1. Ka ce: "Ya kũ kãfirai!"
2. "Bã zan bautã wa abin da kuke bautã wa ba."
3. "Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba."
4. "Kuma nĩ ban zama mai bautã wa abin da kuka bautã wa ba."
5. "Kuma kũ, ba ku zama mãsu bautã wa abin da nake bautã wa ba."
6. "Addininku na garẽ ku, kuma addinina yanã gare ni."