Wani muhimmin al’amari kuma da ya kasan a cikin tattaunawa tare da hare haren ta’addanci akan kasar Amurka shine dangantaka tsakanin kasashen yamma da duniyar musulunci. Kamar yadda aka sani, a shekarun casa’inoni (90s), an sami wasu masana bayar da bayanan karya cewa wai za a sami fafatawa tsakanin kasashen yamma da duniyar musulunci a wasu shekaru masu zuwa. Wannan shine ginshiken sanannen rubutun Samuel Huntington “The Clash of Civilizations.” Sai dai kuma shi wannan rubutu – wanda Edward W. Said ya kira shi da “Clash of Ignorance – ya ginu ne akan kirkirarren yanayin da aka samar da shi daga tasirin wasu bangarorin jahilai masu tsattsauran ra’ayi da suke cikin duk al’ummun biyu. A hakikanin gaskiya, babu wata fafatawa da za a yi tsakanin tsarin rayuwar yammaci da kuma tsarin musulunci, saboda tsarin addinan Kiristanci da Yahudanci, wadanda akan su ne tsarin rayuwar yamma ya ginu, ba su da matsala da musulunci.
A cikin Alkur’ani, an kira Yahudawa da Kiristoci da sunan “Ahlul Kitabi.” Dalilin wannan kuwa shine saboda mabiya wadannan addinai biyu suna aiki ne da Saukakkun Littattafai daga Allah Mahalicci. Matsayin Musulunci akan Ahlul Kitabi shine na tsantsar adalci da jin kai.
Wannan halayya kulawa ga Ahlul Kitabi ta samo asali ne tun lokacin kafuwar musulunci a bisa tsarin Alkur’ani. A wancan lokaci, musulmai sun kasance ‘yan tsiraru, suna kokarin tsare addininsu sannan suna fama da zalunci da azabtarwa daga maguzawan Makka. Saboda wannan matsantawa, sai wasu daga cikin Musulman suka yanke shawarar tserewa daga Makka don su nemi mafaka a kasa mai aminci karkashin adalin shugaba. Manzon Allah Muhammad (SAW) ya umarce su da su nemi mafaka a wajen sarkin kasar Habasha wanda kirista ne. Musulmin da suka tafi Habasha sun sami gwamnati mai adalci wadda ta karbe su tare da girmamawa da kauna. Sarki kuma ya ki amincewa da bukatar ‘yan aiken maguzawan Makka wadanda suka je Habasha suna neman ya damka musulmin a hannunsu don su dawo su Makka, inda ya sanar da cewa musulmin suna da ‘yancin zama a kasarsa.
An nuna wannan halayyar kiristoci ta tausayi, jin kai, da kuma adalci a ayar Alkur’ani:
… Kuma lalle za ka sami mafiya kusanta a soyayya ga wadanda suka yi imani su ne wadanda suka ce: "Mu ne Nasara." Wannan kuwa saboda akwai kissisuna da ruhubanawa daga cikinsu. Kuma lalle su ba sa yin girman kai. (Alkur'ani, sura ta 5, aya ta 82)
A cikin Alkur'ani, an kira Kiristoci da Yahudawa da Ahlul Kitabi, sannan an yi umarni da nuna musu girmamawa, jin kai da kyautatawa. Duk Kiristoci da Yahudawa sun yi imani da Allah kuma suna tarayya da Musulmai cikin kyawawan dabi'u. |
Al’amuran addinin kirista da na musulmai sun yi kama da juna a hanyoyi da dama.Addinin yahudanci ma yana tarayya da musulunci ta wasu al’amuran. A cikin Alkur’ani, Allah Yana fada mana cewa Musulmai suna tarayya da Ahlul Kitabi a al’amarin addini inda suke cewa da su “Mun yi imani da abin da aka saukar a gare mu kuma aka saukar a gare ku, kuma Abin bautawarmu da Abin bautawarku Guda ne, kuma mu masu sallamawa ne a gare Shi.” (Alkur’ani, sura ta 29, aya ta 46)
Duk mabiyan wadannan addinai guda uku:
Sun yi imani cewa Allah Ya halicci duniya baki dayanta inda ya kirkire ta ba daga komai ba sannan da cewa iliminsa ya game komai.
Sun yi imanin cewa Allah ya halicci mutum da sauran abubuwa masu rai cikin hikima da kudurarsa da kuma cewa Allah ya sanya wa mutum ruhi.
A yau gaba daya Musulmai da Ahlul Kitabi sun kaddamar da yunkurin yaki da dabi'un fasikanci kamar zina da shan miyagun kwayoyi. Kowanne daga cikin wadannan addinai uku ya yarda da kame-kai, gaskiya da kuma sadaukar da kai a matsayin kyawawan dabi'u. |
Sun yi imani da tashin bayan mutuwa, Aljanna da Wuta da mala'iku, da kuma cewa Allah Ya halicci rayukanmu ya rubutawa kowa makomarsa.
Sun yi imani cewa Allah ya aiko annabawa da yawa kamar Annabi Nuhu (AS), Annabi Ibrahim (AS), Annabi Ishak (AS), Annabi yusuf (AS) da Annabi Musa (AS) a tsawon tarihi, sannan kuma suna kauna duk wadannan annabawa.
A wata aya, an nuna cewa Musulmai ba sa banbancewa a tsakanin annabawa kamar haka:
Manzo ya yi imani da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da muminai. Kowannensu ya yi imani da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Ba ma rarrabewa a tsakanin daya daga manzanninSa. Kuma (muminai) suka ce, "Mun ji kuma mun yi da'a: (muna neman) gafararka, ya Ubangijinmu, kuma zuwa gare Ka makoma take." (Alkur'ani, sura ta 2, aya ta 285)
Musulmai ba su da matsala da addinan Ahkuk Kitabi, ba kawai a al’amuran addini ba, har ma da dabi’u na gari. A yau, a duniyar da ayyukan rashin kyakkyawar dabi’a irinsu zina, luwadi, shan kwayoyi da nau’o’in son kai da keta suka cika ko’ina, Musulmai da Ahlul Kitabi suna tarayya akan dabi’a iri daya: karramawa, gudun zina, kaskantar da kai, sadaukar da kai, gaskiya, tausayi, jin kai da kuma soyayya marar iyaka.
Adnan Oktar: Bani-Isra'ila zuriyar annabawa ne, su ne jikokin annabawanmu. Sannan suna bin shari'ar Annabi Musa (AS) inda suka adana dokokin shariar suna aiki da su har zuwa yau din nan. Saboda haka, abu ne da ya sabawa hankali da tunani a bar wadannan tsarkakan mutane suna gararamba ba tare da kasa ba, da yunkarin korar su daga kasarsu ta haihuwa ko kuma haramta musu rayuwa baki daya. An san musulmi da halin kyautatawa, tausayi da kuma soyayya. Yahudawa 'yan uwanmu ne kuma suna da hakkinsu na rayuwa. Mutane ne masu daraja, wadanda ke rayuwarsu, kasuwanci, yin ayyukan fasaha da na kumiyya yadda suke so a yankin. To don me za a kore su daga kasarsu ko kuma a hana musu hakkin yin rayuwarsu yadda suke so? Wannan abu ne da wanda zai yadda da shi. Ni ma ba zan yadda da shi ba. Tabbas za su yi rayuwarsu cikin farin ciki da aminci, kuma za a tsare musu rayukansu. Za su rayu cikin yalwar arziki da wadata karkashin Hadaddiyar Daular Musulunci ta Turkiyya. Abin da Alkur'ani ya fada a bayyane yake ga kowa, kamar yadda yake a sunnar Manzonmu (SAW). A zamanin Annabi, Ahlul Kitabi, Bani-Isra'ila, sun yi rayuwar aminci. Haka kuma a wancan zamani sun zauna a Kudus, a yankin Isra'ila. Sun yi rayuwar farin ciki da wadatar arziki kuma an nuna musu kauna da kyautatawa. Mutum zai iya auren 'yanmatan Yahudawa, ya zauna a teburinsu, ya ci abincin da suka dafa, ziyarci gidajensu har ya kulla abota da su. Wannan shine abin da ya gudana a zamanin Annabi (SAW) da kuma sunnarsa. Hakan kuma ya hada da Kiristoci. Kamar yadda ka sani, daya daga cikin kayangun Annabinmu (SAW) ta kasance kirista ce. Ita ce uwarmu, wadda muke tunawa da matukar girmamawa. Ba ina magana akan yahudanci ba ne kadai. Kiristoci ma mutane ne da ya wajaba mu ba su 'yancinsu na rayuwa cikin aminci, farin ciki da wadatar arziki. (The Gulf Today, Nuwamba 2008)
Adnan Oktar: Da farko, kuntatawa, tsawa da zagi ba su ne mafita ba, haka nan tsoro ko razana. Wajibi ne musulmi ya kasance mai amfani da tunaninsa sannan ya yi aiki kamar yadda Alkur'ani da kuma yadda Manzon Allah ya aikata. ya umarta. Wajibi ne ya dora dabi'arsa akan abin da Manzon Allah (SAW) ya yi, akan yadda abubuwa suke a zamanin sahabbai. Sahabbai sun kasance mutane masu kyakkyawan hali. Kuma Manzonmu (SAW) shine mafi kyawun hali a cikin mutane. Dabi'u da halayensa madaukaka sun yi cikar kamala da rashin aibu. Ya kasance mai nuna soyayya da bada kariya ga Ahlul Kitabi. Kyawun halaye da dabi'un Ma'aikinmu (SAW) sun birge su inda suka rika musulunta a kungiya kungiya, da ma al'umma a dunkule. To ta ya ya Kiristoci suka ga kyawawan dabi'unsa ba don ya yi mu'amala das u ba? Ta ya ya za su yi sha'awar shiga musulunci ba don ya kyautata musu ba? Saboda haka, kamar yadda na bayyana tun da farko, wajibi ne kowane musulmi ya koyi da matsayin da sahabbai suka dauka game da Ahlul Kitabi a zamaninsu. (Gidan talbijin na Kral Karadeniz TV, 25 January 2010)
Akidun musun samuwar Allah irin su farkisanci, gurguzu, wariyar launin fata da kuma akidar zaman kara-zube ta rashin bin doka sun jawo wa duniya bala'i kuma sun haddasa gaba a cikin al'umma. |
Wani kuma muhimmin al’amarin da ya kara hada kan Kiristanci, Yahudanci da kuma Musulunci shi ne falsafar akidun zindikanci wadanda suke da tasirin gaske a zamaninmu.
