Duk wadannan misalai suna nuna cewa shirya ayyukan ta’addanci akan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ya sabawa Musulunci kuma abu ne mai wuya wani Musulmi ya aikata wannan laifi. Sabanin haka ma, hakkin Musulmai ne su hana wadannan mutane aikata wannan danyen aiki, wanda shi ne kauda “barna a bayan kasa” da kuma tabbatar da aminci da tsaro ga duk jinsin mutane a fadin duniya.
Abu ne da ba zai yiwu ba a rika maganar “Ta’addancin kiristanci,” “Ta’addanci musulunci” ko “Ta’addancin yahudanci.” Tabbas, in za a binciki asalin masu aikata wadannan ayyukan barna za san cewa wannan ta’addanci ba shi da alaka addini ba ne, kawai al’marin juyin rayuwa ne.
A ranar 12 ga Satumban 1204, 'Yan Salibiyyar suka shiga Istanbul wanda ke hannun 'yan uwansu kirista. Sun barnata birnin tare da wawashe arzikinsa abin da ya kai har sun kwashe gwalagwalai daga majami'u (coci). |
Kamar yadda aka bayyana a farko, masu mummunar fahimtar addini ko tsarin akida wani lokaci kan gurbata gaskiyar sakon addinin. ‘Yan Salibiyya, wadanda zamaninsu ya kasance bakin al’mari a tarihin Kiristanci, misali ne na irin wannan gurbatar addini.
‘Yan Salibiyya Kiristocin Turai ne wadanda suka daura yaki tun daga karshen karni na 11 da nufin sake karbo Kasa Mai tsarki (kasar Falasdinu da yankunanta) daga hannun musulmai. Sun fita ne wai da hadafin addini, amma duk kasar da suka shiga sai sun tarwatsa ta inda suka yi ta yada barna da razani a duk inda suka keta. A kan hanyarsu sun rika yi wa farar hula kisan kare-dangi suna rusa kauyuka da garuruwa. Randa suka kama birnin Kudus, inda musulmai, yahudawa da kiristoci suke zaune cikin aminci karkashin mulkin musulunci, ranar an ga malalar jini. Sun hallaka duk Musulmai da Yahudawan da ke cikin birnin ba tare da tausayi ba.
A cewar wani marubucin tarihi, “Sun kashe duk Sarasiyawa da Turkawan da suka samu… mace ko namiji.”15 Daya daga cikin ‘Yan Salibiyyar, Raymond na Aguiles, wanda abin ya faru akan idonsa, ya yi alfahari da wannan kisan kare-dangi:
An ga abubuwan burgewa. Wasu daga cikin dakarunmu (wadannan su ne suka fi sauran tausayi) sun datse kawunan abokan gabarsu; wasu sun harbe su da kibiyoyi, inda suka rika fadowa daga saman hasumiyoyi; wasu kuwa sun gana musu doguwar azaba ne ta hanyar wurga su cikin wuta. Za ka ga tarin kawuna, hannaye da kafafuwa ko'ina a kan titunan birnin. Ta kai dole sai mutum ya bi ta kan gawarwakin mutane da dokuna kafin ya sami hanyar wucewa. Amma duk wadannan ba komai ba ne in aka kwatanta su da abin da ya faru a Masallacin Annabi Sulaiman, wurin da aka saba gudanar da ayyukan addini … a cikin Masallacin da kuma farfajiyar Sulaiman, jini ya kai har guiwoyin dakaru da igiyar linzaman dawakansu. 16
A cikin kwanaki biyu sojojin Salibiyya sun hallaka wajen Musulmai 40,000 ta hanyar dabbancin da aka bayyana.17
Dabbancin ‘Yan Salibiyyar ya kai matuka, inda a lokacin Salibiyya Ta Hudu, sai da suka yi raga raga da birnin Istanbul, wanda garin Kiristoci ne, sannan suka sace abubuwan zinare daga coci coci.
