• 1. Ḥ. M̃.
  • 2. Saukar da littafi daga Allah, Mabuwãyi, Mai hikima yake.
  • 3. Ba Mu halitta sammai da ƙasa ba, da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da wani ajali ambatacce, kuma waɗanda suka kãfirta, mãsu bijirẽwa ne daga abin da aka yi musu gargaɗi (da shi).
  • 4. Ka ce: "Shin, kun gani, abin da kuke kira, wanda yake baicin Allah? Ku nũna mini, menene suka halitta daga ƙasa? Kõ kuwa sunã da tãrayya a cikin sammai? Ku zo mini da wani littãfi na gabãnin wannan (Alƙur`ãni) kõ wata alãma daga wani ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya."
  • 5. Kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ke kiran wanin Allah wanda da bã zai karɓa masa ba, bar Rãnar Kyama, alhãli sũ (waɗanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiransu?
  • 6. Kuma idan aka tãra mutãne sai su kasance maƙiya a gare su, alhãli sun kasance mãsu ƙi ga ibãdarsu.
  • 7. Kuma idan anã karãtun ãyõòyinMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta ga gaskiya a lõkacin da ta jẽ musu, su ce, "Wannan sihiri ne bayyananne."
  • 8. Kõkuwã sunã cẽwa: "Yã ƙirƙira shi (Alƙur`ãni) ne?" Ka ce: "Idan na ƙirƙira shi ne, to bã ku mallaka mini kõme daga Allah. Shĩ ne Mafi sani ga abin da kuke kũtsãwa a cikinsa na magana. (Allah) Yã isa Ya zama shaida a tsakãnĩnada tsakãninku. Kuma shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."
  • 9. Ka ce: "Ban kasance fãrau ba daga Manzanni, kuma ban san abin da zã a yi game da ni kõ game da ku (na gaibi) ba, bã ni bin kõme fãce abin da ake yin wahayi zuwa gare ni, kuma ban zama ba, fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa."
  • 10. Ka ce: "Shin, kun gani, idan (Alƙur`ãni) ya kasance daga wurin Allah yake, kuma kuka kãfirta da shi, kuma wani mai shaida daga Banĩ Isrã`ĩla ya bãyar da shaida a kan kwatankwacinsa, sa`an nan ya yi ĩmãni, kuma kuka kangare? Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai."
  • 11. Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni: "Da (Alƙur`ãni) ya kasance, wani alhẽri ne," dã ba su riga muzuwa gare shi ba. Kuma tun da ba su shiryu game da shĩ ba, to, zã su ce, "Wannan ƙiren ƙarya ne daɗaɗɗe."
  • 12. Alhãli kuwa a gabãninsa akwai littãfin Mũsã, wanda ya kasance abin kõyi, kuma rahama. Kuma wannan (Alƙur`ãni) littafi ne mai gaskatãwa (ga littafin Mũsã), a harshe na Larabci dõmin ya gargaɗi waɗanda suka yi zãlunci, kuma ya zama bushãra ga mãsu kyautatãwa.
  • 13. Lalle ne waɗanda suka ce: "Ubangijinmu Allah ne," sa`an nan suka daidaitu, to, bãbu wani tsõro a kansu, kuma bã zã su yi baƙin ciki ba.
  • 14. Waɗannan `yan Aljanna ne, sunã madawwama a cikinta, a kan sakamako ga abin da suka kasance sunã aikatãwa.
  • 15. Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu da kyautatãwa, uwarsa tã yi cikinsa wahala, kuma ta haife shi wahala. cikinsa da yãyensa watã talãtin. Har a lõkacin da ya kai ga mafi ƙarfinsa, kuma ya kai shẽkara arba`in, ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka kange nidõmin in gõde wa ni`imarKa, wadda Ka ni`imta a kaina da kuma a kan mahaifãna biyu, kuma dõmin in aikata aikin ƙwarai wanda Kake yarda da shi, kuma Ka kyautata mini a cikin zuriyata. Lalle nĩ, nã tũba zuwa gare Ka, kuma lalle ni, inã daga mãsu sallamãwa (ga umurninKa)."
  • 16. Waɗancan ne waɗanda Muke karɓa, daga gare su, mafi kyaun abin da suka aikata, kuma Muke gãfarta mafi mũnanan ayyukansum (sunã) a cikin `yan Aljanna, a kan wa`adin gaskiya wanda suka kasance anã yi musu alkawari (da shi).
  • 17. Kuma wanda ya ce wa mahaifansa biyu: "Tir gare ku! shin, kunã tsõratar da ni cẽwa zã a fitar da ni daga (kabari) ne, alhãli kuwa ƙarnõni na mutãne da yawa sun shũɗe a gabãnĩna (ba su kõmo ba)?" Kuma sũ (mahaifan) sunã nẽman Allah taimako (sunãce masa) "Kaitonka! Ka yi ĩmãni, lalle wa`adin Allah gaskiya ne." Sai shi kuma ya ce. "Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko."
