• 1. Ḥ. M̃.
  • 2. Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.
  • 3. Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ` Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.
  • 4. A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.
  • 5. Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã.
  • 6. Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.
  • 7. (Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka).
  • 8. Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.
  • 9. A`a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.
  • 10. Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.
  • 11. Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.
  • 12. Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.
  • 13. Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?
  • 14. Sa`an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci."
  • 15. Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin).
  • 16. Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.
  • 17. Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir`auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.
  • 18. (Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku."
  • 19. "Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne."
  • 20. "Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni."
  • 21. "Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni."
  • 22. Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.
  • 23. (Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)"
  • 24. "Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa."
  • 25. Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari.
  • 26. Da shuke-shuke da matsayi mai kyau.
  • 27. Da wata ni`ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.
  • 28. Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.
  • 29. Sa`an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.
  • 30. Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã`ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.
  • 31. Daga Fir`auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna.
  • 32. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne.
  • 33. Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu`ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni`ima bayyananna
  • 34. Lalle waɗannan mutãne, haƙĩka, sunã cẽwa,
  • 35. "Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."
  • 36. "Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."
  • 37. shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba`u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi.
  • 38. Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã.
  • 39. Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.
  • 40. Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa`adinsu gabã ɗaya.
  • 41. Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba.
  • 42. fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
  • 43. Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã),
  • 44. Ita ce abincin mai laifi.
  • 45. Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna.
  • 46. Kamar tafasar ruwan zãfi.
  • 47. (A cẽ wa malã`ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa`an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm."
  • 48. "Sa`an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi."
  • 49. (A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!"
  • 50. "Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi."
  • 51. Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce.
  • 52. A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari.
  • 53. Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna.
  • 54. Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu.
  • 55. Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan `ya`yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro).
  • 56. Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm.
  • 57. Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.
  • 58. Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur`ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa.
  • 59. Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne.
SHARE
logo
logo
logo
logo
logo
  • 1.Al-Fatihah
  • 2.Al Baqara
  • 3.Ali `Imran
  • 4.An-Nisa
  • 5.Al-Ma`idah
  • 6.Al-An`am
  • 7.Al-A`raf
  • 8.Al-Anfal
  • 9.At-Tawbah
  • 10.Yunus
  • 11.Hud
  • 12.Yusuf
  • 13.Ar-Ra`d
  • 14.Ibrahim
  • 15.Al-Hijr
  • 16.An-Nahl
  • 17.Al-Isra
  • 18.Al-Kahf
  • 19.Maryam
  • 20.Taha
  • 21.Al-Anbya
  • 22.Al-Haj
  • 23.Al-Mu`minun
  • 24.An-Nur
  • 25.Al-Furqan
  • 26.Ash-Shu`ara
  • 27.An-Naml
  • 28.Al-Qasas
  • 29.Al-`Ankabut
  • 30.Ar-Rum
  • 31.Luqman
  • 32.As-Sajdah
  • 33.Al-Ahzab
  • 34.Saba
  • 35.Faatir
  • 36.Ya-Sin
  • 37.As-Saffat
  • 38.Sad
  • 39.Az-Zumar
  • 40.Ghafir
  • 41.Fussilat
  • 42.sh-Shuraa
  • 43.Az-Zukhruf
  • 44.Ad-Dukhan
  • 45.Al-Jathiyah
  • 46.Al-Ahqaf
  • 47.Muhammad
  • 48.Al-Fath
  • 49.Al-Hujurat
  • 50.Qaf
  • 51.Adh-Dhariyat
  • 52.At-Tur
  • 53.An-Najm
  • 54.Al-Qamar
  • 55.Ar-Rahman
  • 56.Al-Waqi`ah
  • 57.Al-Hadid
  • 58.Al-Mujadila
  • 59.Al-Hashr
  • 60.Al-Mumtahanah
  • 61.As-Saf
  • 62.Al-Jumu`ah
  • 63.Al-Munafiqun
  • 64.At-Taghabun
  • 65.At-Talaq
  • 66.At-Tahrim
  • 67.Al-Mulk
  • 68.Al-Qalam
  • 69.Al-Haqqah
  • 70.Al-Ma`arij
  • 71.Nuh
  • 72.Al-Jinn
  • 73.Al-Muzzammil
  • 74.Al-Muddaththir
  • 75.Al-Qiyamah
  • 76.Al-Insan
  • 77.Al-Mursalat
  • 78.An-Naba
  • 79.An-Nazi`at
  • 80.Abasa
  • 81.At-Takwir
  • 82.Al-Infitar
  • 83.Al-Mutaffifin
  • 84.Al-Inshiqaq
  • 85.Al-Buruj
  • 86.At-Tariq
  • 87.Al-A`la
  • 88.Al-Ghashiyah
  • 89.Al-Fajr
  • 90.Al-Balad
  • 91.Ash-Shams
  • 92.Al-Layl
  • 93.Ad-Duhaa
  • 94.Ash-Sharh
  • 95.At-Tin
  • 96.Al-`Alaq
  • 97.Al-Qadr
  • 98.Al-Bayyinah
  • 99.Az-Zalzalah
  • 100.Al-`Adiyat
  • 101.Al-Qari`ah
  • 102.At-Takathur
  • 103.Al-`Asr
  • 104.Al-Humazah
  • 105.Al-Fil
  • 106.Quraysh
  • 107.Al-Ma`un
  • 108.Al-Kawthar
  • 109.Al-Kafirun
  • 110.An-Nasr
  • 111.Al-Masad
  • 112.Al-Ikhlas
  • 113.Al-Falaq
  • 114.An-Nas