Tabbas, duk wannan aikin dabbanci ya sabawa koyarwar addinin kirista. Addinin Kirista, kamar yadda Injila ta fada, “sako ne na soyayya.” An fada a cikin Injilar Matta cewa Annabi Isa (AS) ya ce da mabiyansa, “Ku nuna so ga makiyanku kuma ku yi addu’a ga wadanda ke zaluntar ku.” (Matta, 5: 44). An fada kuma a Injilar Luka cewa Annabi Isa (AS) ya ce, “Idan mutum ya mare ku a kunci daya, ku juya masa daya kuncin.” (Luka, 6: 29) Babu wani bangare a cikin Injila da aka halatta kisa; don haka kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba abu ne da ba a tsammani. Za ka iya samun maganar “kashe mutanen da ba su yi laifin komai ba” a cikin Injila; amma fa a labarin yunkurin da azzalumin Sarki Herod ya yi na kashe Annabi Isa (AS) tun yana dan jariri.
Idan addinin Kiristanci addini ne da ya ginu kan soyayya kuma babu ruwansa da ta’addanci, to ta ya ya Kiristoci ‘Yan Salibiyya suka aiwatar da wasu daga cikin mafi munin ayyukan ta’addanci a tarihi? Babban dalili a nan shine mafi yawa daga cikin ‘Yan Salibiyyar tsantsar jahilai ne wadanda za a iya kwatanta su da “ya-ku-bayi.” Wadannan talakawa, wadanda ba su san komai game da addininsu ba, wanda ma watakila ba su taba karantawa ko kuma ganin littafin Baibul a rayuwarsu ba balle su san kyawawan dabi’un da Baibul ke koyarwa, an ja su zuwa aikin dabbanci karkashin kirarin ‘Yan Salibiyya wanda ke nuna cewa suna yaki ne don “Addinin Allah.” Ta hanyar wannan yaudara da rudu aka ingiza dimbin mutane suka aikata mugayen ayyukan da Ubangiji ya haramta.
Yana da kyau a fadi cewa a wancan zamani, Kiristocin Gabas – misali, mutanen daular Byzantine – wadanda suka yi wa Kiristocin Yammacin Turai nisa ta fuskar al'ada da wayewa, sun nuna kyawawan dabi'un mutumtaka. Kafin da kuma bayan yakukuwan 'Yan Salibiyya, Kiristocin Gargajiya (othodox) sun yi zaman lafiya tare da musulmai. Kamar yadda wani mai sharhin BBC, Terry Jones, ya fada, bayan janjewar 'Yan Salibiyya daga Gabas ta Tsakiya, "an ci gaba da rayuwa irin ta wayewa da cigaba yayin da mabiya addinan tauhidi suka ci gaba da zama tare da juna."18
Misalin ‘Yan Salibiyya alama ce ta wani babban al’amari. Da zarar an sami mabiya wata akida cikin duhun kai, jahilai marasa ilimi, to akwai yiwuwar su fada harkar ta’addanci. Wannan kuma haka yake ga akidojin da babu ruwansu da addini. Duk kungiyoyin ‘yan gurguzu a fadin su ma ba su da maraba da tashe tashen hankula. Amma mafi tsananin ta’addanci da zubar da jini a cikinsu ita ce kungiyar Red Khmers a kasar Cambodia. Dalili kuwa shine sun fi kowa jahilci.
Kamar yadda jahilan mutane su ke iya kai duk wani ra’ayi mai kawo tashin hankali zuwa makurar hauka, haka kuma za su iya shigar da ta’addanci a Saukakkun Addinai, wadanada a fili yake ba sa shiri da ta’addanci. Haka nan misalan irin wannan sun faru a kasashen musulmai.
Kauyawa kabilun larabawa ne da ke zaune cikin hamada a zamanin Ma'aiki Muhammad (SAW). Saboda yanayi mai tsanani da suke zaune ciki, sai hakan ya yi tasiri akan al'adarsu. |
A zamanin Manzo Muhammad (SAW), akwai manyan tsarin zamantakewar rayuwa iri biyu a tsibirin Larabawa: Mazauna-Birni da kuma Kauyawa (Larabawan daji). A garuruwan Larabawa ana rayuwa bisa tsarin rayuwa da wayayyar al’ada. Huldar kasuwanci ta hada garuruwan da sauran kasashen duniya, wanda hakan ya taimaka sosai wajen wayewar kan Larabawan da ke zaune a birane. Sun kasance suna da kyawawan al’adu, sun kware a fannin adabi musamman bangaren wakoki. Su kuwa Larabawan Kauye, a daya hannun, sun kasance kabilun daji da ke rayuwarsu a cikin hamada, wadanda kuma da ke da koma-bayan al’ada. Ba abin da suka sani a ayyukan fasaha ko adabi, yayin mafi yawancinsu suka taso da dabi’un duhun kai.