Daga cikin shahararru kuma mafiya hatsarin falsafar zamaninmu za a iya ambatar zahiranci, gurguzu, farkisanci, akidar zaman-kara-zube ta kin jinin gwamnati, wariyar launin fata, kin addini da kuma akidar ‘yan burin rayuwa. Mutane da dama wadanda suka gaskata bayanan wadannan ra’ayoyi na yaudara da karyar samar da mafita ga matsalolin da mutum, al’umma da kuma duniya ke ciki, tuni sun dawo daga rakiyar su ko kuma sun fara jin shakku akan su. Abin day a rage, wadannan akidu sun jefa mutane, al’ummu da kuma kasashe cikin rikici, tashin hankali da yakukuwa. Kamashon zunubinsu na wahalhalu da bala’in da bil-adama suka shiga daga yau ba karami ba ne.
Yayin da suke musun samuwar Allah da kuma ikon yin halitta, duk wadannan akidu da aka fada a sama sun ginu ne akan hadafi daya, wani tsarin kimiyya na karya; wayo Labarin Rudun halitta na Charles Darwin. Darwiniyanci shine asasin falsafar akidun zindikanci. A takaice wannan labara yana ikrarin – ba tare da wata hujjar kimiyya ba – cewa wai halittu masu rai sun samu ne ta hanyar katari ko dace da kuma ta gwagwarmayar rayuwa. Saboda haka, Darwiniyancew ke aika wannan sakon yaudara da rudi ga mutane:
"Babu hakkin kowa a kanka, rayuwarka ta samu ne a bias katari ko dace, kana bukatar ka yi da gaske, kuma in ya zama dole kana iya murkushe sauran mutane don ka cimma burinka. Wannan dukiya gidan rikici ce da son-kai".
Sakonnin rayuwa da tsarin Darwiniyanci ke fitarwa irinsu “Zabi na dabi’a,” In baka yi ba ni wuri,” “Karfinka ya kwace ka” duk hanyoyi ne masu hatsari na jawo hankalin mutane. Wannan muguwar dabi’a tana cusa wa mutane girman kai, son kai, keta da danniya. Tana rusa dabi’u irinsu jin kai, tausayi, sadaukar da kai da kuma kaskantar da kai, kyawawan dabi’u na addinan tauhidi guda uku, inda ta ke gabatar da hakan tamkar shine wajibin “tsarin rayuwa.”
Wannan hanyar jawo mabiya ta masu akidar Darwiniyanci kishiyar tsarin addinan Ahlul Kitabi ce da kuma koyarwar Alkur’ani. Sakamakon haka, hanyar jawo mabiya ta masu akida Darwiniyanci ginshiken duniyar da ke adawa da duk saukakkun addinai guda uku.
Tunda haka ne, to ya zama wajibi ga Ahlul Kitabi da Musulmai su hada kai, tunda sun yi imani da Allah kuma sun karbi dabi’un da Ya ke koyarwa. Ya kamata mabiya wadannan addinai guda uku su fallasa karyar Darwiniyanci, wadda bat a da wani tushe a kimiyya, amma wadda mutane k eta hankoron rikewa kawai don falsafar zahiranci, ga duniya. Kamata ya yi su hada hannu wajen aiwatar da gwagwarmayar ilimi akan dukkan akidun yaudara (gurguzu, farkisanci, wariyar launin fata) wadanda reshe ne na zindikanci. Yayin da haka ta samu, a cikin dan lokaci duniya za ta rungumi hanayar aminci, kwanciyar hankali da adalci.
Burin Darwiniyanci shine samar da al'ummar da a cikinta ake ganin tashin hankali da rikici a matsayin hanyoyin cigaba. Amma wani nazari da aka gudanar kan tasirin akidar akan al'umma ya nuna cewa Darwiniyanci ya kawo kunci da halaka ne kawai. |
Azabtarwar da aka yi wa Yahudawa a tsawon tarihi sakamako ne na akidar wariyar launin fata, wadda ta saba wa Musulunci. Babu wani Musulmi da zai goyi bayan rashin adalci ko nuna halin keta ga Yahudawa da kuma yaran da ba su yi laifin komai ba. |
A zamaninmu, akidar kin jinin Yahudu ta kasance akidar da ke yin barazana ga zaman lafiyar duniya inda ta ke yaki da walwala da kuma tsaron talakawa. Wannan kiyayyar wariyar launin fat ace da wasu ke yi wa Yahudawa.
A karni na 20, akidar kin jinin yahudu ta yi kaurin suna ta hanyar aiwatar da wasu munanan ayyukan ta’addanci, daga cikinsu wanda ya fi muni shine kisan kare-dangi da ‘yan Nazi suka yi wa Yahudawa. Kari akan wannan, a kasashe da dama azzaluman gwamnatoci sun sa Yahudawa a gaba inda suka gana musu bakar azaba. Kungiyoyin masu akidar Farkisanci sun tsangwami Yahudawa inda suka yi ta kashe su ba kakkautawa.
To a wane matsayi musulmi zai dauki akidar kin jinin Yahudu?
Amsar a sarari ta ke. Wajibi ne kowane musulmi ya ki akidar kin jinin Yahudu kamar yadda zai ki duk wata akidar wariyar launin fata. Dole ne ya yaki wannan akida mai cike da gaba sannan ya kare ‘yancin Yahudawa, kamar yadda zai kare ‘yancin kowane mutum a duniya. Wajibi ne kowane musulmi ya girmama tare da kare hakkin dukkan Yahudawa a duniya, a Isra’ila suke ko sauran sassan duniya, don su tafiyar da rayuwa da bautarsu cikin ‘yanci, su tsare al’adarsu da kuma ‘yancin bayyana ra’ayinsu.
Hanin yi wa wata al’umma fyaden ‘ya’yan kadanya umarni ne day a zo a Alkur’ani, akwai bukatar bambancewa tsakanin na kirki da mutanen banza, mugaye da na gari. Alkur’ani ya bayyana kyawun dabi’ar da Yahudawa da Kiristoci suke nunawa kamar haka:
Ba su zama daidai ba; daga Mutanen Littafi (Ahlul Kitabi) akwai al'umma wadda take tsaye, suna karatun ayoyin Allah a cikin sa'o'in dare, alhali kuwa suna masu yin sujada. Suna imani da Allah da Ranar Lahira, kuma suna umarni da kyakkyawa kuma suna hani daga mummuna, kuma suna gaggawa a cikin alherai.Kuma wadannan suna cikin salihai. Kuma abin da suka aikata daga alheri, to ba za a yi musu musunsa ba. Kuma Allah Masani ne ga masu takawa. (Alkur'ani, sura ta 3, aya ta 113-115)
Musulmai suna son ganin sun zauna lafiya da Kiristoci da kuma Yahudawa cikin hakuri, fahimtar juna, abota, girmamawa da kuma tausayin juna. |
Akidar kin jinin yahudu akida ce da ta sabawa addini wadda ta samo asali daga maguzancin zamani. Saboda haka, abu ne mai wuya a ce wai ga Musulmi yana yada akidar ko kuma yana goyon bayan ta. ‘yan akidar kin jinin Yahudu bas a ganin girman annabawan Allah Ibrahim (AS), Musa (AS) ko Annabi Dawud (AS) wadanda annabawa ne da Allah Ya zabe su don su zama misalai abin koyi ga ‘yan Adam.
