• 1. Kiran gaskiya!
  • 2. Mẽne ne kiran gaskiya?
  • 3. Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya?
  • 4. Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya!
  • 5. To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani.
  • 6. Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi.
  • 7. (Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi.
  • 8. To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu?
  • 9. Kuma Fir`auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi.
  • 10. Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani).
  • 11. Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan.
  • 12. Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi).
  • 13. To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya.
  • 14. Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya.
  • 15. A ran nan, mai aukuwa zã ta auku.
  • 16. Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce.
  • 17. Kuma malã`iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã`iku) takwas na ɗauke da Al`arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar.
  • 18. A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa.
  • 19. To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina."
  • 20. "Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne."
  • 21. Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda.
  • 22. A cikin Aljanna maɗaukakiya.
  • 23. Nunannun `yã`yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba),
  • 24. (Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni`ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige."
  • 25. Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba!"
  • 26. "Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!"
  • 27. "In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce!
  • 28. "Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!"
  • 29. "Ĩkona ya ɓace mini!"
  • 30. (Sai a ce wa malã`iku) "Ku kãmã shi, sa`an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi."
  • 31. "Sa`an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi."
  • 32. "Sa`an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã`i saba`in, sai ku sanya shi."
  • 33. "Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!"
  • 34. "Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!"
  • 35. "Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi."
  • 36. "Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn."
  • 37. "Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci."
  • 38. To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba,
  • 39. Da abin da bã ku iya gani.
  • 40. Lalle ne, shi (Alƙur`ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne.
  • 41. Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata.
  • 42. Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa.
  • 43. Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka.
  • 44. Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu.
  • 45. Dã Mun kãma shi da dãma.
  • 46. sa`an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã.
  • 47. Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbarMu) daga gare shi.
  • 48. Kuma lalle ne shi (Alƙur`ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa.
  • 49. Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa.
  • 50. Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai.
  • 51. Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙshẽni.
  • 52. Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma.
SHARE
logo
logo
logo
logo
logo
  • 1.Al-Fatihah
  • 2.Al Baqara
  • 3.Ali `Imran
  • 4.An-Nisa
  • 5.Al-Ma`idah
  • 6.Al-An`am
  • 7.Al-A`raf
  • 8.Al-Anfal
  • 9.At-Tawbah
  • 10.Yunus
  • 11.Hud
  • 12.Yusuf
  • 13.Ar-Ra`d
  • 14.Ibrahim
  • 15.Al-Hijr
  • 16.An-Nahl
  • 17.Al-Isra
  • 18.Al-Kahf
  • 19.Maryam
  • 20.Taha
  • 21.Al-Anbya
  • 22.Al-Haj
  • 23.Al-Mu`minun
  • 24.An-Nur
  • 25.Al-Furqan
  • 26.Ash-Shu`ara
  • 27.An-Naml
  • 28.Al-Qasas
  • 29.Al-`Ankabut
  • 30.Ar-Rum
  • 31.Luqman
  • 32.As-Sajdah
  • 33.Al-Ahzab
  • 34.Saba
  • 35.Faatir
  • 36.Ya-Sin
  • 37.As-Saffat
  • 38.Sad
  • 39.Az-Zumar
  • 40.Ghafir
  • 41.Fussilat
  • 42.sh-Shuraa
  • 43.Az-Zukhruf
  • 44.Ad-Dukhan
  • 45.Al-Jathiyah
  • 46.Al-Ahqaf
  • 47.Muhammad
  • 48.Al-Fath
  • 49.Al-Hujurat
  • 50.Qaf
  • 51.Adh-Dhariyat
  • 52.At-Tur
  • 53.An-Najm
  • 54.Al-Qamar
  • 55.Ar-Rahman
  • 56.Al-Waqi`ah
  • 57.Al-Hadid
  • 58.Al-Mujadila
  • 59.Al-Hashr
  • 60.Al-Mumtahanah
  • 61.As-Saf
  • 62.Al-Jumu`ah
  • 63.Al-Munafiqun
  • 64.At-Taghabun
  • 65.At-Talaq
  • 66.At-Tahrim
  • 67.Al-Mulk
  • 68.Al-Qalam
  • 69.Al-Haqqah
  • 70.Al-Ma`arij
  • 71.Nuh
  • 72.Al-Jinn
  • 73.Al-Muzzammil
  • 74.Al-Muddaththir
  • 75.Al-Qiyamah
  • 76.Al-Insan
  • 77.Al-Mursalat
  • 78.An-Naba
  • 79.An-Nazi`at
  • 80.Abasa
  • 81.At-Takwir
  • 82.Al-Infitar
  • 83.Al-Mutaffifin
  • 84.Al-Inshiqaq
  • 85.Al-Buruj
  • 86.At-Tariq
  • 87.Al-A`la
  • 88.Al-Ghashiyah
  • 89.Al-Fajr
  • 90.Al-Balad
  • 91.Ash-Shams
  • 92.Al-Layl
  • 93.Ad-Duhaa
  • 94.Ash-Sharh
  • 95.At-Tin
  • 96.Al-`Alaq
  • 97.Al-Qadr
  • 98.Al-Bayyinah
  • 99.Az-Zalzalah
  • 100.Al-`Adiyat
  • 101.Al-Qari`ah
  • 102.At-Takathur
  • 103.Al-`Asr
  • 104.Al-Humazah
  • 105.Al-Fil
  • 106.Quraysh
  • 107.Al-Ma`un
  • 108.Al-Kawthar
  • 109.Al-Kafirun
  • 110.An-Nasr
  • 111.Al-Masad
  • 112.Al-Ikhlas
  • 113.Al-Falaq
  • 114.An-Nas