Addinin musulunci ya taso ne kuma ya ginu a tsakanin mazauna birnin Makka, babban birnin wannan yanki. Amma kuma, yayin da musulunci ya yadu zuwa sauran sassan yankin, sai dukkan kabilun da ke Kasar Larabawa suka karbe shi. A cikin wadannan kabilu kuwa akwai larabawan kauye, wadanda aka sha fama da su; tasirin al’adar da suka taso a cikinta ya hana wasu daga cikinsu fahimtar kyakkyawar manufa da tsarin musulunci. Game da wannan Allah Yana cewa a cikin Alkur’ani:
Kauyawa ne mafi tsananin kafirci da munafinci, kuma su ne mafi kamanta ga rashin sanin haddodin abin da Allah Ya saukar ga ManzonSa. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima. (Alkur'ani, sura ta 9, aya ta 97)
Wasu daga cikin larabawan kauye wadanda su ke “mafi tsananin kafirci da munafunci” kuma wadanda suke daidai da sabawa dokokin Allah, suka shiga cikin al’ummar musulmai a lokacin rayuwar Manzo (SAW). Amma bayan wani lokaci, saboda kuskuren fahimta da kuma halayya, sai wasunsu suka kirkiro wasu kungiyoyi wadanda akidunsu suka ci karo da koyarwar musulunci.
Misalin wannan shine darikar da ta bayyana a tsakanin Kauyawa da ake kira “Kharijawa.” Babbar alamar wannan batacciyar darika (ana kiransu “kharijawa,” wato “’yan tawaye,” saboda sun kauce daga tafarkin sunni), shine tsattsauran ra’ayinsu na ga-ni-kashe-ni. “Kharijawa,” wadanda suka jahilci ainihin koyarwar musulunci ko kuma kyawawan dabi’u da halayyar Alkur’ani, sun kaddamar da yaki akan sauran musulmi wadanda ba sa ra’ayinsu inda suka halatta yakin ta kafa hujja da wasu ayoyin Alkur’ani da suka yi wa gurbataccen tawili. Bugu da kari, sun kaddamar da “ayyukan ta’addanci.” Su ne suka yi wa Sayyidina Ali (ra), wanda yake babban sahabin Manzon Allah ne kuma wanda aka bayyana da cewa shine “kofar birnin ilimi,” kisan gilla.
Daba bisani kuma, aka sami bayyanar wata muguwar kungiya mai suna “Hashashis.” Wannan kungiyar ‘yan ta’adda ce da ta kunshi jahilai da masu tsattsauran ra’ayi wadanda ba abin da suka sani na daga kyawun koyarwar musulunci wadanda kawai ake ruda da kirari da alkawuran karya.