Akidar kin jinin yahuda da kuma sauran nau’in akidun wariyar launin fata (misali kin jinin bakar fata) ba su da gurbi a cikin addinin gaskiya; baudaddun ra’ayoyi ne kawai da suka fito daga akidu da camfe camfe daban daban.
Bugu da kari, idan muka yi nazarin akidar kin jinin yahudu da kuma sauran nau’in wariyar launin fata, za mu ga cewa suna yada manufa da tsari na al’umma wadda ta yi hannun riga da koyarwar Alkur’ani. Misali, a cikin akidar kin jinin yahudu ake samun kiyayya, tashin hankali da kuma rashin tausayi. Mai ra’ayin kin jinin yahudu ya kan kai matuka wajen mugunta inda ya kan taimaka a kashe Yahudawa, maza, mata, yara da kuma tsofaffi, sa’annan da goyon bayan azabtar da su. Amma kuma kyakkyawar koyarwar Alkur’ani tana horo da nuna soyayya, tausayi da jin kai ga dukkan mutane. Sannan kuma tana umartar Musulmai da su nuna adalci da yin afuwa hatta ga makiyansu.
A daya bangaren kuwa, ‘yan kin jinin yahudu da sauran ‘yan wariyar launin fata sun tsani su ga mutanen suna zaman tare da mabambantan jinsi ko akida (misali ‘yan wariyar launin fata na Jamus (‘yan Nazi) sun tsani zaman tare tsakanin Jamusawa da Yahudawa). Sai dai, Alkur’ani bai nuna wani bambanci tsakanin jinsina ba; Alkur’ani yana kira ne don hadin kai da zaman tare tsakanin mutane masu bin addinai daban daban a cikin al’umma guda cikin farin ciki da aminci.
A Alkur’ani, akwai wani bayyanannen bamabnci tsakanin Ahlul Kitabi da kuma wadanda ba su yi imani da Allah ba. Musamman an fi jaddada wannan a bangaren zamantakewar rayuwa. Ga misali, an fada game da wadanda suke hada bautar wasu da ta Alla cewa: “najasa ne, saboda haka kada su kusanci Masallaci Mai alfarma a bayan shekararsu wannan.” (Alkur’ani, sura ta 9, aya ta 28) Wadanda ke hada bautar wasu da Allah mutane ne da ba su san dokokin Allah ba, ba su da dabi’ar kirki wadanda kuma sukan iya aikata duk wani mummunan aiki ba tare da tunani ba.
Amma Ahlul Kitabi, da yake sun dogara akan abin da Allah ya saukar, suna da kyakkyawar dabi’a kuma sun san abin da yake halal da kuma wanda yake haram. Akan haka, an baiwa musulmi izinin aurar mace daga cikin Ahlul Kitabi. A kan wannan al’amari Allah Yana cewa:
A yau an halatta muku abubuwa masu dadi, kuma abincin wadanda aka bai wa littafi halal ne a gare ku, kuma abincinku halal ne a gare su, da mata masu kamun kai daga muminai da mata 'ya'ya daga Wadanda aka bai wa Littafi gabaninku, idan kunje musu da sadakokinsu, kuma masu yin aure, ba masu yin zina ba, kuma ba masu rikon abokai ba. Kuma wanda ya kafirta da imani, to lalle ne aikinsa ya baci, kuma a lahira yana daga masu hasara. (Alkur'ani, sura ta 5, aya ta 5)
Wadannan umarni suna nuna za a iya kulla dangantakar ‘yan uwantaka ta hanyar auren musulmi namiji da kuma mace daga Ahlul Kitabi sannan kuma mutanen kowane bangare kan iya amsar gayyatar cin abinci. Wadannan sune ginshikan al’amuran da za su tabbatar da kafuwar dangantakar mutumtaka mai adalci da kuma zaman tare cikin farin ciki. Tun da Alkur’ani ya yi horo da wannan hali na adalci da tausayi, abu ne mai wuya a ce musulmi ya bi kishiyar haka.
Adalci da tausayi da Annabi (SAW) ya nuna akan Ahlul Kitabi sun kasance kyawawan misalai abin koyi ga Musulmai. A cikin yarjejeniyar da aka kulla da Kiristocin Najran, wadanda suka zauna a kudancin kasar larabawa, Manzo Muhammad (SAW) ya bayyanar da daya daga mafi kyawawan misalai na jin kai da adalci. Yarjejeniyar ta kunshi wannan sidirar:
- Rayukan mutanen Najran da zagayenta, addininsu, kasarsu, kadarorinsu, dabbobi da wadanda suke nan da wadanda ba sa nan, 'yan aikensu da kuma wuraren bautarsu suna karkashin kariyar Allah da kuma wakilcin AnnabinSa.19
Ta hanyar wadannan yarjejeniyoyi, Ma’aikin Allah (SAW) ya kafa tsarin rayuwa ga musulmai gami da Ahlul Kitabi, wanda ke cike da ainci da tsaro. Wannan tsari shine matukar cikar wannan aya:
Lalle ne wadanda suka yi imani, da wadanda suka tuba, da Nasara da Makarkata, wanda ya yi imani da Allah da kuma Ranar Lahira, kuma ya aikata aikin kwarai, to suna da ladansu a wurin Ubangijinsu, kuma babu tsoro a kansu, kuma ba su zama suna yin bakin ciki ba. (Alkur'ani, sura ta 2, aya ta 62)
A zamanin Ma'aiki Muhammad (SAW), an aiwatar da tsarin gwamnati mai adalci da tausayawa game da Ahlul Kitabi. |
Tsarin mulki na Madina ya kasance mafi muhimmancin yarjejeniya da ta tsayar da adalci da aminci a tsakanin al’ummun Kiristoci, Yahudawa da kuma maguzawa.
An tsara tsarin mulkin Madina karkashin jagorancin Manzon Allah (SAW) shekaru 1,400 da suka wuce, wato a shekara ta 622 (lissafin kirista), don kula da bukatun rayuwa na mutane masu bambancin addini, sannan aka dabbaka shi a matsayin yarjejeniyar doka. Al’ummu daban dandan masu bin addinai da jinsi daban daban, wadanda suka yin zaman gaba da juna na tsawon shekaru 120, da su aka zayyana wannan yarjejeniyar dokar. Da wannan yarjejeniya, Ma’aikin Allah (SAW) ya nuna cewa rikicin da ke tsakanin wadannan al’ummu, wadanda suka kasance makiyan juna da kuma suka kasa sulhu a tsakaninsu, zai iya karewa inda za su iya zaman lafiya da junansu.
Kamar yadda yake a cikin tsarin mulkin Madina, kowane mutum yana da ‘yancin bin addini, ra’ayin siyasa ko falsafar da yake so. Mutanen da ke tarayya a ra’ayiguda za su iya haduwa su kafa al’umma guda. Kowa yana da ‘yancin kafa tsarin shari’arsa. Amma kuma, duk wanda ya aikata laifi ba mai ba shi kariya. Al’ummun da ke cikin wannan yarjejeniya za su ci gaba da hadin kai da juna, su bayar da goyon baya ko tallafi ga junansu, sannan za su kasance karkashin kariyar Annabi Muhammad (SAW). Idan sun sami sabani za a kawo wajen Manzon Allah (SAW) don ya yi hukunci.
Wannan yarjejeniya ta yi aiki tun daga shekarar 622 zuwa 632 (shekarar kirista). Ta hanyar wanna kundi, aka soke tsarin kabilanci wanda a da ya ginu akan jini da ‘yan’uwantaka, inda mutane daga al’adu, kabilu da kuma yankuna daban daban suka hadu cikin hadin kai. Tsarin mulkin Madina ya samar da cikakken ‘yancin addini.
Wani muhimmin al’amari da za mu koya daga Alkur’ani shine cewa wajibi ne Musulmai su girmama wuraren bautar Yahudawa da Kiristoci. A cikin Alkur’ani, an ambaci wuraren bautar Ahlul Kitabi, wato gidajen ibada, majami’u da wuraren bautar yahudawa, da wuraren bauta karkashin kariyar Allah.
… ba domin tunkudewar Allah ga mutane, sashensu da sashe ba, da an rusa sauma'o'in (Ruhubanawa) da majami'o'in Nasara da gidajen ibadar yahudu da masallatai wadanda ake ambaton Allah a cikinsu da yawa. Kuma lalle Allah Yana taimakon wanda yake taimakonSa. Lalle Allah Mai karfi ne, Mabuwayi. (Alkur'ani, sura ta 22, aya ta 40)
Wannan aya tana nunawa kowane musulmi muhimmancin girmamawa da kuma kare wurare masu tsarki na Ahlul Kitabi.
