Mutane da yawa sun dauka cewar Charles Darwin ne ya fara kirkiro ka`idar juyin halitta(theory of evolution) wanda ya rataya akan hujjoji, lura da gwaje-gwajen kimiyya. Saboda haka, ta wannan fuska, Darwin ba shine ya kirkiro ba, ballantana ma ka`idar ba`a kafa ta akan hujjojin kimiyya ba. Ka`idar ta kunshi daukar yanayi (nature) daga imanin mutanen Da akan falsafar jari-hujja. Duk da cewar dai babu wata hujja ta kimiyya, sabo- da haka, sun marawa ka`idar baya ne a karkashin sunan falsafar jari-hujja. Wannan tsantseni ya haifar da annoba iri-iri. Saboda haduwar da yada akidar Darwin da Falsafar jari-hujja suka bunkasa, da amsar tambayar 'Menene dan Adam?'ya canza. Mutanen da suka saba fadin:Allah ne ya halicci `yan Adam, kuma su rayu akan kyawawan dabi`un da ya (Ubangiji) koyar sun fara canza tunaninsu zuwa'Mutum ya samu ne haka nan, kuma dabba ne wanda ya ginu da fafutukar rayuwa. 'Lalle zasu biya farashi mai nauyi akan wannan gagarumar yaudara. Akidu masu kawo rigingimu, irin su wariyar launin fata, mulkin kama-karya, kwaminisanci dadai sauran akidoji munana wadanda sun alakantu da wannan yaudara. Wannan gaba ta tattaunawa zata yi nazari akan annobar da Darwinism ko akidar Darwin ta jawowa duniya da alakar ta da ta`addanci, daya daga cikin muhimman matsalolin da suka addabi duniya a zamaninmu.