1. Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!
2. Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?
3. Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?
4. Rãnar da mutãne za su kasance kamar `ya`yan fari mãsu wãtsuwa.
5. Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.
6. To, amma wanda ma`aunansa suka yi nauyi.
7. To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.
8. Kuma amma wanda ma`aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi).
9. To, uwarsa Hãwiya ce.
10. Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?
11. Wata wuta ce mai zafi.