• 1. A. L̃.R. Waɗancan ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa.
  • 2. Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi.
  • 3. Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa`an nan da sannu zã su sani.
  • 4. Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne.
  • 5. Wata al`umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.
  • 6. Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur`ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne."
  • 7. "Dõmin me bã zã ka zo mana da malã`ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?"
  • 8. Bã Mu sassaukar da malã`iku fãce da gaskiya, bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba.
  • 9. Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur`ãni), kuma lal1e Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi.
  • 10. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãninka.
  • 11. Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi.
  • 12. Kamar wancan ne Muke shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi.
  • 13. Bã su yin ĩmãni da shi, kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige.
  • 14. Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa.
  • 15. Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã`a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce."
  • 16. Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo.
  • 17. Kuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa.
  • 18. Fãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi.
  • 19. Kuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli.
  • 20. Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba.
  • 21. Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne.
  • 22. Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa`an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa`an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba.
  • 23. Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada.
  • 24. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri.
  • 25. Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani.
  • 26. Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja.
  • 27. Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar iskar zafi.
  • 28. Kuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã`iku: "Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja."
  • 29. "To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada."
  • 30. Sai malã`iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya.
  • 31. Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar.
  • 32. Ya ce: "Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?"
  • 33. Ya ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja."
  • 34. Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne."
  • 35. "Kuma lalle ne akwai la`ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako."
  • 36. Ya ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su."
  • 37. Ya ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri."
  • 38. "Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sananne."
  • 39. Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya."
  • 40. "Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake."
  • 41. Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici."
  • 42. "Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu."
  • 43. Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma`a1kawartarsu gabã ɗaya.
  • 44. Tanã da ƙõfõfi bakwai, ga kõwace ƙõfa akwai wani juz`i daga gare su rababbe.
  • 45. Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa.
  • 46. "Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu."
  • 47. Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama `yan`uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã.
  • 48. Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikinta ba.
  • 49. Ka bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai.
  • 50. Kuma azãbãTa ita ce azãba mai raɗaɗi.
  • 51. Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm.
  • 52. A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne."
  • 53. Suka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani."
  • 54. Ya ce: "Shin kun bã ni bushãra ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?"
  • 55. Suka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni."
  • 56. Ya ce: "Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijinsa, fãce ɓatattu?"
  • 57. Ya ce: "To, mẽne ne babban al`amarinku? Yã kũ manzanni!"
  • 58. Suka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi."
  • 59. "Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya."
  • 60. "Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka."
  • 61. To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu,
  • 62. Ya ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba."
  • 63. Suka ce: "Ã`a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa."
  • 64. "Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne."
  • 65. "Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku."
  • 66. Kuma Muka hukunta wancan al`amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga asuba.
  • 67. Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra.
  • 68. Ya ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni."
  • 69. "Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki."
  • 70. Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?"
  • 71. Ya ce: "Ga waɗannan, `ya`yãna idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."
  • 72. Rantsuwa da rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa.
  • 73. Sa`an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã.
  • 74. Sa`an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu.
  • 75. Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali.
  • 76. Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya.
  • 77. Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni.
  • 78. Kuma lalle ne ma`abũta Al`aika sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci!
  • 79. Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani.
  • 80. Kuma lalle ne haƙĩƙa ma`abũta Hijiri sun ƙaryata Manzanni.
  • 81. Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su.
  • 82. Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu.
  • 83. Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga asuba.
  • 84. Sa`an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba.
  • 85. Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã`a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau.
  • 86. Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani.
  • 87. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu da Alƙur`ãni mai girma.
  • 88. Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau`i-nau`i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni.
  • 89. Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyananne."
  • 90. Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa,
  • 91. Waɗanda suka sanya Alƙur`ãni tãtsuniyõyi.
  • 92. To, rantsuwa da Ubangijinka! Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.
  • 93. Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa.
  • 94. Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki.
  • 95. Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu izgili.