Tabbas, Ma’aiki Muhammad (SAW) shi ma ya kulla yarjejeniyoyi da maguzawa da kuma Ahlul Kitabi. Koda yaushe ana yin mu’amala da maguzawa cikin adalci, kuma yayin da suka nemi a sanya su karkashin kariya, Muhammad (SAW) ya amsa bukatarsu. Wannan yana nufin eadannan al’ummu sun nemi kariyar Ma’aikin Allah (SAW) a lokacin hari ko kulla sharri. A tsawon rayuwar Annabi (SAW), da yawan wadanda ba musulmi ba tare da maguzawa sun nemi kariya daga gareshi, inda kuma ya ba su kariya tare da tabbatar da tsaronsu. A Alkur’ani Allah yana umartar musulmai da su bayar da kariya ga maguzawa yayin da suka zo da bukatar hakan. A kan haka, Allah Allah Yana cewa:
Idan wani daga mushirikai ya nemi makwabtakarka, to ka ba shi makwabtakar har ya ji maganar Allah, sa'annan ka isar da shi ga wurin amincewarsa… (Alkur'ani, sura ta 9, aya ta 6)
Yahudawa da Kiristoci, saboda abubuwan da suka yi tarayya da Musulmai, sun fi kusanci da Musulmai akan marasa imani. Kowanne daga cikin wadannan addinai yana da littafinsa, wato suna aiki ne da littafi da Allah ya saukar. Sun san abu mai kyau da marar kyau, abin da yake halal da na haram kamar yadda littattafansu suka fasalta, kuma dukkansu suna girmama annabawa da manzanni da suka zo musu. Duk sun yi imani da ranar lahira, da kuma rayuwa bayan mutuwa lokacin da za su yi wa Ubangiji bayani game da dukkan ayyukansu. Saboda haka, akwai asali ko ginshiken da aka yi tarayya akansa wanda za mu iya haduwa akansa.
Dangane da Ahlul Kitabi, Allah Yana baiwa musulmai umarni a cikin Alkur’ani; su hadu akan kalma daya:
Ka ce: "Ya ku Mutanen Littafi! Ku taho zuwa ga kalma mai daidaitawa a tsakaninmu daa ku: kada mu bautawa kowa face Allah. Kuma kada mu hada komai da Shi, kuma kada sashenmu ya riki sashe Ubangiji, baicin Allah." (Alkur'ani, sura ta 3, aya ta 64)
Masallatai, Majami'u da kuma wuraren bautar Yahudawa wurare ne na musamman don ibada da ake girmama sunan Allah. Allah Yana fada a cikin Alkur'ani cewa dole ne a girmama tare da tsare duk wadannan wurare masu tsarki. |
Tabbas wannan shine kiranmu ga Kiristoci da Yahudawa: A matsayin mutanen da suka yi imanni da Allah kuma suke bin abin da Ya saukar, ku zo mu hadu kan kalma guda – “imani.” Ku zo mu so Allah wanda Shine Mahalicci kuma Ubangijinmu, sannan mu bi umarninSa. Sannan ku zo mu yi addu’a ga Ubangiji don Ya shiryar da mu zuwa ga mikakken tafarki.
Wajibi ne duk masu imani su yi wa junansu addu'a da kuma hadin kai da juna.
Yayin da Musulmai, Kiristoci da Yahudawa suka hadu kan kalma guda ta wannan siga; yayin da suka fahimci cewa su abokan juna ne ba makiya ba, yayin da suka gane cewa babban makiyi shine musun samuwar Allah, daga nan duniya za ta canja, ta gyaru. Yakukuwan da ake yi a sassan duniya da dama, kiyayya, fargaba da kuma harin ‘yan ta’adda duk za su zo karshe, inda kuma za a kafa sabon tsarin rayuwa da ya ginu akan soyayya, girmama juna da kuma aminci a birbishin wannan “kalma guda daya.”
Abin muhimman abubuwan lura ga Musulmai. Abin da Allah Ya ke koyar da mu a cikin Alkur’ani game da mabambantan mutane da akudu a bayyane ya ke:
Koyarwar Alkur'ani ba ta kunshi duk wani nau'in wariyar launin fata ba.
An yi umarni a cikin Alkur'ani kan mu nuna wa sauran addini halin daidaito da abota.
Sabah, 19.09.01 - Bayan harin 11 ga Satumba, mutane daga kowane yare da addini sun yi addu'a don nuna tausayawa da goyon baya.
Türkiye, 16.09.01 - Muzammil Siddique, Shugaban Kungiyar Al'ummar Musulmi ta Amurka ta Arewa, ya karanta ayoyi daga Alkur'ani Mai girma a taron addu'ar da aka yi a majami'ar National Cathedral da ke birnin Washington bayan harin 11 ga Satumba.
Star, 18.09.01 - Bush ya ziyarci Cibiyar Musulunci da ke Washingon.
After the attacks of September 11, people of every language and religion prayed to Allah in empathy and solidarity with the victims. |
Sanannen abu ne cewa wasu daga cikin Yahudawan zamunan baya sun aikata kuskure da yawa wadanda aka ambata kuma aka yi Allah-wadai da su a cikin Alkur’ani. To amma bai kamata Musulmai su dauki wadannan a matsayin hujjar yin gaba da Yahudawa ba. Ba za a jingina laifukan da wasu daga cikin Yahudawa wadanda akidun zindikanci suka yi wa tasiri suka aikata ba. Akan addinin Yahudanci dakuma al’ummar Yahudawa.
Har ila yau, wani babban al’amari da Alkur’ani ya bayyana shine na hanin yanke hukunci akan al’amari mutane kawai saboda bambancin jinsi, kasa ko kuma addininsu. A kowace al’umma, akwai mutane mutanen kirki kamar yadda yake akwai na banza. An bayyana wannan bamabanci a cikin Alkur’ani. Misali, bayan ambaton dabi’ar kafirci – ga Allah da addininSa – ta wasu daga cikin Yahudawa da Kiristoci, akwai nuni da cewa ba dukkansu ba ne, sannan sai Allah ya ce:
Ba su zama daidai ba; daga Mutanen Littafi (Ahlul Kitabi) akwai al'umma wadda take tsaye, suna karatun ayoyin Allah a cikin sa'o'in dare, alhali kuwa suna masu yin sujada. Suna imani da Allah da Ranar Lahira, kuma suna umarni da kyakkyawa kuma suna hani daga mummuna, kuma suna gaggawa a cikin alherai.Kuma wadannan suna cikin salihai. Kuma abin da suka aikata daga alheri, to ba za a yi musu musunsa ba. Kuma Allah Masani ne ga masu takawa. (Alkur'ani, sura ta 3, aya ta 113-115)
1. Time, 01.10.01, 2. Planet Easton, 01.11.01 |
A wata ayar, Allah Yana cewa:
Kuma lalle mun aika a cikin kowace al'umma da wani Manzo (ya ce), "Ku bauta wa Allah, kuma ku nisanci Dagutu." Daga cikinsu akwai wanda Allah Y ashiryar, kuma daga cikinsu akwai wanda bata ya wajaba akansa. Ku yi tafiya a cikin kasa, sannan ku duba yadda karshen masu karyatawa ya kasance. (Alkur'ani, sura ta 16, aya ta 36)
Allah Ya yi wahayi zuwa ga dukkan manzanni cewa Shi daya ne kuma babu wani abin bauta da yi wa biyayya sai Shi. An isar da sakon Allah, wanda Allah ya aiko zuwa ga mutane da hanyar manzanninSa, ga mutane tun farkon halittar mutum. Wasu al’ummun sun karbi sakon suka bi tafarkin gaskiya, yayin da sauran suka karyata suka yi tawaye gareshi. Haka ma abin ya ke a wannan zamani. Wasu mutane za su kasance tare da masu gaskiya yayin da wasu kuma za su kutsa cikin barna. Haka tsarin Allah ya ke. Wadanda suka yi imani ya kamata kuma su rungumi wannan fikira sannan kar su mance cewa za a iya samun mutane tsarkakan mutane masu gaskiya da ke da tsoron Allah daga cikin mabiya dukkan addinai sannan kuma da wadanda suka baram baram da tsarin addini.