  • 18. Waɗancan ne waɗanda kalmar azãba ta wajaba a kansu, a cikin al`ummõmi waɗanda suka shũɗe, (bã da daɗẽwa ba), a gabãninsu, daga aljannu da mutãne. Lalle sũ, sun kasance mãsu hasãra.
  • 19. Kuma ga kõwane nau`i, yanã da darajõji daga abinda suka aikata. Kuma dõmin (Allah) Ya cika musu (sakamakon) ayyukansu, alhãli kuwa sũ, bã zã a zãlunce su ba.
  • 20. Kuma rãnar da ake gitta waɗanda suka kãflrta a kan wutã (a ce musu): "Kun tafiyar da abũbuwanku na jin dãɗi a cikin rayuwarku ta dũniya, kuma kun nẽmi jin dãdi da su, to, ayau anã sãka muka da azãbar wulãkanci, dõmin abin da kuka kasance kanã yi na gmian kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, kuma dõmin abin da kuka kasance kuna yi na fãsiƙansi."
  • 21. Kuma ka ambaci ɗan`uwan Ãdãwa a lõkacin da ya yi gargaɗi ga mutãnensa, a Tuddan Rairayi, alhãli kuwa waɗansu mãsu gargaɗi sun shũɗe agaba gare shi da bãya gare shi (da cẽwa) "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah. Lalle nĩ inã tsõrata muku azãbar yini mai girma."
  • 22. Suka ce: "Shin, kã zo mana ne dõmin ka karkatar da mu daga gumãkaumu? To, ka zo mana da abin da kake yi mana wa`adin, idan kã kasance daga mãsu gaskiya."
  • 23. Ya ce: "Ilimi a wurin Allah kawai yake, kuma inã iyar maku abin da aka aiko ni da shi, kuma amma inã ganin, kũ, wasu mutãne ne, kunã jãhiltar gaskiya."
  • 24. To, a lõkacin da suka ga azãbar, kumar hadari mai fuskantar rãfukansu, suka ce: "Wannan hadari ne mai yi mana ruwa. Ã`a, shĩ na abin da kuke nẽman gaggawar saukarsa; Iska ce, a cikinta akwai wata azaba mai raɗaɗi.
  • 25. Tanã darkake kõwane abu da umurnin Ubangijinta. Sai suka wãyi gari, bã a ganin kõme fãce gidãjensu. Kamar wannan ne Muke sãka wa mutãne mãsu laifi.
  • 26. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun ba su ĩko ga abin da ba Mubã ku ĩko gare shi ba, kuma Muka sanya musu wani irin jĩ da gani dazukãta. Sai dai jnsu bai amfãne su ba, kuma zukãtansu ba su amfãne su ba ga kõme, dõmin sun kasance sunã musu game da ãyõyin Allah, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa na izgili game da shi ya wajaba a gare su.
  • 27. Kuma ne, lalle haƙĩƙa, Mun halakar da abin da yake kẽwayenku na alƙaryu kuma Muka jujjũya ãyõyi, tsammãninsu zã su kõmo.
  • 28. To, don mẽne ne waɗanda suka riƙa, baicin Allah, abũbuwan yi. wa baiko, gumaka, ba su taimake su ba? Ã`a, sun ɓace musu Kuma wannan shi ne ƙiren ƙaryarsu da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa.
  • 29. Kuma a lõkcin da Muka jũya waɗansu jama`a na aljamiu zuwa gare ka sunã saurãren Alƙur`ãni. To, alõkacin da suka halarce shi suka ce: "Ku yi shiru." Sa`an nan da aka ƙãre, suka jũya zuwa ga jama`arsu sunã mãsu gargaɗi.
  • 30. Suka ce: "Ya mutãnenmu! Lalle mũ, mun ji wani littãfi an saukar da shi a bãyãn Mũsã, mai gaskatãwa ga abin da ke a gaba da shi, yanã shiryarwa ga gaskiya da kuma zuwa ga hanya madaidaiciya.
  • 31. "Yã mutãnenmu! Ku karɓa wa mai kiran Allah, kuma ku yi ĩmãni da Shi, Ya gãfarta muku daga zunubanku, kuma ya tserar da ku daga azãba mai raɗaɗi.
  • 32. "Kuma wanda bai karɓa wa mai kiran Allah ba to bai zama mai buwãya a cikin ƙasa ba, kuma ba ya da waɗansu majiɓinta, baicin Shi. Waɗannnan sunã a cikin ɓata bayyananna."
