1. Ashe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa ba?
2. Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba?
3. Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama`a-jama`a.
4. Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.
5. Sa`an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?