Fatanmu shine a kafa duniya wadda a cikinta mutane za su iya zama tare cikin aminci, duk da irin bambancin addini ko jinsin su, wadda a cikinta za a yi watsi da batattun akidun wariyar launin fata, za a kare hakkin kowa sannan kuma da girmama kowa. Gwagwarmayar wadda za a gina ta bisa ginshiken ilimi don nyaki da dukkan akidun kin jinin addini, ana fatan za ta samar da zaman lafiya da amincin da aka dade ana hankoro. A game da haka, Allah yana cewa a cikin Alkur’ani:
Wadanda suka kafirta sashensu ne waliyyan sashe, idan ba ku aikata shi ba, wata fitina za ta kasance a cikin kasa da fasadi babba. (Alkur'ani, sura ta 8, aya ta 73)
To don me masu hankali ba su kasance daga mutanen karnonin da suke a gabaninku ba, suna hani daga barna a cikin kasa? Face kadan daga wanda muka kubutar daga gare su (sun yi hanin). Kuma wadanda suka yi zalunci suka bi abin da aka ni'imtar da su a cikinsa, suka kasance masu laifi. (Alkur'ani, sura ta 11, aya ta 116)
Those who perform good actions will receive better than them ...
(Surat an-Naml, 89)
Adnan Oktar: Game da yadda Amurka ke daukar Musulmai a matsayin 'yan ta'adda, akwai dalilai biyu. Da farko dai, babu ta'addanci a musulunci, wannan a bayyane ya ke. Musulunci yana nufuin soyayya, taussayi, jin kai, yafiya da afuwa; Allah ma Yana son mu yi afuwa hatta ga wanda ya yi kisa. Akwai tsarin fitar da hakki a hukuncin kisa a cikin Alkur'ani amma Allah Yana cewa zai fi alheri idan muka yi afuwa. Rashin hikima da lura ne zai sa wai a ga gyauron ta'addanci a cikin addinin da yake koyar da wannan. Allah Madakaki Yana son mu yi afuwa hatta ga wanda ya yi kisa; wannan addini ne na aminci da soyayya. Musulunci cike yake da afuwa; akwai yin afuwa a cikin komai. Yi afuwa, yi umarni da kyakkyawa da hani da mummuna. Soyayya, jin kai, tausayi da hadin kai; duk an yi bayaninsu (a cikin Alkur'ani). Amma akwai 'yan ta'adda wadanda suke aikata ta'addanci. Dan ta'adda yana aiki ne da jahilci inda, misali, ya ke jefa bam akan fararen hula. Ya kan jefa bam a wajen da ya san akwai mata da yara. Shin wannan musulmi ne? Wannan abin tambaya ne. Ban sani ba ko irin wadannan mutane Musulmai ne. Da farko dai zai zama ba ma'ana a kira su da musulmai sannan kuma a zo ana jimamin taaddancin da musulmi ya aikata. Da farko muna bukatar mu tantance in wadannan mutane musulmai ne ko a'a. A ra'ayina, idan mutum ya kashe yaro da gangan, wannan ba musulmi ba ne. Wannan ba abin yarda ba ne. Matasa masu akidun Darwiniyanci, zahiranci da kuma Markisanci suna sha'awar musulunci a wasu lokutan amma wannan ba ya canja su daga matsayinsu na Markisawa ko Darwiniyawa. Suna aikata ta'addancin gurguzu da sunan musulunci. Abin nufi shine, duk wani abu da ya yi a matsayin dan gurguzu, to yana yi ne da sunan musulunci sannan yana ikrarin cewa ya halasta. Amma gaskiyar lamari ita ce wannan mutum yana dauke da kuduri da manufar ta'addanci a cikin ruhinsa. Ian bai kira kansa musulmi ba, ya kan yi wadannan munanan ayyuka ne a matsayin mabiyin Markisanci. Idan kuma ba haka ba, to a dan farkisanci. Ya kan yi hana a dukkan yanayi. Wannan na nufin, yana da ciwo a ruhinsa. Saboda haka cewa wai akwai ta'addanci a musulunci yana nuna gurguwar fahimta ga musuluncin. Wannan mummunan kuskure ne. Musulunci addini ne na zaman lafiya kamar yadda za mu fahimta daga ma'anar kalmar 'islam' wadda ke nufin aminci ko zaman lafiya. Saboda wannan dalili, babu wani mai tunani da zai yarda da wannan. (Gidan talbijin na Denge, 9 ga Disamba 2008)
Adnan Oktar: Ta ya ya ta'addanci zai zauna a musulunci? Musulunci kamar ruwa ne yayin da ta'addanci ya ke wuta. Musulunci ruwa ne da ke kashe wuta.Shin wuta za ta iya kona ruwa? Ruwa yana kashe wuta. Sakamakon haka, tun da soyayya, tausayi, jin kai, girmamawa, zurfin tunani, gaskiya, hadin kai duk dabi'u ne na addini, abu ne mai wuya addini ya goyi bayan ta'addanci. Babu wannan a tsarin Musulunci. Hakika, yayin da wani ya kashe mutum, Allah yakan ce an gafarta masa. Allah yana cewa abin zargi ne ma idan ba ba yafe masa ba. Shin irin wannan addini zai goyi bayan ta'addanci? (Associated Press Ta Pakistan, 6 ga Satumba 2008)
Ma'aiki (SAW) ya kasance yana isar da mu'amala da duk wani bangare na al'umma kuma yana ganawa da daidaikun mutane, tun daga kan shugabanni har zuwa fursunonin yaki, yara da kuma marayu. Ta hanyar hada kan mutane daga duk sassan rayuwa, hali, yana yi da al'adu, sai ya assasa tattaunawa mai amfani, ya sami nasarar jawo hankulansu inda ya nuna hakuri da kyakkyawar fahimta garesu.
Kamar yadda sahabbai na kusa da shi suka ruwaito, Manzonmu (SAW) ya kasance "mai matukar kyautatawa, halinsa ya wuce kushewa, mai kyauta, abin so kuma mai saukin kai." Lafazinsa da ya ce, "An aiko ni don in kyautata kyawun halayya" (Mishkat Shareef) nuni ne ga madaukakiyar dabi'arsa. Aisha, wadda ta san halinsa kwarai, ta bayyana dabi'arsa mai ban sha'awa a cikin wadannan kalmomi: "Dabi'ar Annabi Alkur'ani." (Hadisin Sahih Muslim)
Anas, wanda shi a gidan Manzon Allah (SAW) ya girma kuma ya yi masa hidima na tsawon shekaru, ya fasalta kawaicin Manzon Allah kamar haka:
Ma'aikin Allah (SAW), ya kasance in ya yi musabaha da mutum, ba ya janye hannunsa har sai shi mutumin ya fara janye nasa. Haka kuma, ba ya dauke fuskarsa daga mutum har sai mutumin ya kauda fuskarsa tukuna. Kuma ba a taba ganinsa ya tura guiwarsa a gaban wanda suke zaune tare ba. ('Ma'ariful Hadith' (Ma'anonin Hadisi) na Maulana Muhammad Manzur Nu'umani, Darul-Ishaat Publications, Karachi, Mujalladi na 4, shafi na 334)
Idan wani yana magana da shi to yakan yi shiru ya saurare shi har sai ya gama maganarsa. (Abubuwan da ke cikin Shamaa-il Tirmizi, (334) Hadisi na 9)
Anas bin Malik (ra) ya kasance yana cewa, "Na kasance ina yi wa Ma'aikin Allah (SAW) hidima har tsawon shekaru goma. Bai taba gaya min bakar magana ba. Idan na yi wani abu, bai taba ce mini 'me ya sa ka yi haka?' ba. Kuma idan ban yi wani abu da ya kamata in yi ba, bai taba cewa me ya sa ban yi shi ba. (Shamaa-il Tirmizi, Islamic Book Service Publications, New Delhi, 2000, shafi na 362)
A tsawon rayuwar Manzon Allah (SAW), ya ilmantar da dubban mutane. Ta hanyar kokarinsa, mutanen da a baya ba su san komai game da addini ba suka zama masu saukin kai, wadanda ke shirye su sadaukar da kansu, masu kyawun hali da madaukakiyar dabi'a. Ko a yanzu, karnoni da yawa bayan rasuwar sa, Manzaonmu shine mafi kyawun mai shiriya kuma malami, wanda lafazai da dabi'arsa ke ci gaba da yin tasiri akan biliyoyin mtane.
Annabinmu (SAW) ya hori masu imani da su kasance masu nuna soyayya Manzonmu (SAW) ya bayyana cewa yana da matukar muhimmanci masu imani su so junansu tare cikakkiyar kauna, ba tare da sanya bukatun kansu ba, sannan kuma kar su kullaci mugun nufi kamar tsana, fushi da hassada.
