãyayyakinku.
16. Kuma duka wanda ya jũya musu bãyansa a yinin nan, fãce wanda ya karkata dõmin kõɗayya, kõ kuwa wanda ya jẽ dõmin haɗuwa da wata ƙungiya, to, lalle ne ya kõma da fushi daga Allah, kuma matattararsa Jahannama, kuma tir da makõma ita!
17. To, bã kũ ne kuka kashe su ba; kuma amma Allah ne Ya kashe su: kuma ba ka yi jĩfa ba a lõkacin da ka yi jĩfa; kuma amma Allah ne Ya yi jĩfar. Kuma dõminYa jarraba Musulmi da jarrabãwa mai kyau daga gare shi. Kuma Allah Mai ji ne, Masani.
18. Wancan ne, kuma lalle ne, Allah Mai raunana kaidin kãfirai ne.
19. Idan kun yi alfãnun cin nasara to lalle nasarar tã je muku, kuma idan kun hanu, to Shi ne Mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun kõma zã Mu kõma, kuma jama`arku bã zã ta wadãtar muku da kõme ba, kõ dã tã yi yawa. Kuma lalle ne cẽwa Allah Yanã tãre da mũminai!
20. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã`a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku jũya daga barinSa, alhãli kunã ji.
21. Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka ce: "Mun ji, alhãli kuwa sũ bã su ji."
22. Lalle ne, mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne kurãme, bẽbãye, waɗanda bã, su yin hankali.
23. Dã Allah Yã san wani alhẽri a cikinsu, dã Yã jiyar da su, kuma kõ da Yãjiyar da su, haƙĩƙa, dã sun jũya, alhãli sũ, sunã mãsu hinjirẽwa.
24. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku karɓa wa Allah, kuma ku karɓa wa Manzo, idan Ya kirãye ku zuwa ga abin da Yake rãyar da ku; Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã shãmakacẽwa a tsakãnin mutum da zũciyarsa, kuma lalle ne Shĩ, a zuwa gare Shi ake tãra ku.
25. Kuma ku ji tsõron fitina wadda bã ta sãmun waɗanda suka yi zãlunci daga gare ku kẽɓe, kuma ku sani, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.
26. Ku tuna a lõkacin da kuke kaɗan, waɗanda ake raunanarwã a cikin ƙasa kunã tsõron mutãne su cafe ku, sai Ya tattara ku (a wurin natsuwa, Maɗina), kuma Ya ƙarfafã ku da taimakonSa kuma Ya azurtã ku daga abũbuwa mãsu dãɗi; Tsammãninku, kunã gõdẽwa.
27. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yaudari Allah da ManzonSa, kuma ku yaudari amãnõninku, alhãli kuwa kunã sane.
28. Kuma ku sani cẽwa abin sani kawai, dũkiyõyinku da `ya`yanku, wata fitina ce, kuma lalle ne Allah, a wurinSa, akwai ijãra mai girma.
29. Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun bi Allah da taƙawa, zai sanyã muku mararraba (da tsõro) kuma Ya kankare ƙanãnan zunubanku daga barinku. Kuma Ya gãfartã muku. Kuma Allah ne Ma`abũcin falalã Mai girma.
30. Kuma a lõkacin da waɗanda suka kãfirta sukẽ yin mãkirci game da kai, dõmin su tabbatar da kai, kõ kuwa su kashe ka, kõ kuwa su fitar da kai, sunã mãkirci kuma Allah Yanã mayar musa da mãkirci kuma Allah ne Mafificin mãsu mãkirci.
31. Kuma idan aka karanta, ãyõyinMu a kansu, sukan ce: "Lalle ne mun ji dã muna so, haƙĩƙa, da mun faɗi irin wannan; wannan bai zama ba fãce tãtsunãyõyin mutãnen farko."
32. A lõkacin da suka ce: "Yã Allah! Idan wannan ya kasancc shĩ ne gaskiya daga wurinKa, sai Ka yi ruwan duwãtsu, a kanmu, daga sama, kõ kuwa Kazõ mana da wata azãba, mai raɗaɗi."
33. Kuma Allah bai kasance Yanã yi musu azãba ba alhãli kuwa kai kanã cikinsu, kuma Allah bai kasance Mai yi musu azãba ba alhãli kuwa sunã yin istigfãri.
34. Kuma mẽne ne a gare su da Allah ba zai yi musu azãba ba, alhãli kuwa sũ, sunã kangẽwa daga Masallaci Mai alfarma kuma ba su kasance majiɓintanSa ba? Bãbu majiɓintanSa fãce mãsu taƙawa. Kuma mafi yawansu ba su sani ba.
35. Kuma sallarsu a wurin ¦ãkin ba ta kasance ba fãce shẽwa da yãyã; sai ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci.
