• 1. Ina rantsuwa da mala`iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.
  • 2. Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.
  • 3. Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.
  • 4. Sa`an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre.
  • 5. Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.
  • 6. Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.
  • 7. Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.
  • 8. Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.
  • 9. Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.
  • 10. Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?
  • 11. "Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"
  • 12. Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"
  • 13. To, ita kam, tsãwa guda kawai ce.
  • 14. Sai kawai gã su a bãyan ƙasa.
  • 15. Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?
  • 16. A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?
  • 17. Ka tafi zuwa ga Fir`auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi.
  • 18. "Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka.
  • 19. "Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?"
  • 20. Sai ya nũna masa ãyar nan mafi girma.
  • 21. Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni),
  • 22. Sa`an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri.
  • 23. Sai ya yi gayya, sa`an nan ya yi kira.
  • 24. Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka."
  • 25. Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko.
  • 26. Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah.
  • 27. Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.
  • 28. Ya ɗaukaka rufinta, sa`an nan Ya daidaita ta.
  • 29. Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.
  • 30. Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta.
  • 31. Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta.
  • 32. Da duwatsu, Yã kafe ta.
  • 33. Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku.
  • 34. To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo.
  • 35. Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata.
  • 36. Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani.
  • 37. To, amma wanda ya yi girman kai.
  • 38. Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya).
  • 39. To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma.
  • 40. Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.
  • 41. To, lalle ne Aljanna ita ce makõma.
  • 42. Sunã tambayar ka game da sa`a, wai yaushe ne matabbatarta?
  • 43. Me ya haɗã ka da ambatonta?
  • 44. Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al`amarinta yake.
  • 45. Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta.
  • 46. Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa.
SHARE
logo
logo
logo
logo
logo
  • 1.Al-Fatihah
  • 2.Al Baqara
  • 3.Ali `Imran
  • 4.An-Nisa
  • 5.Al-Ma`idah
  • 6.Al-An`am
  • 7.Al-A`raf
  • 8.Al-Anfal
  • 9.At-Tawbah
  • 10.Yunus
  • 11.Hud
  • 12.Yusuf
  • 13.Ar-Ra`d
  • 14.Ibrahim
  • 15.Al-Hijr
  • 16.An-Nahl
  • 17.Al-Isra
  • 18.Al-Kahf
  • 19.Maryam
  • 20.Taha
  • 21.Al-Anbya
  • 22.Al-Haj
  • 23.Al-Mu`minun
  • 24.An-Nur
  • 25.Al-Furqan
  • 26.Ash-Shu`ara
  • 27.An-Naml
  • 28.Al-Qasas
  • 29.Al-`Ankabut
  • 30.Ar-Rum
  • 31.Luqman
  • 32.As-Sajdah
  • 33.Al-Ahzab
  • 34.Saba
  • 35.Faatir
  • 36.Ya-Sin
  • 37.As-Saffat
  • 38.Sad
  • 39.Az-Zumar
  • 40.Ghafir
  • 41.Fussilat
  • 42.sh-Shuraa
  • 43.Az-Zukhruf
  • 44.Ad-Dukhan
  • 45.Al-Jathiyah
  • 46.Al-Ahqaf
  • 47.Muhammad
  • 48.Al-Fath
  • 49.Al-Hujurat
  • 50.Qaf
  • 51.Adh-Dhariyat
  • 52.At-Tur
  • 53.An-Najm
  • 54.Al-Qamar
  • 55.Ar-Rahman
  • 56.Al-Waqi`ah
  • 57.Al-Hadid
  • 58.Al-Mujadila
  • 59.Al-Hashr
  • 60.Al-Mumtahanah
  • 61.As-Saf
  • 62.Al-Jumu`ah
  • 63.Al-Munafiqun
  • 64.At-Taghabun
  • 65.At-Talaq
  • 66.At-Tahrim
  • 67.Al-Mulk
  • 68.Al-Qalam
  • 69.Al-Haqqah
  • 70.Al-Ma`arij
  • 71.Nuh
  • 72.Al-Jinn
  • 73.Al-Muzzammil
  • 74.Al-Muddaththir
  • 75.Al-Qiyamah
  • 76.Al-Insan
  • 77.Al-Mursalat
  • 78.An-Naba
  • 79.An-Nazi`at
  • 80.Abasa
  • 81.At-Takwir
  • 82.Al-Infitar
  • 83.Al-Mutaffifin
  • 84.Al-Inshiqaq
  • 85.Al-Buruj
  • 86.At-Tariq
  • 87.Al-A`la
  • 88.Al-Ghashiyah
  • 89.Al-Fajr
  • 90.Al-Balad
  • 91.Ash-Shams
  • 92.Al-Layl
  • 93.Ad-Duhaa
  • 94.Ash-Sharh
  • 95.At-Tin
  • 96.Al-`Alaq
  • 97.Al-Qadr
  • 98.Al-Bayyinah
  • 99.Az-Zalzalah
  • 100.Al-`Adiyat
  • 101.Al-Qari`ah
  • 102.At-Takathur
  • 103.Al-`Asr
  • 104.Al-Humazah
  • 105.Al-Fil
  • 106.Quraysh
  • 107.Al-Ma`un
  • 108.Al-Kawthar
  • 109.Al-Kafirun
  • 110.An-Nasr
  • 111.Al-Masad
  • 112.Al-Ikhlas
  • 113.Al-Falaq
  • 114.An-Nas