A cikin Alkur'ani, Allah Yana umartar ManzonSa (SAW) ya ce:
Wancan shi ne Allah ke yin bushara da shi ga bayinSa wadanda suka yi imani kuma aikata ayyukan kwarai. Ka ce, 'Ba na tambayarku wani lada a kansa, face dai soyayya ga makusanta." Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, za Mu kara masa kyau a cikinsa. Allah Mai gafara ne, Mai godiya. (Alkur'ani, sura ta 42, aya ta 23)
Wasu hadisai dangane da nuna kauna, abota da kuma 'yan uwantaka na Annabi (SAW) suna cewa:
Mumini yana so wa 'yan uwansa abin da ya so ga kansa.(Ihya Ulumuddin (Littafin Koyon Addini) na Imam Ghazali, madaba'ar Islamic Book Service, New Delhi, 2001, Mujalladi na 3, shafi na 68)
Manzon Allah (SAW) ya kasance yana karbar kyauta kuma ya kan bayar da tukuici. (Sahih Bukhari, madaba'ar Islamic Book Service, New Delhi, 2002, Mujalladi na 3, shafi na 597)
Duk wanda aka yi wa kyautar furen ganyen kamshi kar ya ki karba, saboda ba shi da nauyi kuma mai dadin kamshi. (Riyadus Salihin, mujalladi na 2, wanda Imam Abu Zakariyya Yahya bin Sharaf An-Nawawi Ad-Dimashqi ya hada, shafi na 1330)
Kada ku yi gaba da junanku, kada ku yi wa juna hassada, kada ku yi ciniki akan cikin junanku, kada ku yi jayayya da juna sannan kada ku yi zunden junanku. Bayin Allah 'yan uwan juna ne. (Ihya Ulumuddin (Littafin Koyon Addini) na Imam Ghazali, madaba'ar Islamic Book Service, New Delhi, 2001, Mujalladi na 3, shafi na124)
Halayyar wadanda suka gabace ku ta kama ku – hassada da gaba. Hassada aski ne. Ba za ku shiga aljanna ba har sai kun yi imani. Ba za ku yi imani ba har sai kun so juna. Shin ba zan sanar da ku abin da zai tabbatar da ku akai ba? Ku yada aminci tsakanin ku. (Ihya Ulumuddin (Littafin Koyon Addini) na Imam Ghazali, madaba'ar Islamic Book Service, New Delhi, 2001, Mujalladi na 3, shafi na 167)
Mai karfi ba shi ne wanda ya yi kaye a kokawa ba, sai dai wanda ya iya rike zuciyarsa yayin fushi. (Hadisin Sahih Bukhari)
Ku kiyayi hassada, domin hassada tana cin kyawawan ayyuka kamar yadda wuta ke cin itace. (Hadisin Abu Dawud)
Musulmai 'yan uwan juna ne. Kada su yi cuta, karya ko wulakanta junansu. (Hadisin Tirmizi)
Da dokokin da ya mikawa musulmai; Ma'aikinmu ya kasance, da adalcinsa da kuma fahimta ga sauran addinai, jinsi, harsuna da kuma kabilu sannan da daidaiton mu'amalarsa da kowa, mai arziki da talaka, babban abin koyi ne ga dukkan bil-adama. A wata aya, Allah ya gaya masa "Amma idan za ka yi hukunci, ka yi hukunci tsakaninsu da adalci. Allah Yana son masu adalci." (Alkur'ani, sura ta 5, aya ta 42) Annabi (SAW) bai taba yin sassauci a cikin al'amarin adalci ba, koda kuwa a wane irin hali ne.
Al'amura da yawa da suka faru a rayuwar Annabi (SAW) sun tabbatar da kyakkyawar dabi'arsa abar koyi. A kasar da ya rayu, mabambantan addinai, jinsi da kuma kabilun mutane sun zauna tare. Wadannan alu'ummu sun kasa zaman lafiya da junansu balle har su hana wadanda ke son tayar da fitina a tsakaninsu. Amma kuma adalcin Annabinmu (SAW) shi ya samar da aminci da tsaro ga wadanda ba musulmai ba fiye da su kan su musulman. A zamaninsa, duk wanda ke zaune a tsibirin larabawa – Kirista, Bayahude ko bamaguje – an yi masa adalci ba tare da nuna bambanci ba.
Kyawawan halayen Ma'aikinmu (SAW), wadanda tushensu Alkur'ani ne, sun kasance misalai abin koyi ga mabiya wasu addinai inda ya nuna musu yadda za su yi mu'amala da junansu. Adalcinsa ne ya jawo sassaucin ra'ayi tsakanin mutane mabambantan jinsi.
A cikin jawabansa da dama, hatta a Hudubar Ban-kwana, ya tabbatar da cewa jinsin mutum ko matsayinsa ba zai ba shi daukaka ba. Daukaka tana samuwa ne daga tsoron Allah, kamar yadda Allah ya fada a cikin Alkur'ani: "Ya ku mutane! Hakika mun halicce ku daga tsatson namiji da mace, sannnan muka sanya ku jinsi da kabilu don ku san juna. Mafi daukakar ku a gurin Allah shine mafi takawa a cikinku. Allah Masani ne, Mai yalwar ilimi. (Alkur'ani, sura ta 49, aya ta 13) Hadisai akan wannan yana cewa:
Ku 'yayan Adam ne, Adam kuwa daga yumbu aka halicce shi. Mutane su daina alfahari da tsatson asalinsu. (Sunan Abu Dawud, Littafi na 41, Lamba ta 5097)
Wannan tsatson asalin naku bai isa abin yi wa wani gori ba. Dukkanku 'ya'yan Adam ne. Babu wanda ke da wata daukaka kan wani, sai a addini da takawa. (Ahmad, 158/4)
Ma'aikinmu (SAW) bai taba burin yaki ba kuma a tsawon shekaru ya yi ta kokarin yada musulunci ta hanyoyin aminci da lumana. Ya yi hakuri akan kuntatawa da cutarwa. Sai da ta kai babu makawa face sai an gwabza, sannan ne ya bayar da umarnin fita yaki a kan wahayi daga Mahaliccinsa. Bai taba ayyana yaki ba matukar ya san akwai ragowar dama ta yin sulhu, kuma in har musulmi sun tsira daga kuntawa da farmakin abokan gaba.
Lokacin rayuwar Annabinmu (SAW), Yakin Mu'tah shine muni da kuma wahala a cikin yakukuwan da Musulmai suka gwabza. Ya nada Zaid ibn Harithah a matsayin jagoran rundunar sannan ya gabatar da jawabi ga dakarun cewa:
Ku yi yaki da sunan Allah, a tafrkin Allah, akan wadanda suka kafircewa Allah. Kada ku juya baya. Kada ku yanke kunnuwa da hanci da sauran sassan jiki. Kada ku kashe mata da yara, tsofaffi, da kuma masu bautar addini a dakunan bautarsu. Kada ku sare bishiyar dabino ko sauran bishiyoyi, haka kuma kada ku rushe gine gine. (Bukhari)
A bisa dokokin da Annabi (SAW) ya shimfida na yaki, musulmai masana sun fitar da wadannan ka'idoji, wadanda za a iya kiransu da "Ka'idojin Musulunci na Yaki":
Yarjejeniyar Madina, wadda Manzonmu ya sanyawa hannu tare da al'ummun Yahudawa da mushirikan da ke birnin, ita ma muhimmin al'amari ne na adalci da girmama juna tsakanin al'ummu daban daban. Yarjejeniyar wadda aka rubuta don samar da wani tsarin mulki a tsanin al'ummu mabambantan addinai da kuma baiwa kowace al'umma damar kiyaye ka'idojinta, ta samar da aminci da zaman lafiya ga wadanda a tsawon shekaru suka kasance magabtan juna.
Daya daga cikin abubuwa mafi burgewa da yarjejeniyar ta kunsa shine 'yancin addini. Sidira akan wannan tana cewa:
Yahudawan Banu Awf al'umma daya suke tare da musulmi; Yahudawa suna addininsu, Musulmai ma suna da nasu… (Tsarin Mulkin Madina, http://www.islamic-study.org/jews-prophet-p.-2.htm)
Sidira ta 16 ta yarjejeniyar tana cewa: "Duk Bayahuden day a bi mu to yana da tabbacin goyon bayanmu da kuma hakki daidai da kowannenmu. Ba za a cutar da shi bah aka nan ba za a taimaki makiyinsa akansa ba." Halifofin Annabi sun ci gaba da dabbaka wannan yarjejeniyar day a kulla, inda suka fadada ta har zuwa kan Buzaye, mabiya addinin Budda, mabiya addinin Hindu da kuma masu sauran addinai.
Wani dalili da ya sa zamanin Annabi (SAW) ke cike da aminci da tsaro shine matsayinsa na adalci, wanda yake daidai da koyarwar Alkur'ani. Su ma marubutan kasashen waje, madaukakan halayensa sun burge su inda suka jinjinawa dabi'un Ma'aikin a cikin rubuce rubucensu.