Mutumin da ya kirkiro tsarin zaman-kara-zube na ‘yan ba-ruwanmu-da-doka na kasar Rasha, Michael Bakunin shi da almajirinsa Nechayev, sun fitar da siffar cikakken dan ta’adda kamar haka:
Michael Bakunin
Gaba dayan akin rayuwarsa (dan juyin-juya-hali), ba wai a magana ba kadai, har ma a aikace, yana kan yaki ne da tsarin al’umma da ake aiki da shi a yanzu, haka kuma da gaba dayan duniyar da take karyar wayewa da cigaba, tare da dokoki, dabi’u da al’adunta, shi makiyi ne marar sassauci… Kimiyya guda daya kawai ya sani; ita ce kimiyyar rusawa. (Jaridar The Alarm, mukala mai taken “Bakunin’s Ground-Work for the Social Revolution,” shafi na 8, 26 ga Disamba 1885)
Kamar yadda aka fahimta daga wadannan kalmomi na Bakunin da Nechayev, ‘yan ta’adda mutane ne da ke yanke dangantakarsu da duk wani tsarin addini da na rayuwa wanda sakamakon haka suka yi watsi da duk wani tsarin dabi’a, wadanda kuma suke kallon wadannan tsaruka a matsayin tarnaki ga na su shirin. Bakunin ya ci gaba da cewa, “Dare da rana ba shi (dan juyin-juya-halin) da tunani ban da tunani daya, manufa daya: kisan rashin imani; yayin da, a hankali kuma ba tare da hutu ba, ya ke bin wannan manufa, dole ne shi kansa ya shirya wa mutuwa a kowane lokaci sannan ya kasance a shirye yake ya kashe duk wanda ya nemi hana shi cimma manufarsa, da hannunsa.” A cikin rubutunsa, Ground-Work for the Social Revolution, akwai wannan fasali na irin mutumin da dan ta’adda zai zama:
Mai tsanantawa kansa sannan da tsanantawa wasu. Dole ne a danne duk wasu raunanan tunani game da dangantaka, abota, soyayya da godiya, ta hanyar kumajin aikin juyin-juya-hali. (Jaridar The Alarm, mukala mai taken "Bakunin's Ground-Work for the Social Revolution," shafi na 8, 26 ga Disamba 1885)
Wadannan kalmomi sun kwaye rufin bakar fuskar ta'addanci tare da nuna cewa ya yi hannun riga da addinin Musulunci wanda ya ginu akan zaman lafiya, jin kai da kuma soyayya. 20A wannan aya, Yana gaya mana cewa zaman lafiya da aminci shine hanyar tsirar bani-Adama sannan kuma aiki da kishiyar hakan, wato yaki da tashe tashen hankula, shiga hanyar shaidan ne:
Ya ku wadanda suka yi imani! Ku shiga cikin musulunci gaba daya; kuma kada ku bi zambiyoyin shaidan; lalle shi a gare ku makiyi ne, bayyananne. (Alkur'ani, sura ta 2, aya ta 208)
Abin nufi anan shine, kamar yadda ‘Yan Salibiyya suka gurbata tare da bata ma’anar addinin kirista suka maida shi addinin ta’annati, haka wasu batattun kungiyoyi da ke bullowa a kasashen musulmi suka yi wa musuluncin mummunar fahimta inda suka shiga aikata barna. Abin da ya hada wadannan kungiyoyi da kuma ‘Yan Salibiyya shine tsantsar jahilcinsu, duhun kai da bakar dabi’a, da kuma rashin sanin ainihin kkoyarwar addininsu. Rashin fahimtarsu ga addinin ita ce musabbabin ta’addancin da suke aikatawa, amma ba addinin da suke karyar aiki da shi ba.
Kwambar Tunanin Ta'addanci
Wata muhimmiyar siffar ‘yan ta’adda shine sukan yi aiki a ne a gamayya. A cikin wannan gamayya, ana watsi da zabi da daidaikun ra’ayi inda kowa ke fuskantar manufa daya kawai. Wadannan ke aiki cikin wannan gamayya kan iya yin abubuwan da ba za su taba yi a cikin hankalinsu ba yayin da suke aikata abubuwa ba tare da aiki da hankali ko hankalinsu ba. A kasashen duniya da dama kungiyoyin ‘yan ta’adda sun kunshi wadansu mutane kalilan marasa ilimi da kwakwalwa da suke samun kansu a rudu na son rai daga wuraren taro, kirari da wakoki, sannan ba tare da sanin abin da suke yi ba ko kuma saboda me suke yi, sai su shiga aikata barna da ta’annati. A lokaci guda irin wadannan mutane sukan iya zama ma-kasa da jini a hannayensu, har zukatansu su kekashe su zama cikakkun ‘yan ta’adda wadanda ke iya aikata munanan ayyukan barna. Ana iya ganin mutum shiru da alamar nutsuwa yayin da yake shi kadai, amma da zarar ya shiga kungiyar ‘yan ta’adda, zai iya aiwatar da kisa da sauran hare hare ba tare da wani kwakkwaran dalili ba. Wankin kwakwalwar da ake musu, tamkar sihiri, wanda ke sanya su rika fatan a kashe su akan manufarsu. Mafi yawan wadanda ke aikata ayyukan ta’adda yawanci za ka samu suna da raunin kuduri da tunani, inda suke zama tamkar garken dabbobi karkashin tasirin kwambar tunani. Ana naye gurbin hankali da zurfin tunani da tsananin kumaji da shauki da kuma karkata zuwa saurin afkawa da kisa. Irin wadannan mutane suna saurin hasala, ga keta da rashin bin doka.
