• 1. Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).
  • 2. Sa`an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi.
  • 3. Sa`an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.
  • 4. Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne.
  • 5. Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.
  • 6. Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.
  • 7. Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.
  • 8. Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama`a mafi ɗaukaka (Malã`iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe.
  • 9. Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.
  • 10. Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.
  • 11. Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.
  • 12. Ã`a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.
  • 13. Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.
  • 14. Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.
  • 15. Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne."
  • 16. "Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?
  • 17. "Ashe kõ da ubanninmu na farko?"
  • 18. Ka ce: "Na`am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu."
  • 19. Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.
  • 20. Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako."
  • 21. Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.
  • 22. Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.
  • 23. Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.
  • 24. Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.
  • 25. Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?
  • 26. Ã`a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.
  • 27. Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.
  • 28. Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)."
  • 29. Suka ce: "Ã`a, ba ku kasance mũminai ba.
  • 30. "Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã`a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka."
  • 31. "Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne."
  • 32. "Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu."
  • 33. To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.
  • 34. Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.
  • 35. Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai.
  • 36. Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?
  • 37. Ã`a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.
  • 38. Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.
  • 39. Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
  • 40. Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
  • 41. Waɗannan sunã da abinci sananne.
  • 42. `Ya`yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.
  • 43. A cikin gidãjen Aljannar ni`ima.
  • 44. A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.
  • 45. Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari.
  • 46. Farã mai dãɗi ga mashãyan.
  • 47. A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,
  • 48. Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.
  • 49. Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.
  • 50. Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.
  • 51. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)."
  • 52. Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?"
  • 53. "Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?"
  • 54. (Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?"
  • 55. Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim.
  • 56. Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni."
  • 57. "Kuma bã dõmin ni`imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)."
  • 58. "Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba."
  • 59. "Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?"
  • 60. Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma.
  • 61. Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa.
  • 62. Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm?
  • 63. Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai.
  • 64. Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm.
  • 65. Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne.
  • 66. To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa`an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta.
  • 67. Sa`an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi.
  • 68. Sa`an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take.
  • 69. Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu.
  • 70. Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa.
  • 71. Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu.
  • 72. Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu.
  • 73. Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.
  • 74. Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
  • 75. Kuma lalle, haƙĩƙa` Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu.
  • 76. Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba.
  • 77. Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa.
  • 78. Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama`ar ƙarshe.
  • 79. Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu.
  • 80. Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
  • 81. Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai.
  • 82. Sã`an nan Muka nutsar da waɗansunsu.
  • 83. Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.
  • 84. A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya.
  • 85. A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?"
  • 86. "Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?"
  • 87. "To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?"
  • 88. Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri.
  • 89. Sã`an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne."
  • 90. Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.
  • 91. Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa`an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba?
  • 92. "Me ya sãme ku, bã ku magana?"
  • 93. Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma.
  • 94. Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.
  • 95. Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,
  • 96. "Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"
  • 97. Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa`an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm."
  • 98. Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.
  • 99. Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni."
  • 100. "Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne."
  • 101. Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri.
  • 102. To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri."
  • 103. To, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa.
  • 104. Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!"
  • 105. "Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
  • 106. Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.
  • 107. Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.
  • 108. Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.
  • 109. Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.
  • 110. Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
  • 111. Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.
  • 112. Kuma Muka yi masa bushãra Da Is`hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.
  • 113. Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is`hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin).
  • 114. Kuma lalle, Mun yi ni`ima ga Mũsã da Hãrũna.
  • 115. Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma.
  • 116. Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya.
  • 117. Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni.
  • 118. Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya.
  • 119. Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe.
  • 120. Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna.
  • 121. Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
  • 122. Lalle, sunã daga bãyinMu mũminai.
  • 123. Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
  • 124. A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?"
  • 125. "Shin, kunã bauta wa Ba`al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?"
  • 126. "Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?"
  • 127. Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã).
  • 128. Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
  • 129. Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.
  • 130. Aminci ya tabbata ga Ilyãs.
  • 131. Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
  • 132. Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.
  • 133. Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
  • 134. A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.
  • 135. Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba).
  • 136. Sã`an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen.
  • 137. Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.
  • 138. Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?
  • 139. Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
  • 140. A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.
  • 141. Sã`an nan ya yi ƙuri`a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.
  • 142. Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
  • 143. To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,
  • 144. Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.
  • 145. Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.
  • 146. Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.
  • 147. Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).
  • 148. Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.
  • 149. Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da `ya`ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?"
  • 150. Kõ kuma Mun halitta malã`iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?
  • 151. To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa.
  • 152. "Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.
  • 153. Shin, Yã zãɓi `yã`ya mãtã ne a kan ɗiya maza?