George Bernard Shaw ya bayyana wadannan madaukakan halaye a cikin littafinsa mai suna The Genuine Islam (Musuluncin Gaskiya):
Koda yaushe ina daukar addinin Muhammad da matukar kima saboda gaskiyar lamarinsa. Shi kadai addinin da a gani na yake da damar dacewa da yanayin canjin rukunin rayuwa wanda zai iya nuna kansa a kowane karni. Na yi nazarin sa… dole a kira shi da Mai ceton Mutane. Na yi imani cewa da mutum kamarsa zai karbi mulkin kama-karya na duniyar wannan zamani, da zai yi nasara wajen warware matsalolin ta ta hanyar da za a samar da zaman kafiya da farin cikin da ake matukar hankoro…" (Sir George Bernard Shaw a cikin 'The Genuine Islam,' 1936, http://www.geocities.com/Athens/Forum/9192 /mainquote2.html#shaw)
Haka ma a namu zamanin, rayuwa akan dabi'un Alkur'ani ita ce kadai maganin duk matsalolin rikice rikice, fadace fadace da kuma rashin zaman lafiya a duniya. Kamar Ma'aikinmu, mu ma ba za mu kauce daga tafarkin adalci ba, sannan kuma koda yaushe mu rika girmama hakkin al'ummu da daidaikun mutane daban daban, ba tare da bambance addini ko inda suka fito ba.
"Tawagar wakilan Kiristoci daga Najran sun zo Madina lokacin sallar azahar suka shiga Masallacin Annabi. Yayin da suka shigo a lokacin da Annabinmu (SAW) shi da mutanensa suke tsakiyar sallar azahar, sai Kiristocin suka juya gabas da nufin yin ibada. WASU DAGA CIKIN SAHABBAI SUN SO SU HANA SU, AMMA SAI ANNABI (SAW) YA YI UMARNI DA A KYALE SU SANNAN YA BA SU IZININ SU YI IBADARSU." (Tabari, ibn Kathir, Razi, Qurtubi; Alkur'an, 3: 1-61; Wani bangaren wadannan sharhi ya yi bayanin farkon surar, wasu kuma da aya ta 61, wadda aka sani da ayar mubahala). (Hamidullah, Annabin Musulunci, fassara: Salih Tug, Ankara 2003, 1,920; Saricam, Annabi Muhammad da Sakonsa na Diniya baki daya, 278.)
Kari kuma, a wasu riwayoyin an ce Annabinmu (SAW) ya halarci daurin aurensu, ya ziyarci marasa lafiyarsu, kuma ya kasance yana yi musu kyauta. ANNABI MUHAMMAD (SAW) HAR YA SHIMFIDA WA KIRISTOCIN NAJRAN WADANDA SUKA KAWO MASA ZIYARA MAYAFINSA DON SU ZAUNA AKAI.
A cikin yarjejeniyar da Ma'aiki (SAW) ya yi shifta aka rubuta, sidira zuwa ga Harris ibn Ka'ab, wanda Kirista ne, da kuma sauran Kiristoci: "ADDINI, WURAREN IBADA, RAYUKA, MUTUNCI DA KUMA KADARORIN GABA DAYAN KIRISTOCIN DA KE ZAUNE A GABAS DA YAMMA SUNA KARKASHIN KARIYAR ALLAH, DA MANZONSA DA KUMA DUKKAN MUMINAI. Babu wani daga cikin Kiristoci da za a tilastawa shiga musulunci. Idan aka yi wa wani daga cikin Kiristoci kisan gilla ko rashin adalci, to nmusulmai za su tashi su taimake shi," sai ya karanta ayar: "Kada ku yi jayayya da Ahlul Kitabi sai dai akan abin da yake mafi kyawu…" (Alkur'ani, sura ta 29, aya ta 46) (Ibn Hisham, Abu Muhammad, Abdul-Malik, (v.218/834), as-Seerat an-Nabaweeyat, Darut-Turasil Arabiyye, Beirut, 1396/1971, IV/241-242; Hamidullah, Al-Wasaiq, s.154-155, No.96-97; Dogu Bati kaynaklarinda birlikte yasama, "Living together in Eastern and Western sources, p.95)
A zamanin Ma'aikinmu (SAW) jakadu da wakila sun ziyarci Madina kungiya kungiya. Wasu lokutan wadannan kungiyoyi – da suka hada da Ahlul Kitabi – za su zauna har na sama da kwanaki a goma, inda har sai ya kasance cewa gidajen wadansu mutane kamar su Abdurrahman ibn Awf, Mughira ibn Sube, Abu Ayyub al-Ansari da Ansar an samar da su garesu. Kari akan wannan, akan shirya wani tanti da ke kusa da Masallaci, wanda Ahlus Suffa ke zama a cikinsa suna daukar darasi, don maziyartan. Ma'aikinmu (SAW) ya kan bayar da takardu (rubutattun ka'idoji da dokoki wadanda ke fayyace hakki da alfarmar da aka baiwa wasu rukunin jama'a da daidaikun mutgane yayin yarjejeniya da baki) da kuma rubutattun bayanan gwamnati da ke sanar da kasar da aka ware musu. Ya kan nada gwamnoni daga cikinsu zuwa wasu yankunan. Har ila yau, idan Annabin Allah (SAW ) zai aika jami'ai masu karbar zakka zuwa ga mawadata musulmai, ya kan kuma nada Kiristoci a matsayin jami'ai masu karbar haraji da Kiristoci 'yan uwansu. A gaskiya ma, wannan tawagar hukuma da ta zo shi ke nuna hujjar cewa gaba dayan Tsibirin Larabawa ya mika wuya ga annabta da jagorancin Annabi Muhammad (SAW). (Saricam, The Prophet Muhammad and His Universal Message, 356.)
A birnin Makka, Manzon Allah (SAW) ya kasance baya aiki da abin da maguzawan Makka suke yi a kan lamarin da ba shi da wahayi akai, INDA YA KAN YI AIKI DA ABIN DA AHLUL KITABI SU KE YI. (Bukhari, al-Libas 70; Muslim, al-Fada'il 90)
Kasar Kiristoci ta farko da ta dauki hankalin Manzo Allah (SAW) kafin hijira wadda kuma ya so musulmai su yi hijira zuwa cikinta it ace Habasha. Yayin da zalunci da azabtarwa daga maguzawan Makka suka kai makura, sai Annabi (SAW) ya nemi musulmai da su yi hijira daga Makka zuwa Habasha inda ya bayyana cewa: "Idan kun ga dama kuma kuna da hali, to ku nemi mafaka a Habasha. DOMIN BA A KUNTATAWA KOWA A KASAR SARKIN DA YA KE MULKI A CAN. WANNAN SHINE CIKAKKEN WURI MAI AMINCI. KU ZAUNA A CAN HAR LOKACIN DA ALLAH ZAI SAUKAKA ABUBUWA" (MuhammadHamidullah, al-Wasa'ik al-Siyasiyya, (fassarar Vecdi Akyuz), Kitabevi, Istanbul 1997, p.115; Hamidullah, The Prophet of Islam, 1,297.)
Jabir ibn Abdullah ya ruwaito cewa: An wuce da gawa ta gabanmu, sai Annabi (SAW) ya mike tsaye inda mu ma muka mike tsaye. Sai mu ka ce, "Ya Ma'aikin Allah! Wannan fa gawar Bayahude ce ake wucewa da ita". Sai ya ce, " Duk lokacin da ku ka ga ana wucewa da gawa, ku mike tsaye." (Sahih Bukari, Mujalladi na 2, Littafi na 23, Lamba ta 398)
Abdurrahman bin Abi Laila ya ruwaito cewa: Wata rana Sahl bin Hunaif da Qais bin Sad sun kasance suna zaune a cikin birnin Qadisiyya, sai aka wuce da gawa ta gabansu, sai suka mike tsaye. Sai aka shaida musu cewa gawar daya daga cikin mutanen garin ne, wato wanda ba musulmi ba, wanda ke karkashin kariyar musulmi.Sai suka ce "An wuce ta gaban Annabi (SAW) da gawa sai aka gay a mike. Yayin da aka gaya masa cewa makarar Bayahude ce, sai y ace, 'Shin ba mutum ba ne?' (Sahih Bukhari, Mujalladi na 2, Littafi na 23, Lamba ta 399)
… Sai Ma'aikin Allah ya dawo da Wahayi yayin da zuciyarsa take bugawa da karfi. Sai ya tafi zuwa ga Khadija bint Khuwailid … Sai Khadija tar aka shi zuwa wurin dan uwanta Waraqa bin Naufal bin Asad bin Abdul 'Uzza, wanda ya zama Kirista lokacin jahiliyya kuma ya kasance yana rubutu da haruffan yahudanci. Yakan rubuta abin da Allah yah ore masa rubutawa na daga Injila da haruffan yahudanci. … (Sahih Bukhari, Mujalladi na 1, Littafi na 1, Lamba ta 3)
Annabinmu (SAW) ya aikata ma'anar ayar La ikhraha fid deen "Babu tilas a cikin addin" (Alkur'ani, sura ta 2, aya ta 256) wadda ke nuni da 'yancin mutum na zaben addininsa, kuma a shekara ta 630 ya aika da wannan umarni ga jakadun sarkin Himyar don ya sanar da su cewa su Musulmai ne:
"Bayahude ko Kirista suna da hakkin doka daya da Muminai idan su musulmai ne. DUK WANDA YA SO YA CIGABA DA ZAMANSA A BAYAHUDE KO KIRISTA, BABU WANDA ZAI HANA(Ibn Hisham, as-Sira, II, 586
Daya daga cikin ka'idojin da Annabin Allah (SAW) ya gina dangantakarsa da mutane shine gaskiya. Kasancewar mutum mabiyin wani addini daban ba ya hana shi yin mu'amalar kasuwanci das hi matukar ya amince da gaskiyarsa. Shi da kansa ya karbi bashi da kayan abinci daga Yahudawan Madina.
