• 1. Idan mai aukuwa ta auku.
  • 2. Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.
  • 3. (Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.
  • 4. Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.
  • 5. Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.
  • 6. Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.
  • 7. Kuma kun kasance nau`i uku.
  • 8. Watau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
  • 9. Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?
  • 10. Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,
  • 11. Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.
  • 12. A ckin Aljannar ni`ima.
  • 13. Jama`a ne daga mutãnen farko.
  • 14. Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.
  • 15. (Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu.
  • 16. Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.
  • 17. Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.
  • 18. Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.
  • 19. Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.
  • 20. Da wasu `ya`yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.
  • 21. Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha`awa.
  • 22. Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.
  • 23. Kamar misãlan lu`ulu`u wanda aka ɓõye.
  • 24. A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.
  • 25. Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.
  • 26. Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.
  • 27. Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
  • 28. (Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.
  • 29. Da wata ayaba mai yawan `ya`ya.
  • 30. Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya.
  • 31. Da wani ruwa mai gudãna.
  • 32. Da wasu `ya`yan itacen marmari mãsu yawa.
  • 33. Bã su yankẽwa kuma bã a hana su.
  • 34. Da wasu shimfiɗu maɗaukaka.
  • 35. Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.
  • 36. Sa`an nan Muka sanya su budurwai.
  • 37. Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.
  • 38. Ga mazõwa dãma.
  • 39. Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko.
  • 40. Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.
  • 41. Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?
  • 42. Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.
  • 43. Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.
  • 44. Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni`ima ba.
  • 45. Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.
  • 46. Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.
  • 47. Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?"
  • 48. "Shin, kuma da ubanninmu na farko?"
  • 49. Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe."
  • 50. "Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne."
  • 51. "Sa`an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!"
  • 52. "Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)."
  • 53. "Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta."
  • 54. "Sa`an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi."
  • 55. "Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa."
  • 56. Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.
  • 57. Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?
  • 58. Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?
  • 59. Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?
  • 60. Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa ba,
  • 61. A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.
  • 62. Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?
  • 63. Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?
  • 64. Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?
  • 65. Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.
  • 66. (Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!"
  • 67. "Ã`a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!"
  • 68. Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?
  • 69. Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?
  • 70. Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?
  • 71. Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?
  • 72. Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?
  • 73. Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa`azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.
  • 74. Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.
  • 75. To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.
  • 76. Kuma lalle ne` haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.
  • 77. Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.
  • 78. A cikin wani littafi tsararre.
  • 79. Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.
  • 80. Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.
  • 81. Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?
  • 82. Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?
  • 83. To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).
  • 84. Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.
  • 85. Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.
  • 86. To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?
  • 87. Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.
  • 88. To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,
  • 89. Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni`ima.
  • 90. Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,
  • 91. Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.
  • 92. Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,
  • 93. Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.
  • 94. Da ƙõnuwa da Jahĩm,
  • 95. Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.
  • 96. Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangijinka, Mai karimci.
SHARE
logo
logo
logo
logo
logo
  • 1.Al-Fatihah
  • 2.Al Baqara
  • 3.Ali `Imran
  • 4.An-Nisa
  • 5.Al-Ma`idah
  • 6.Al-An`am
  • 7.Al-A`raf
  • 8.Al-Anfal
  • 9.At-Tawbah
  • 10.Yunus
  • 11.Hud
  • 12.Yusuf
  • 13.Ar-Ra`d
  • 14.Ibrahim
  • 15.Al-Hijr
  • 16.An-Nahl
  • 17.Al-Isra
  • 18.Al-Kahf
  • 19.Maryam
  • 20.Taha
  • 21.Al-Anbya
  • 22.Al-Haj
  • 23.Al-Mu`minun
  • 24.An-Nur
  • 25.Al-Furqan
  • 26.Ash-Shu`ara
  • 27.An-Naml
  • 28.Al-Qasas
  • 29.Al-`Ankabut
  • 30.Ar-Rum
  • 31.Luqman
  • 32.As-Sajdah
  • 33.Al-Ahzab
  • 34.Saba
  • 35.Faatir
  • 36.Ya-Sin
  • 37.As-Saffat
  • 38.Sad
  • 39.Az-Zumar
  • 40.Ghafir
  • 41.Fussilat
  • 42.sh-Shuraa
  • 43.Az-Zukhruf
  • 44.Ad-Dukhan
  • 45.Al-Jathiyah
  • 46.Al-Ahqaf
  • 47.Muhammad
  • 48.Al-Fath
  • 49.Al-Hujurat
  • 50.Qaf
  • 51.Adh-Dhariyat
  • 52.At-Tur
  • 53.An-Najm
  • 54.Al-Qamar
  • 55.Ar-Rahman
  • 56.Al-Waqi`ah
  • 57.Al-Hadid
  • 58.Al-Mujadila
  • 59.Al-Hashr
  • 60.Al-Mumtahanah
  • 61.As-Saf
  • 62.Al-Jumu`ah
  • 63.Al-Munafiqun
  • 64.At-Taghabun
  • 65.At-Talaq
  • 66.At-Tahrim
  • 67.Al-Mulk
  • 68.Al-Qalam
  • 69.Al-Haqqah
  • 70.Al-Ma`arij
  • 71.Nuh
  • 72.Al-Jinn
  • 73.Al-Muzzammil
  • 74.Al-Muddaththir
  • 75.Al-Qiyamah
  • 76.Al-Insan
  • 77.Al-Mursalat
  • 78.An-Naba
  • 79.An-Nazi`at
  • 80.Abasa
  • 81.At-Takwir
  • 82.Al-Infitar
  • 83.Al-Mutaffifin
  • 84.Al-Inshiqaq
  • 85.Al-Buruj
  • 86.At-Tariq
  • 87.Al-A`la
  • 88.Al-Ghashiyah
  • 89.Al-Fajr
  • 90.Al-Balad
  • 91.Ash-Shams
  • 92.Al-Layl
  • 93.Ad-Duhaa
  • 94.Ash-Sharh
  • 95.At-Tin
  • 96.Al-`Alaq
  • 97.Al-Qadr
  • 98.Al-Bayyinah
  • 99.Az-Zalzalah
  • 100.Al-`Adiyat
  • 101.Al-Qari`ah
  • 102.At-Takathur
  • 103.Al-`Asr
  • 104.Al-Humazah
  • 105.Al-Fil
  • 106.Quraysh
  • 107.Al-Ma`un
  • 108.Al-Kawthar
  • 109.Al-Kafirun
  • 110.An-Nasr
  • 111.Al-Masad
  • 112.Al-Ikhlas
  • 113.Al-Falaq
  • 114.An-Nas