  • 96. Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa`an nan da sannu zã su sani.
  • 97. Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili).
  • 98. Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada.
  • 99. Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.
SHARE
logo
logo
logo
logo
logo
  • 1.Al-Fatihah
  • 2.Al Baqara
  • 3.Ali `Imran
  • 4.An-Nisa
  • 5.Al-Ma`idah
  • 6.Al-An`am
  • 7.Al-A`raf
  • 8.Al-Anfal
  • 9.At-Tawbah
  • 10.Yunus
  • 11.Hud
  • 12.Yusuf
  • 13.Ar-Ra`d
  • 14.Ibrahim
  • 15.Al-Hijr
  • 16.An-Nahl
  • 17.Al-Isra
  • 18.Al-Kahf
  • 19.Maryam
  • 20.Taha
  • 21.Al-Anbya
  • 22.Al-Haj
  • 23.Al-Mu`minun
  • 24.An-Nur
  • 25.Al-Furqan
  • 26.Ash-Shu`ara
  • 27.An-Naml
  • 28.Al-Qasas
  • 29.Al-`Ankabut
  • 30.Ar-Rum
  • 31.Luqman
  • 32.As-Sajdah
  • 33.Al-Ahzab
  • 34.Saba
  • 35.Faatir
  • 36.Ya-Sin
  • 37.As-Saffat
  • 38.Sad
  • 39.Az-Zumar
  • 40.Ghafir
  • 41.Fussilat
  • 42.sh-Shuraa
  • 43.Az-Zukhruf
  • 44.Ad-Dukhan
  • 45.Al-Jathiyah
  • 46.Al-Ahqaf
  • 47.Muhammad
  • 48.Al-Fath
  • 49.Al-Hujurat
  • 50.Qaf
  • 51.Adh-Dhariyat
  • 52.At-Tur
  • 53.An-Najm
  • 54.Al-Qamar
  • 55.Ar-Rahman
  • 56.Al-Waqi`ah
  • 57.Al-Hadid
  • 58.Al-Mujadila
  • 59.Al-Hashr
  • 60.Al-Mumtahanah
  • 61.As-Saf
  • 62.Al-Jumu`ah
  • 63.Al-Munafiqun
  • 64.At-Taghabun
  • 65.At-Talaq
  • 66.At-Tahrim
  • 67.Al-Mulk
  • 68.Al-Qalam
  • 69.Al-Haqqah
  • 70.Al-Ma`arij
  • 71.Nuh
  • 72.Al-Jinn
  • 73.Al-Muzzammil
  • 74.Al-Muddaththir
  • 75.Al-Qiyamah
  • 76.Al-Insan
  • 77.Al-Mursalat
  • 78.An-Naba
  • 79.An-Nazi`at
  • 80.Abasa
  • 81.At-Takwir
  • 82.Al-Infitar
  • 83.Al-Mutaffifin
  • 84.Al-Inshiqaq
  • 85.Al-Buruj
  • 86.At-Tariq
  • 87.Al-A`la
  • 88.Al-Ghashiyah
  • 89.Al-Fajr
  • 90.Al-Balad
  • 91.Ash-Shams
  • 92.Al-Layl
  • 93.Ad-Duhaa
  • 94.Ash-Sharh
  • 95.At-Tin
  • 96.Al-`Alaq
  • 97.Al-Qadr
  • 98.Al-Bayyinah
  • 99.Az-Zalzalah
  • 100.Al-`Adiyat
  • 101.Al-Qari`ah
  • 102.At-Takathur
  • 103.Al-`Asr
  • 104.Al-Humazah
  • 105.Al-Fil
  • 106.Quraysh
  • 107.Al-Ma`un
  • 108.Al-Kawthar
  • 109.Al-Kafirun
  • 110.An-Nasr
  • 111.Al-Masad
  • 112.Al-Ikhlas
  • 113.Al-Falaq
  • 114.An-Nas