Lokacin da Annabi (SAW) ya yi wafati, kadarorin da za a biya basukan da ya karba ne daga taskar makamai.
Daga cikin ganimar da aka samu a yaki Haibar akwai rubutacciyar Attaura a cikin takardu. Sai Annabi (SAW) ya ware wadannan takardu daga cikin ganimar inda ya bayar da umarnin mayar da su ga Yahudawan.
Haka kuma, bayan bude Haibar, an sami sojojin Musulmi sun fara cin dabino da sauran kayan lambu na Yahudawan. Sai Yahudawan suka kai kuka ga Annabi (SAW). Dagan nan sai Annabi (SAW) ya yi umarnin kada wanda ya taba kayan lambu da duk wani abu mallakar mutanen yankin.
Annabi Muhammad (SAW) ya baiwa Yahudawa damar shiga cikin masu tsara Tsarin Mulkin Madina wanda aka kulla yarjejeniya da kabilun Aws da Khazraj, wanda ya bas u damar ci gaba da rayuwa akan tsarin addininsu. An yi bayanin tushen tausayi da fahimtar da Musulmai suke da ita akan Yahudawa a cikin wannan sidira: "YAHUDAWAN BANU AWS ('YAN TSIRARU WADANDA BA MUSULMI BA) AL'UMMA CE TARE DA MUMINAI. YAHUDAWA SU YI ADDININSU, SU MA MUSULMI SU YI ADDINISU."
Yarjejeniyar Madina, wadda gaba daya Muhajirun (Musulmai da suka yi hijira daga Makka), Ansar (musulman Madina) da kuma Yahudawa suka sanya wa hannu, wani muhimmin misali ne na adalci. Wata sidira a wannan tsarin mulki tana cewa:
"Yahudawan Banu Awf al'umma daya suke tare da Musulmai; YAHUDAWA SUNA DA ADDININSU MUSULMI MA SUNA DA NASU…"
Sidira ta 16 a cikin yarjejeniyar tana cewa: "Yahudawan da suka bi mu tabbas sun cancanci goyon bayanmu da kuma dukkan hakukuwan da kowane dayanmu ya cancanta. Ba za a cutar da shi ko a taimaki makiyinsa akansa ba."
Sahabban Annabi (SAW) sun cigaba da dabbaka wannan sidira da ke cikin yarjejeniyar, hatta a bayan wafatinsa, haka kuma sun aiwatar das hi a kan Buzaye, mabiya Budda, mabiya Hindu da kuma sauran mabiya addinai.
Kyautatawar da Annabi (SAW) ya yi wa Ahlul Kitabi a garuruwan Adruh, Maqna, Khaibar, Najran da kuma Aqaba yana nuna cewa Musulmai sun baiwa wadannan wadanda ba musulmai ba tabbacin kariya ga rayuka da kadarorinsu da kuma bas u 'yancin addini da bauta. Akwai bukatar fito da wadannan sidirori na yarjejeniya tsakanin Annabinmu (SAW) da Kiristocin Najran:
"GA KIRISTOCIN NAJRAN DA MAKWABTAN KASASHE, SUNA DA KARIYAR UBANGIJI DA ALKAWARIN MANZONSA GA RAYUKANSU, ADDINISU, DA KUMA KADARORINSU – HAKA NAN GA WADANDA SUKE NAN DA KUMA WADANDA BA SA NAN DA KUMA WASU DABAN."
Babu wani malamin addini da za a fitar daga dakin bautarsa, ko wani mai ibada daga gidan ibadarsa, ko wani limamin addini daga limancinsa, sannan kuma za su cigaba da more duk wani abu babba da karami har zuwa yanzu… Ba za su yi zalunci ko a zalunce sub a. Duk wanda ya nemi hakkinsa daga gurinku, to za a tabbatar da adalci a tsakaninku. Babu dayanku da za a zalunta, haka nan ba za a bar ku ku zalunci wasu ba.
Yarjejeniyoyi da dama da aka kulla a lokacin Annabi (SAW0 sun bayar da wasu alfarma da hakkoki ga al'ummun Yahudawa da Kiristoci da suka ba su hakkin rayuwa. Alfarmar da aka yi ga masu bauta a St. Catherine Monastery a Dutsen Sinina duk misalai ne na wannan. Wadannan takardun yarjejeniyoyi sun bayar da Hakkokin doka, addini da kuma na zamantakewar rayuwa na Yahudawa da Kiristoci wadanda ke karkashin mulkin Musulmai ko kuma suka amince da ikon musulunci. An warware matsaloli ta hanayar amfani da wadannan takardu. Misali, littattafan tarihi sun bayyana cewa Kiristoci a Dimashka sun gabatar da takardun da ke dauke da alfarmar da aka bas u ga Halifa Umar yayin da suka sami wata matsala inda suka roke shi day a warware musu matsalar.
Adnan Oktar: Wannan ya samu ne daga bambancin fassara. Mutumin da ya zurfafa cikin Alkur'ani, wanda ya fahimci Alkur'ani sosai, wanda yake so da tsananin son biyayya ga Ubangiji, wannan shi za a iya cewa tsundum yake cikin soyayya. Yana son Allah kuma yana duban kowane abu da soyayya. Ba za taba fatan ya rusa, ya jefa bam ko ya dagargaza abu ba. Musulunci ya ginu ne akan jawo hankalin mutane. Za ka jawo hankalin mutum, in kuma ba ka yi ba, yana da damar cigaba da addinan day a ke yi. A bayyane yake cewa babu tilas a cikin addini. Idan ka tilastawa mutum ya shiga addini, zai zama munafuki ne. Munafuki shine mutumin da zai shiga wuta ta can kasa, mafi munin halitta. Shi ne mutumin da ya maida kansa injin da ke samar da munanan halittu. Don haka dole mu hori mutane su zama masu gaskiya. Idan bai bada gaskiya ba, to zai fadi gaskiya cewa bai bada gaskiya ba, kuma za a girmama ra'ayin wannan mutum. Ya kamata a girmama duk wani mutum, saboda haka Allah ya halicce su kuma wannan ne abin da aka rubuta musu. Ka gaya musu gaskiya, in mai fahimta ne zai fahimta, in kuma ba mai fahimta ba ne ba zai taba ganewa ba.
Dole ne mutum ya kare kansa yadda Annabinmu (SAW) ya yi, kamar yadda Allah ya fasalta a cikin Alkur'ani. Amma aje a jefa bam akan mata da yara abar su kwance cikin jini, wannan mummunan abu ne a ra'ayina, rashin gaskiya ne kuma tsabar hauka. Mugun aiki ne, ba wani abu ba. Wace irin nasara ce wannan a bar mata da yara kwance cikin jini? Ba komai ba ne face keta da rashin imani. Saboda yaki yana da dokokinsa. Ka daura yaki yayin da su ma daya bangaren suke yaki da kai.
Kasashe suna daura yaki ku kuma ku shiga yaki, sannan duk wanda Allah ya baiwa nasara ya yi galaba. Akan kama wadanda aka cinye da yaki su zama karkashin ikon daya bangaren. Bayan haka, ku kan kulla sulhu da daya bangaren don ku zauna lafiya, kuna kulla sulhu a matsayin kasa, amma in haka kawai ka ce na warware wannan sulhu kuma zan jefa muku bam, in jefa bam akan mata da yara, to wannan sabawa tunani ne, hankali, imani da kuma Alkur'ani a bayyane. Shin Annabinmu (SAW) irin haka ya yi? A'a. (Azerbaijan Ayna, 8 ga Agusta 2008)
Wadana suka zo da kyawawan ayyuka suna da mafi kyawun wannan… (27: 89)