1. Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci."
2. "Allah wanda ake nufin Sa da buƙata."
3. "Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba."
4. "Kuma babu ɗaya da ya kasance tamka a gare Shi."