36. Lalle ne waɗanda suka kãfirta, sunã ciyar da dũkiyõyinsu, dõmin su kange daga hanyar Allah; to, zã a su ciyar da ita, sa` an nan kuma ta kasance nadãma a kansu, sa`an nan kuma a rinjãye su. Kuma waɗanda suka kãfirta zuwa ga Jahannama ake tãra su;
37. Dõmin Allah Ya rarrabe mummũna daga mai kyau, kuma Ya sanya mummũnan, sãshensa a kan sãshe, sa`an nan Ya shirga shi gabã daya, sa`an nan Ya sanyã shi a cikin Jahannama. Waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
38. Ka ce wa waɗanda suka kãfirta, idan sun hanu, zã a gãfarta musu abin da ya riga ya shige, kuma idan sun kõma, to, hanyar kãfiran farko, haƙĩƙa, ta shũɗe.
39. Kuma ku yãƙe su har wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini dukansa ya kasance na Allah. To, idan sun hanu to lalle ne, Allah ia abin da kuke aikatãwa Mai gani ne.
40. Kuma idan sun jũya, to, ku sani cẽwa lalle Allah ne Majiɓincinku: Mãdalla da Majiɓinci, kuma mãdalla da Mai taimako, Shĩ.
41. Kuma ka sani, abin sani kawai, abin da kuka sãmi ganĩma daga wani abu, to, lalle ne Allah Yanã da humusinsa kuma da Manzo, kuma da mãsu zumunta, da marãyu da miskĩnai da ɗan hanya, idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah da abin da Muka saukar a kan bãwanMu a Rãnar Rarrabẽwa, a Rãnar da jama`a biyu suka haɗu, kuma Allah ne, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi.
42. A lõkacin da kuke a gãɓa ta kusa sũ kuma sunã a gãɓa tanẽsa, kuma ãyarin yana a wuri mafi gangarãwa daga gare ku, kuma dã kun yi wa jũna wa`adi, dã kun sãɓa ga wa`adin; kuma amma dõmin Allah Ya hukunta abin da yake ya kasance abin aikatãwa. Dõmin wanda yake halaka ya halaka daga shaida, kuma mai rãyuwa ya rãyu daga shaida, kuma lalle Allah ne, haƙĩƙa, Mai ji Masani.
43. A lõkacin da Allah Yake nũna maka sũ sunã kaɗan, a cikin barcinka, kuma dã Ya nũna maka su sunã da, yawa, lalle ne dã kun ji tsõro, kuma lalle ne dã kun yi jãyayya a cikin al`amarin, kuma amma Allah Yã tsare ku: Lalle Shĩ ne Masani ga abin da yake a cikin ƙirãza.
44. Kuma a lõkacin da Yake nũna muku su, a lõkacin da kuka haɗu, a cikin idanunku sunã kaɗan, kuma Ya ƙarantar da ku a cikin idanunsu dõmin Allah Ya hukunta wani al`amari wanda ya kasance abin aikatãwa. Kuma zuwa ga Allah ake mayar da al`umurra.
45. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun haɗu da wata ƙungiyar yãƙi, to, ku tabbata, kuma ku ambaci Allah da yawa, tsammãninku kunã cin nasara.
46. Kuma ku yi ɗã`a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku yi jãyayya har ku raunana kuma iskarku ta tafi, kuma ku yi haƙuri. Lalle ne Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri.
47. Kada ku kasance kamar waɗanda suka fita daga gidãjensu, sunã mãsu alfahari da yin riya ga mutãne, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma Allah ne ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa.
48. Kuma a lõkacin da Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, kuma ya ce: "Bãbu marinjayi a gareku a yau daga mutãne, kuma nĩ maƙwabci ne gare ku." To, a lõkacin da ƙungiya biyu suka haɗu, ya kõma a kan digãdigansa, kuma ya ce: "Lalle ne nĩ barrantacce ne daga gare ku! Nĩ inã ganin abin da bã ku gani; ni inã tsõron Allah: Kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne."
49. A lõkacin da munãfukai da waɗanda suke akwai cũtã a cikin zukãtansu, suke cẽwa: "Addĩnin waɗannan yã rũɗe su" Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.
50. Kuma dã kã gani, a lõkacin da Malã`iku suke karɓar rãyukan waɗanda suka kãfirta, sunã dukar fuskõkinsu da ɗuwãwunsu, kuma suna cẽwa: "Ku ɗanɗani azãbar Gõbara."
51. "Wancan sabõda abin da hannãyenku suka gabãtar ne. Kuma lalle ne, Allah bai zama Mai zãlunci ba ga, bãyinSa."
52. "Kamar al`ãdar mutãnen Fir`auna da waɗanda suke gabãninsu, sun kãfirta da ãyõyin Allah, sai Allah Ya kãma su da zunubansu. Lalle Allah ne Mai ƙarfi, Mai tsananin uƙũba.
53. "Wancan ne, dõmin lalle ne, Allah bai kasance Mai canza wata ni`ima wadda ya ni`imtar da ita a kan wasu mutãne ba fãce sun sãke abin da yake ga rãyukansu, kuma dõmin lalle Allah ne Mai jĩ, Masani."
54. Kamar al`adar mutãnen Fir`auna da waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata game da ãyõyin Ubangijinsu, sai Muka halaka su, sabõda zunubansu, kuma Muka nutsar da mutãnen Fir`auna. Kuma dukansu sun kasance ne mãsu zãlunci.
