• 1. Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa.
  • 2. Kai, sabõda ni`imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba.
  • 3. Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa.
  • 4. Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya.
  • 5. Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani.
  • 6. Ga wanenku haukã take.
  • 7. Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkinSa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.
  • 8. Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa.
  • 9. Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta.
  • 10. Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce.
  • 11. Mai zunɗe, mai yãwo da gulma.
  • 12. Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi.
  • 13. Mai girman kai, bãyan haka kuma la`ĩmi (bã ya son alhẽri).
  • 14. Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya.
  • 15. Idan ana karanta masa ãyõyinMu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne."
  • 16. Zã Mu yi masa alãma a kan hanci.
  • 17. Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci.
  • 18. Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa.
  • 19. Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, (ya ƙone ta,) alhãli sunã barci.
  • 20. Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare.
  • 21. Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci.
  • 22. Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa.
  • 23. Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa).
  • 24. "Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau!"
  • 25. Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu.
  • 26. Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)!"
  • 27. "Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne."
  • 28. Mafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah?"
  • 29. Suka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai."
  • 30. Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu.
  • 31. Suka ce: "Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka."
  • 32. "Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne."
  • 33. Haka dai azãbar take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã.
  • 34. Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni`ima.
  • 35. Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa`a kamar mãsu laifi?
  • 36. Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)?
  • 37. Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa?
  • 38. Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa?
  • 39. Kõ kunã (riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kanMu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku?
  • 40. Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)?
  • 41. Kõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra`ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya.
  • 42. Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujũda, sai bã zã su iyãwa ba.
  • 43. Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi).
  • 44. Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur`ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.
  • 45. Ina jinkirtã musu, lalle kaidiNa mai ƙarfi ne.
  • 46. Kõ kana tambayar su wata la`ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu?
  • 47. Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne?
  • 48. Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma`abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi.
  • 49. Ba dõmin ni`ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi.
  • 50. Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa`an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki.
  • 51. Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur`ãni, kuma sunã cẽwa, "Lalle ne shi mahaukaci ne!"
  • 52. Shi (Alƙur`ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya.
SHARE
logo
logo
logo
logo
logo
  • 1.Al-Fatihah
  • 2.Al Baqara
  • 3.Ali `Imran
  • 4.An-Nisa
  • 5.Al-Ma`idah
  • 6.Al-An`am
  • 7.Al-A`raf
  • 8.Al-Anfal
  • 9.At-Tawbah
  • 10.Yunus
  • 11.Hud
  • 12.Yusuf
  • 13.Ar-Ra`d
  • 14.Ibrahim
  • 15.Al-Hijr
  • 16.An-Nahl
  • 17.Al-Isra
  • 18.Al-Kahf
  • 19.Maryam
  • 20.Taha
  • 21.Al-Anbya
  • 22.Al-Haj
  • 23.Al-Mu`minun
  • 24.An-Nur
  • 25.Al-Furqan
  • 26.Ash-Shu`ara
  • 27.An-Naml
  • 28.Al-Qasas
  • 29.Al-`Ankabut
  • 30.Ar-Rum
  • 31.Luqman
  • 32.As-Sajdah
  • 33.Al-Ahzab
  • 34.Saba
  • 35.Faatir
  • 36.Ya-Sin
  • 37.As-Saffat
  • 38.Sad
  • 39.Az-Zumar
  • 40.Ghafir
  • 41.Fussilat
  • 42.sh-Shuraa
  • 43.Az-Zukhruf
  • 44.Ad-Dukhan
  • 45.Al-Jathiyah
  • 46.Al-Ahqaf
  • 47.Muhammad
  • 48.Al-Fath
  • 49.Al-Hujurat
  • 50.Qaf
  • 51.Adh-Dhariyat
  • 52.At-Tur
  • 53.An-Najm
  • 54.Al-Qamar
  • 55.Ar-Rahman
  • 56.Al-Waqi`ah
  • 57.Al-Hadid
  • 58.Al-Mujadila
  • 59.Al-Hashr
  • 60.Al-Mumtahanah
  • 61.As-Saf
  • 62.Al-Jumu`ah
  • 63.Al-Munafiqun
  • 64.At-Taghabun
  • 65.At-Talaq
  • 66.At-Tahrim
  • 67.Al-Mulk
  • 68.Al-Qalam
  • 69.Al-Haqqah
  • 70.Al-Ma`arij
  • 71.Nuh
  • 72.Al-Jinn
  • 73.Al-Muzzammil
  • 74.Al-Muddaththir
  • 75.Al-Qiyamah
  • 76.Al-Insan
  • 77.Al-Mursalat
  • 78.An-Naba
  • 79.An-Nazi`at
  • 80.Abasa
  • 81.At-Takwir
  • 82.Al-Infitar
  • 83.Al-Mutaffifin
  • 84.Al-Inshiqaq
  • 85.Al-Buruj
  • 86.At-Tariq
  • 87.Al-A`la
  • 88.Al-Ghashiyah
  • 89.Al-Fajr
  • 90.Al-Balad
  • 91.Ash-Shams
  • 92.Al-Layl
  • 93.Ad-Duhaa
  • 94.Ash-Sharh
  • 95.At-Tin
  • 96.Al-`Alaq
  • 97.Al-Qadr
  • 98.Al-Bayyinah
  • 99.Az-Zalzalah
  • 100.Al-`Adiyat
  • 101.Al-Qari`ah
  • 102.At-Takathur
  • 103.Al-`Asr
  • 104.Al-Humazah
  • 105.Al-Fil
  • 106.Quraysh
  • 107.Al-Ma`un
  • 108.Al-Kawthar
  • 109.Al-Kafirun
  • 110.An-Nasr
  • 111.Al-Masad
  • 112.Al-Ikhlas
  • 113.Al-Falaq
  • 114.An-Nas