1. Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku).
2. Har kuka ziyarci kaburbura.
3. A`aha! (Nan gaba) zã ku sani.
4. Sa`an nan, tabbas, zã ku sani.
5. Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.
6. Lalle ne da kuna ganin Jahĩm.
7. Sa`an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.
8. Sa`an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni`imar (da aka yi muku).