KAMMALAWA: SHAWARA GA YAMMACIN DUNIYA DA KUMA MUSULMAI
A yau, kasashen yammaci sun damu kwarai da kungiyoyin da ke fakewa da musulunci suna aikata ta’addanci kuma wannan damuwa ba a kan kuskure ta ke ba. A bayyane yake cewa wadanda ke kaddamar da ta’addanci da magoya bayansa za a hukunta su ne kamar yadda ka’idat doka ta duniya ta tsara. Sai dai, wani muhimmin abu da za mu lura da shi shine tsarin ka’ida na tsawon lokaci da za a bi don gano naganin wadannan matsaloli.
Bayanan da suka gabata suna nuna cewa ta’addanci ba shi da gurbi a musulunci sannan kuma laifi ne da ake aikatawa akan bil-adama. Haka kuma suna kara nuna yanayin rashin daidaito da sabanin tsarin “Ta’addancin Musulunci.” Wannan ya samar mana da muhimmin abin dubawa:
- Lokaci mai zuwa a nan gaba yana bukatar duk kasashe su yi taka-tsantsam, kaffa kaffa da kuma hikima. Yanayin fid da kauna da ya zo da "Clash of Civilizations" (Arangamar Al'ummu), yana daya daga cikin abubuwan da ke hana hadin kan duniya, wanda ba mai amfana da shi. Al'ummar duniya gaba dayanta dole ne ta dauki damar koyon zama tare da juna cikin mu'amalar zaman lafiya, koyo daga juna, karantar tarihin juna, ayyukan addini, fasaha, adabi, falsafa, kimiyya, fasahar kere kere da al'adu, wadanda za su amfani rayuwar juna.
- Dole a yada yyukan da ke nuna Musulunci na gaskiya. "Tilasta tsarin rashin addini" ba shi ne hanyar yaki da kungiyoyin 'yan tsattsauran ra'ayi a kasashen musulmi ba. A maimakon haka, irin wannan tsari zai jawo maida martani daga talakawa. Maganin matsalar shine yada musuluncin gaskiya da kuma bayyanar misalin musulmi da ya rungumi koyarwar Alkur'ani kamar hakkin dan Adam, dimukradiyya, 'yanci, madaukakiyar dabi'a, kimiyya, addini, hikima da fasaha, da kuma abin da zai kawo farin ciki da ni'ima ga al'umma. Wajibin musulmai ne su yi bayanin kyawawan halaye da Alkur'ani ya kawo kuma Annabi Muhammad (SAW) ya aikata sannan su ma su tafiyar da rayuwarsu kan wannan tsari. Hakki ne akan musulmai da su karbe musulunci daga hannun wadanda suka yi masa gurguwar fahimta suke bata sunan addinin (wanda hakan ke kara sa wa a kasa fahimtar addinin), sannan su maido shi hannun wadanda ke bin koyarwar musulunci sawu da kafa, masu koyi da Ma'aikin Allah (SAW).
- Tushen ta'addanci ya damfaru ne da jahilci da rashin hakurin zama da mutane yayin da maganin matsalar shine ilimi. Ga wadanda ke goyon bayan 'yan ta'adda, za a yi musu bayanin cewa ta'addanci ya sabawa musulunci kuma cewa ta'addanci yana cutar da musuluncin, Musulmai da kuma mutanen duniya baki daya.
- Ya zama dole a kirkiro matakan gyara na al'ada na tsawon lokaci don yakar ta'addanci wanda tushensa ke cikin akidun gurguzu, farkisanci da wariyar launin fata. A yau a kasashe a fadin duniya, tsarin ra'ayin Darwiniyawa shine ginshiken tsarin ilimi. Sai dai, kamar yadda muka fada da farko, Darwiniyanci baudaddiyar akida ce da ke kallon mutum a matsalin dabba da ta bunkasa ta hanyar fada don rayuwa – wani abu da ya kunshi makamancin asalin duk wasu nau'o'i na ta'addanci. Akidar da hasashen cewa kawai masu rike da karfin mulki ne za su rayu sannan ta dauki yaki a matsayin kyakkyawan abu tamkar wani babban shuri ce da za ta cigaba da jawo wa duniya annoba. Tun da abin haka yake, ban da dokoki da sauran matakai da za a kafa don yakar ta'addanci, akwai kuma bukatar gagarumin aikin ilmantarwa da wayar da kai da za a kaddamar a fadin duniya. Tona asirin yaudarar da ke cikin Darwiniyanci da zahiranci da kuma koyarwa akan kyawawan dabi'un da Allah ya saukar ga mutane su za su kasance jiga jigan wannan ilimantarwa. Ana samun zaman lafiya da lumana ne ta hanyar rayuwa akan kyawawan dabi'un addinin gaskiya kadai. Idan ba a rushe shurin ba, to zai yi wuya a raba duniya da wannan annoba.
Fatanmu shine cewa wadannan matakai za su taimakawa duniya wajen ganin bayan ta’addanci da kuma duk turakun kiyayya, dabbanci da ta’addanci. Tun da kasar Amurka ta kira kanta da “kasa mai bin Ubangiji,” da kuma al’adar Kiristanci da ta ke wakilta, ya kamata ta kasance mai abota da zumunci da Musulmai. A cikin Alkur’ani, Allah yana jawo hankalinmu zuwa ga wannan lamari kuma Yana gaya mana cewa kiristoci su ne wadanda “suka fi nuna soyayya ga wadanda suka yi imani.” (Alkur’ani, sura ta 5, aya ta 82)
A tarihi, wasu jahilsn mutsne (misali, ‘Yan Salibiyya) sun kasa fahimtar wannan gaskiya inda suka yi ta haddasa rikici tsakanin wadannan addinai guda biyu. Don hana sake afkuwar irin wadannan al’amari, wanda ake yada shi da take irinsu “Arangamar Al’ummu” ko “Yakin Addini akan Yammaci,” akwai bukatar kiristoci da musulman gaskiya su hada kai da karfi wuri guda.
Hakika, abubuwan da suka faru bayan afkuwar wadannan munanan al’amura suna nuna cewa tun an tiga an dasa itaciyar wannan hadin kai. Wannan mummunan aiki na ta’addanci, wanda ya hada kan al’ummun kirista da na musulmai wuri guda, ya sanya kiristoci da dama sun gano ainihin addinin musulunci inda suka karfafi musulmai don su yi namijin kokari wajen bayyana kyawawan dabi’un musulunci na gaskiya wadanda Alkur’ani ya bayyana.
Duk wadannan abubuwa da ke faruwa bushara ne kan cewa mutane za su fahimci dabi’un musulunci sosai inda za su raba kansu da kiyayya da wariyar da suka dade a ransu. Da yardar Alla, karni na 21 zai zama lokaci ne da mutane za su yarda cewa yada koyarwar musulunci ita ce ingantacciyar hanyar cimma burin zaman lafiyar da aka dade ana hankoro a bayan kasa.
Shi ne Allah, Mai halitta, Mai ginawa, Mai surantawa. Yana da sunaye masu kyau, abin da ke a cikin sammai da kasa suna tsarkake Shi, kuma Shi ne mabuwayi, Mai hikima.
(Alkur'ani, sura ta 59, aya ta 24)