  • 154. Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci)?
  • 155. Shin, bã ku tunãni?
  • 156. Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?
  • 157. To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya.
  • 158. Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)"
  • 159. Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.
  • 160. Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
  • 161. To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,
  • 162. Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi.
  • 163. Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm.
  • 164. "Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, fãce yanã da matsayi sananne."
  • 165. "Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)."
  • 166. "Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi."
  • 167. Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa,
  • 168. "Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko."
  • 169. "Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."
  • 170. Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani.
  • 171. Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni.
  • 172. Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.
  • 173. Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya.
  • 174. Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci.
  • 175. Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.
  • 176. Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa?
  • 177. To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.
  • 178. Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci.
  • 179. Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa.
  • 180. Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.
  • 181. Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni.
  • 182. Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.
SHARE
logo
logo
logo
logo
logo
  • 1.Al-Fatihah
  • 2.Al Baqara
  • 3.Ali `Imran
  • 4.An-Nisa
  • 5.Al-Ma`idah
  • 6.Al-An`am
  • 7.Al-A`raf
  • 8.Al-Anfal
  • 9.At-Tawbah
  • 10.Yunus
  • 11.Hud
  • 12.Yusuf
  • 13.Ar-Ra`d
  • 14.Ibrahim
  • 15.Al-Hijr
  • 16.An-Nahl
  • 17.Al-Isra
  • 18.Al-Kahf
  • 19.Maryam
  • 20.Taha
  • 21.Al-Anbya
  • 22.Al-Haj
  • 23.Al-Mu`minun
  • 24.An-Nur
  • 25.Al-Furqan
  • 26.Ash-Shu`ara
  • 27.An-Naml
  • 28.Al-Qasas
  • 29.Al-`Ankabut
  • 30.Ar-Rum
  • 31.Luqman
  • 32.As-Sajdah
  • 33.Al-Ahzab
  • 34.Saba
  • 35.Faatir
  • 36.Ya-Sin
  • 37.As-Saffat
  • 38.Sad
  • 39.Az-Zumar
  • 40.Ghafir
  • 41.Fussilat
  • 42.sh-Shuraa
  • 43.Az-Zukhruf
  • 44.Ad-Dukhan
  • 45.Al-Jathiyah
  • 46.Al-Ahqaf
  • 47.Muhammad
  • 48.Al-Fath
  • 49.Al-Hujurat
  • 50.Qaf
  • 51.Adh-Dhariyat
  • 52.At-Tur
  • 53.An-Najm
  • 54.Al-Qamar
  • 55.Ar-Rahman
  • 56.Al-Waqi`ah
  • 57.Al-Hadid
  • 58.Al-Mujadila
  • 59.Al-Hashr
  • 60.Al-Mumtahanah
  • 61.As-Saf
  • 62.Al-Jumu`ah
  • 63.Al-Munafiqun
  • 64.At-Taghabun
  • 65.At-Talaq
  • 66.At-Tahrim
  • 67.Al-Mulk
  • 68.Al-Qalam
  • 69.Al-Haqqah
  • 70.Al-Ma`arij
  • 71.Nuh
  • 72.Al-Jinn
  • 73.Al-Muzzammil
  • 74.Al-Muddaththir
  • 75.Al-Qiyamah
  • 76.Al-Insan
  • 77.Al-Mursalat
  • 78.An-Naba
  • 79.An-Nazi`at
  • 80.Abasa
  • 81.At-Takwir
  • 82.Al-Infitar
  • 83.Al-Mutaffifin
  • 84.Al-Inshiqaq
  • 85.Al-Buruj
  • 86.At-Tariq
  • 87.Al-A`la
  • 88.Al-Ghashiyah
  • 89.Al-Fajr
  • 90.Al-Balad
  • 91.Ash-Shams
  • 92.Al-Layl
  • 93.Ad-Duhaa
  • 94.Ash-Sharh
  • 95.At-Tin
  • 96.Al-`Alaq
  • 97.Al-Qadr
  • 98.Al-Bayyinah
  • 99.Az-Zalzalah
  • 100.Al-`Adiyat
  • 101.Al-Qari`ah
  • 102.At-Takathur
  • 103.Al-`Asr
  • 104.Al-Humazah
  • 105.Al-Fil
  • 106.Quraysh
  • 107.Al-Ma`un
  • 108.Al-Kawthar
  • 109.Al-Kafirun
  • 110.An-Nasr
  • 111.Al-Masad
  • 112.Al-Ikhlas
  • 113.Al-Falaq
  • 114.An-Nas