55. Lalle mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne waɗanda suka kãfirta, sa`an nan bã zã su yi ĩmãni ba.
56. Waɗanda ka yi ƙullin alkawari da su, daga gare su, sa`an nan kuma sunã warwarewar alkawarinsu a kõwane lõkaci kuma sũ, bã su yin taƙawa.
57. To, in dai ka kãma su a cikin yãƙi, sai ka kõre waɗanda suke a bãyansu, game da su, tsammãninsu, zã su dinga tunãwa.
58. Kuma in ka ji tsõron wata yaudara daga wasu mutãne, to, ka jẽfar da alkawarin, zuwa gare su, a kan daidaita: Lalle ne Allah, bã Ya son mayaudara.
59. Kuma waɗanda suka kãfirta kada su yi zaton sun tsẽre: Lalle ne sũ, bã zã su gãgara ba.
60. Kuma ku yi tattali, dõminsu, abin da kuka sãmi ĩkon yi na wani ƙarfi, kuma da ajiye dawaki, kunã tsoratarwa, game da shi, ga maƙiyin Allah kuma maƙiyinku da wasu, baicin su, ba ku san su ba, Allah ne Yake sanin su, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu a cikin hanyar Allah, zã a cika muku sakamakonsa, kuma kũ ba a zãluntar ku.
61. Kuma idan sun karkata zuwa ga zaman lãfiya, to, ka karkata zuwa gare shi, kuma ka dõgara ga Allah: Lalle ne Shĩ, Mai ji ne Masani.
62. Kuma idan sun yi nufin su yaudare ka, to, lalle ma`ishinka Allah ne, Shĩ ne wanda Ya ƙarfafa ka da taimakonSa, kuma da mũminai.
63. Kuma Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu. Dã kã ciyar da abin da yake cikin ƙasa, gabã ɗaya, dã ba ka sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu ba, kuma amma Allah Yã sanya sõyayya a tsakãninsu. Lalle Shi ne Mabuwãyi, Mai hikima.
64. Ya kai Annabi! Ma`ishinka Allah ne, kai da wanda ya biye maka daga mũminai.
65. Ya kai Annabi! Ka kwaɗaitar da mũminai a kan yãƙi. Idan mutum ashirin mãsu haƙuri sun kasance daga gare ku, zã su rinjãyi mẽtan kuma idan ɗari suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi dubu daga waɗanda suka kãfirta, dõmin sũ, mutãne ne bã su fahimta.
66. A yanzu Allah Yã sauƙaƙe daga gare ku, kuma Yã sani cẽwa lalle ne akwai mãsu rauni a cikinku. To, idan mutum ɗari, mãsu haƙuri, suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi mẽtan, kuma idan dubu suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi dubu biyu, da iznin Allah. Kuma Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri.
67. Bã ya kasancewa ga wani annabi, kãmammu su kasance a gare shi sai (bãyan) yã zubar da jinainai a cikin ƙasa. Kunã nufin sifar dũniya kuma Allah Yanãnufin Lãhira. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.
68. Bã dõmin wani Littãfi daga Allah ba, wanda ya gabãta, dã azãba mai girma daga Allah tã shãfe ku a cikin abin da kuka kãma.
69. Sabõda haka, ku ci daga abin da kuka sãmu ganĩma, Yanã halal mai kyau. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
70. Ya kai Annabi! Ka ce wa wanda yake a cikin hannãyenku daga kãmammu: "Idan Allah Ya san akwai wani alhẽri a cikin zukãtanku, zai kawo muku mafi alhẽri daga abin da aka karɓa daga gare ku, kuma Ya yi muku gãfara. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."
71. Kuma idan sun yi nufin yaudararka, to, haƙĩƙa, sun yaudari Allahdaga gabãni sai Ya bãyar da dãmã daga gare su: Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.
72. Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi da dũkiyõyinsuda rãyukansu, a cikin hanyar Allah, da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi taimako. Waɗancan, sãshensu waliyyai ne ga sãshe. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma ba su yi hijira ba, bã ku da wani abu daga waliccinsu, sai sun yi hijira. Kuma idan suka nẽme ku taimako a cikin addini, to taimako yã wajaba a kanku, fãce a kan mutãne waɗanda a tsakãninku da tsakãninsu akwai wani alkwari. Kuma Allah ne, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani.
73. Kuma waɗanda suka kãfirta sãshensu ne waliyyan sãshe, idan ba ku aikata shi ba, wata fitina zã ta kasance a cikin ƙasa, da fasãdi babba.
74. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka yi hijira, kuma suka yi Jihãdi, a cikin hanyar Allah, kuma da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi tamiako, waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya, sunãda gãfara da wani abinci na karimci.
75. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni daga bãya, kuma suka yi hijira kuma suka yi jihãdi tãre da ku, to, waɗannan daga gare ku suke. Kuma ma`abũta zumunta, sãshensu ne waliyyan sãshe a cikin Littãfin Allah. Lalle Allah ne ga dukkan kõme Masani.