1. Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
2. Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;
3. Mai rahama, Mai jin ƙai;
4. Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.
5. Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.
6. Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.
7. Hanyar waɗanda Ka yi wa ni`ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.