1. Sabõda sãbon ¡uraishawa.
2. Sãbonsu na tafiyar hunturu da ta bazara.
3. Sabõda haka sai su bauta wa Ubangijin wannan Gida (Ka`abah).
4. wanda Ya ciyar da su (Ya hana su) daga yunwa, kuma Ya amintar da su daga wani tsõro.