Alkur’ani ya yi bayanin kuskuren wannan kwambar tunani inda yake cewa wajibi ne ga mutum ya yi aiki da hankali da ‘yancin tunaninsa:
Kuma kada ka bi abin da ba ka da ilimi game da shi, Lalle ne ji ga gani da zuciya, dukkan wadannan za a tambayi (mutum) a kansu. (Alkur'ani, sura ta 17, aya ta 36)
Wadannan misalai daga tarihi za su iya taimaka mana wajen samun kyakkyawar fahimta akan al’amarin da ke faruwa a halin yanzu, abin da a ke kira wai “Ta’addancin musulunci, wanda yau shine ya cika duniya. Wannan ya kasance ne saboda wadanda suke tasowa suna aikata ayyukan ta’addanci da sunan Musulunci da kuma wadanda suke goyon bayan wadannan ayyuka, wadanda ‘yan kalilan ne a cikin Musulmai, sun samo asali ne daga wannan “dabi’a ta kauyawa” da kuma akidun Darwiniyanci, zindikanci da zahiranci, amma ba daga musulunci ba. Saboda ba su fahimci ainihin sakon musulunci ba, wanda sako ne na zaman lafiya adalci, sai suka maida addinin wani makami na ayyukan dabbanci, wanda kuma wannan tasirin al’adu da tsarin rayuwarsu ne. Asalin wannan dabbanci, wanda za a iya kiransa da “Tsattauran Ra’ayin Kasashe Masu tasowa,” muguwar kirkira ce ta mutanen da ba su da darsashin kauna ga ‘yan uwansu mutane a cikin zukatansu.
Sanannen abu ne, a cikin karnonin da suka gabata, sojojin kasashen turai da kawayensu sun yi ta kuntatawa tare da kisan al’ummar Musulmai a ko’ina cikin sassan dukiya. Musulmai sun sha azaba da wuya a hannun wasu kasashen Turai masu tunani irin na mulkin mallaka, ‘yan mulkin mallakar cikin gida da ke samun goyon bayan wasu sojojin kasashen waje ko kuma azzaluman gwamnatocin kasashen su. Amma, ga Musulmai, wannan al’amari ne da za a dube shi ta mahangar Alkur’ani.
Babu ko’ina a cikin Alkur’ani inda Ubangiji Ya umarci musulmai da su rama ta’addanci da ta’addanci. A maimakon haka, Allah Yana umartar Musulmai da su “rama mugunta da alheri”:
Kuma kyautatawa ba ta daidaita, kuma haka munanawa. Ka tunkude cuta da abin da yake mafi kyau, sai ga shi wanda akwai kiyayya a tsakaninka da shi, kamar da shi majibinci ne, masoyi. (Alkur'ani, sura ta 41, aya ta 34)
Tabbas, damar musulmai ce ta su maida martani akan wannan zalunci. Sai dai kuma, kada martanin ya kasance bisa makauniyar gaba ko kiyayya ta rashin adalci. Allah Yana gargadi akan haka a ayar Alkur’ani mai zuwa:
… Kuma kada kiyayya da wasu mutane ta dauke ku, domin sun kange ku daga Masallaci Mai alfarma ga ku yi zalunci. Kuma ku taimaki juna a kan aikin kwarai da takawa. Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zalunci… (Alkur'ani, sura ta 5, aya ta 2)
Saboda haka, kaddamar da hare haren ta’addanci akan talakawan wasu kasashen da sunan “ana goyon bayan raunanan kashashe,” ya sabawa addinin musulunci.
Daya daga cikin Dabarun Ta'addanci Shine Cusa Tsoro da Razani a cikin Al'umma
Daya daga cikin muhimman alamomin ta'addanci shine ya kan zabi abubuwan da zai kai wa hari ba tare da bambancewa ba. Wannan hali na zabar abin da zai kai wa hari babu bambancewa daya ne daga cikin manyan dalilan cusa tsoro, tun da ba wanda ya ke da tabbacin ya tsira. Idan mutane suka san za a iya kai musu hari ba tare da dalili ba, to ba wanda zai ji cewa ya tsira daga 'yan ta'addar. Ba wani abu da wadanda aka nufa da hari za su iya yi don kare kansu, tun da 'yan ta'addar suna kai harinsu ne yadda suka ga dama, a kuma lokaci da wurin da suka ga dama. Don haka ayyukan ta'addanci a cikin al'umma ba su da ka'ida ko lokacin yin su.