  • 33. Shin, kuma ba su gani ba cẽwa: "Lalle Allah, Wanda Yã halitta sammai da ƙasa kuma bai kãsa ga halittarsu ba, Mai ĩkon yi ne a kan rãyar da matattu?" Na`am, lalle Shi, Mai ĩkon yi ne a kan kõme.
  • 34. Kuma rãnar da ake gittar da waɗanda suka kãfirta a kan wutã, (a ce musu) "Ashe, wannan bã gaskiya ba ne?" Su ce: "Na`am, gaskiya ne, mun rantse da Ubangijinmu!" Sai Ya ce, "To, ku ɗanɗani azãbar sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci."
  • 35. Sabõda haka, ka yi haƙuri kamar yadda mãsu ƙarfin niyya daga Manzanni suka yi haƙuri. Kuma kada ka yi musu gaggãwa. Kamar dai sũ, a rãnar da suke ganin (sakamako) abin da ake yi musu wa`adi ba su zauna ba, fãce sa`a guda daga yini. Iyarwa dai da Manzanci). Shin, akwai wanda za a halakar? (Bãbu), fãce mutãne fasiƙai.
SHARE
logo
logo
logo
logo
logo
  • 1.Al-Fatihah
  • 2.Al Baqara
  • 3.Ali `Imran
  • 4.An-Nisa
  • 5.Al-Ma`idah
  • 6.Al-An`am
  • 7.Al-A`raf
  • 8.Al-Anfal
  • 9.At-Tawbah
  • 10.Yunus
  • 11.Hud
  • 12.Yusuf
  • 13.Ar-Ra`d
  • 14.Ibrahim
  • 15.Al-Hijr
  • 16.An-Nahl
  • 17.Al-Isra
  • 18.Al-Kahf
  • 19.Maryam
  • 20.Taha
  • 21.Al-Anbya
  • 22.Al-Haj
  • 23.Al-Mu`minun
  • 24.An-Nur
  • 25.Al-Furqan
  • 26.Ash-Shu`ara
  • 27.An-Naml
  • 28.Al-Qasas
  • 29.Al-`Ankabut
  • 30.Ar-Rum
  • 31.Luqman
  • 32.As-Sajdah
  • 33.Al-Ahzab
  • 34.Saba
  • 35.Faatir
  • 36.Ya-Sin
  • 37.As-Saffat
  • 38.Sad
  • 39.Az-Zumar
  • 40.Ghafir
  • 41.Fussilat
  • 42.sh-Shuraa
  • 43.Az-Zukhruf
  • 44.Ad-Dukhan
  • 45.Al-Jathiyah
  • 46.Al-Ahqaf
  • 47.Muhammad
  • 48.Al-Fath
  • 49.Al-Hujurat
  • 50.Qaf
  • 51.Adh-Dhariyat
  • 52.At-Tur
  • 53.An-Najm
  • 54.Al-Qamar
  • 55.Ar-Rahman
  • 56.Al-Waqi`ah
  • 57.Al-Hadid
  • 58.Al-Mujadila
  • 59.Al-Hashr
  • 60.Al-Mumtahanah
  • 61.As-Saf
  • 62.Al-Jumu`ah
  • 63.Al-Munafiqun
  • 64.At-Taghabun
  • 65.At-Talaq
  • 66.At-Tahrim
  • 67.Al-Mulk
  • 68.Al-Qalam
  • 69.Al-Haqqah
  • 70.Al-Ma`arij
  • 71.Nuh
  • 72.Al-Jinn
  • 73.Al-Muzzammil
  • 74.Al-Muddaththir
  • 75.Al-Qiyamah
  • 76.Al-Insan
  • 77.Al-Mursalat
  • 78.An-Naba
  • 79.An-Nazi`at
  • 80.Abasa
  • 81.At-Takwir
  • 82.Al-Infitar
  • 83.Al-Mutaffifin
  • 84.Al-Inshiqaq
  • 85.Al-Buruj
  • 86.At-Tariq
  • 87.Al-A`la
  • 88.Al-Ghashiyah
  • 89.Al-Fajr
  • 90.Al-Balad
  • 91.Ash-Shams
  • 92.Al-Layl
  • 93.Ad-Duhaa
  • 94.Ash-Sharh
  • 95.At-Tin
  • 96.Al-`Alaq
  • 97.Al-Qadr
  • 98.Al-Bayyinah
  • 99.Az-Zalzalah
  • 100.Al-`Adiyat
  • 101.Al-Qari`ah
  • 102.At-Takathur
  • 103.Al-`Asr
  • 104.Al-Humazah
  • 105.Al-Fil
  • 106.Quraysh
  • 107.Al-Ma`un
  • 108.Al-Kawthar
  • 109.Al-Kafirun
  • 110.An-Nasr
  • 111.Al-Masad
  • 112.Al-Ikhlas
  • 113.Al-Falaq
  • 114.An-Nas