• 1. Ka ce: "An yi wahayi zuwa gare ni cewa wasu jama`a na aljannu sun saurũri (karatuna), sai suka ce: Lalle ne mũ mun ji wani abin karantãwa (Alƙui`ãni), mai ban mãmãki."
  • 2. "Yana nũni zuwa ga hanyar ƙwarai, sabõda haka mun yi ĩmãni da shi bã zã mu kõma bautã wa Ubangijinmu tãre da kõwa ba."
  • 3. "Kuma lalle ne shĩ girman Ubangijinmu, Ya ɗaukaka, bai riƙi mãta ba, kuma bai riƙi ɗã ba."
  • 4. "Kuma lalle ne shi, wãwanmu ya kasance yana faɗar abin da ya ƙetare haddi ga Allah."
  • 5. "Kuma lalle ne mũ, mun yi zaton mutum da aljani bã zã su iya faɗar ƙarya ba ga Allah."
  • 6. "Kuma lalle ne shi wasu maza daga cikin mutãne, sun kasance sunã nẽman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, sabõda haka suka ƙara musu girman kai."
  • 7. "Kuma lalle ne sũ, sun yi zato, kamar yadda kuka yi zato, cewa Allah bã zai aiko kowa ba."
  • 8. "Kuma lalle ne mũ mun nẽmi (hawan) sama, sai muka, sãme ta an cika ta da tsaro mai tsanani da kuma yũlãye."
  • 9. "Kuma lalle ne mũ, mun kasance muna zama daga garẽta, a wurãren zama dõmin saurare. To wanda ya yi saurãre a yanzu, zai sãmi yũla, mai dãko dõminsa."
  • 10. "Kuma lalle ne mũ ba mu sani ba, shin, sharri ne aka yi nufi ga waɗanda ke cikin ƙasa, ko Ubangijinsu Yã yi nufin shiriya a gare su ne?"
  • 11. "Kuma lalle ne mũ, akwai sãlaihai a cikinmu, kuma akwai a cikinmu waɗanda ba haka bã mun kasance ƙungiyõyi dabam-dabam."
  • 12. "Kuma lalle ne mũ mun tabbatã bã zã mu buwãyi Allah ba, a cikin ƙasa, kuma bã zã mu buwãye Shi da gudu ba."
  • 13. "Kuma lalle ne mũ, a lõkacin da muka ji shiriya, mun yi ĩmãni da ita. To wanda ya yi ĩimãni da Uhangijinsa, bã zai ji tsõron nakkasa ba, kuma bã zai ji tsõron zãlunci ba."
  • 14. "Kuma lalle ne mũ akwai a cikinmu, waɗanda suka mĩƙa wuya, kuma akwai a cikinmu karkatattu. to, wanda ya mĩƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa."
  • 15. "Kuma amma karkatattu sai suka kasance makãmashi ga Jahannama."
  • 16. "Kuma dã sun tsayu sõsai a kan hanya, dã lalle Mun shãyar da su ruwa mai yawa."
  • 17. "Domin Mu jarraba su a ciki, kuma wanda ya kau da kai daga tuna Ubangijinsa, Ubangijinsa zai shigar da shi azãba mai hauhawa."
  • 18. "Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kõwa tãre da Allah (da su, a cikinsu)."
  • 19. "Kuma, lalle ne shi, a lõkacin da bãwan Allah ke kiran Sa sun yi kusa su zama kamar shirgi a kansa."
  • 20. Ka ce: "lna kiran Ubangijina ne kawai, kuma bã zan tãra kowa da Shi ba."
  • 21. Ka ce: "Lalle ne, nĩ bã ni mallakar wata cũta gare ku, kuma bã ni mallakar wani alhẽri."
  • 22. Ka ce: "Lalle ne, nĩ kõwa bã ya iya cẽtona daga Allah, kuma bã zan iya sãmun mafaka ba daga gare Shi."
  • 23. "Fãce iyarwa, daga Allah, da manzancinsa. To, wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, to, lalle yana da wutar Jahannama suna mãsu dawwama a cikinta, har abada."
  • 24. Har idan sun ga abin da ake yi musu gargaɗi da shi, to, zã su san wanda ya zama mafi raunin mataimaki da mafi ƙarancin adadi.
  • 25. Ka ce: "Ban sani ba a kusa ne abin da ake yi muku gargaɗi da shi, ko Ubangijina Ya sanya maSa dõgon ajali!"
  • 26. "Shi ɗai ne Masanin fake sabõda haka, bã Ya bayyana gaibinSa ga kowa."
  • 27. "Fãce ga wanda Yã yarda da shi, wato wani manzo sa`an nan lalle ne, zai sanya gãdi a gaba gare shi da bãya gare shi."
  • 28. "Dõmin Ya san lalle, sun iyar da sãƙonnin Ubangijinsu, kuma (Shi Ubangijin) Yã kẽwaye su da sani, kuma Yã lissafe dukan kõme da ƙididdiga."
SHARE
logo
logo
logo
logo
logo
  • 1.Al-Fatihah
  • 2.Al Baqara
  • 3.Ali `Imran
  • 4.An-Nisa
  • 5.Al-Ma`idah
  • 6.Al-An`am
  • 7.Al-A`raf
  • 8.Al-Anfal
  • 9.At-Tawbah
  • 10.Yunus
  • 11.Hud
  • 12.Yusuf
  • 13.Ar-Ra`d
  • 14.Ibrahim
  • 15.Al-Hijr
  • 16.An-Nahl
  • 17.Al-Isra
  • 18.Al-Kahf
  • 19.Maryam
  • 20.Taha
  • 21.Al-Anbya
  • 22.Al-Haj
  • 23.Al-Mu`minun
  • 24.An-Nur
  • 25.Al-Furqan
  • 26.Ash-Shu`ara
  • 27.An-Naml
  • 28.Al-Qasas
  • 29.Al-`Ankabut
  • 30.Ar-Rum
  • 31.Luqman
  • 32.As-Sajdah
  • 33.Al-Ahzab
  • 34.Saba
  • 35.Faatir
  • 36.Ya-Sin
  • 37.As-Saffat
  • 38.Sad
  • 39.Az-Zumar
  • 40.Ghafir
  • 41.Fussilat
  • 42.sh-Shuraa
  • 43.Az-Zukhruf
  • 44.Ad-Dukhan
  • 45.Al-Jathiyah
  • 46.Al-Ahqaf
  • 47.Muhammad
  • 48.Al-Fath
  • 49.Al-Hujurat
  • 50.Qaf
  • 51.Adh-Dhariyat
  • 52.At-Tur
  • 53.An-Najm
  • 54.Al-Qamar
  • 55.Ar-Rahman
  • 56.Al-Waqi`ah
  • 57.Al-Hadid
  • 58.Al-Mujadila
  • 59.Al-Hashr
  • 60.Al-Mumtahanah
  • 61.As-Saf
  • 62.Al-Jumu`ah
  • 63.Al-Munafiqun
  • 64.At-Taghabun
  • 65.At-Talaq
  • 66.At-Tahrim
  • 67.Al-Mulk
  • 68.Al-Qalam
  • 69.Al-Haqqah
  • 70.Al-Ma`arij
  • 71.Nuh
  • 72.Al-Jinn
  • 73.Al-Muzzammil
  • 74.Al-Muddaththir
  • 75.Al-Qiyamah
  • 76.Al-Insan
  • 77.Al-Mursalat
  • 78.An-Naba
  • 79.An-Nazi`at
  • 80.Abasa
  • 81.At-Takwir
  • 82.Al-Infitar
  • 83.Al-Mutaffifin
  • 84.Al-Inshiqaq
  • 85.Al-Buruj
  • 86.At-Tariq
  • 87.Al-A`la
  • 88.Al-Ghashiyah
  • 89.Al-Fajr
  • 90.Al-Balad
  • 91.Ash-Shams
  • 92.Al-Layl
  • 93.Ad-Duhaa
  • 94.Ash-Sharh
  • 95.At-Tin
  • 96.Al-`Alaq
  • 97.Al-Qadr
  • 98.Al-Bayyinah
  • 99.Az-Zalzalah
  • 100.Al-`Adiyat
  • 101.Al-Qari`ah
  • 102.At-Takathur
  • 103.Al-`Asr
  • 104.Al-Humazah
  • 105.Al-Fil
  • 106.Quraysh
  • 107.Al-Ma`un
  • 108.Al-Kawthar
  • 109.Al-Kafirun
  • 110.An-Nasr
  • 111.Al-Masad
  • 112.Al-Ikhlas
  • 113.Al-Falaq
  • 114.An-Nas