Kungiyoyin 'yan ta'adda sukan kai hari ga wadanda suka nufa ba tare bambancewa ba, wanda hakan ke nuna ana kashe mutanen da ba ruwansu ko a raunata su. Misali a nan shi ne harin sinadari mai kashe laka da aka kai a tashar jirgi mai tafiya karkashin kasa ta birnin Tokyo a ranar 20 ga Maris, 1995.
Wani abin da ya kamata mu ambace shi anan shine cewa ba za a dora laifin kashe kashen da zaluncin da aka yi wa musulmai akan duk kasashen Turai da al’ummunsu ba. A hakikanin gaskiya, akidun zahiranci da falsafar zindikai marasa addini wadanda suka yi tashe a karni na 19 su ne asalin wannan barna.Ba daga addinin kirista tsarin mulkin mallaka na Turawa ya samo asali ba. Sabanin haka, kungiyoyin kin-addini wadanda ke yaki da tsarin kiristanci su suka assasa tsarin mulkin mallaka. Akidar tsarin rayuwa ta Darwiniyanci ta taka muhimmiyar rawa cikin ayyukan ta’addancin da suka faru a karni na 19. A yau a yankin kasashen yammacin turai, akwai ragowar mugayen akidu da ra’ayoyi masu hatsarin gaske, kamar yadda yake kuma akwai mutane masu al’adun zaman lafiya da ke da tushe da addinin kirista. A gaskiya ma, asalin rigimar ba tsakanin Yammacin Turai da Musulunci ba ne. Sabanin abin da mafi yawan mutane suke dauka, rigimar tsakanin mutanen kirki na Yammacin Turai da kuma Musulmai ne a bangare daya, da kuma masu gaba da addini (‘yan zahiranci, zindikai, Darwiniyawa da sauransu) a daya bangaren.
Wata alamar da take nuna cewa Tsattsauran Ra’ayin Kasashe Masu tasowa ba shi da alaka da musulunci shine cewa, ban da ‘yan shekarun nan, ana daukar wannan ra’ayi a matsayin bangaren akidar gurguzu. Kamar yadda kowa ya sani, kungiyoyin ‘yan gurguzu, da ke samun goyon bayan jamhuriyar Soviet, sun kaddamar da ayyukan ta’addanci akan kasashen Yammacin Turai a shekarun 1960 da na 1970. Yayin da tasirin akidar gurguzu ya zagwanye, sai wasu daga cikin tsarukan rayuwar da suka haifar da kungiyoyin ‘yan gurguzu suka juyo kan musulunci. Wannan “ta’addanci da ake gabatar da shi da sunan addini,” wanda aka gina shi da hadakar wasu ka’idoji da alamomin musulunci a cikin tsohon adabin tsarin gurguzu, gaba daya ya yi hannun riga da kyawawan dabi’u wadanda su ne suka gina tsarin musulunci.
Maganar karshe akan wannan mas’ala ita ce, Musulunci ba addinin wata kasa ko yanki ba ne. Sabanin yadda mafi yawan mutane a Yammacin Turai suka dauka, Musulunci ba “al’adar gabashin duniya” ba ce. Musulunci shi ne addinin karshe da aka saukar ga mutane a matsayin jagora zuwa tafarkin gaskiya wanda kuma ke kai sakonsa ga dukkan mutanen dukiya. Hakki ne akan musulmai da su isar da ciakken sakon musulunci wanda suka yi imani da shi ga mutanen duniya baki daya don su kusanto da su ga musulunci.
Saboda haka, akwai hanya daya da za a yi maganin mutane da kungiyoyin da suke fadawa harkar ta’addanci da sunan musulunci, suke kafa gwamnatocin zalunci sannan suke maida duniyar nan wurin tashin hankali da ban tsoro a maimakon kawata ta: ita ce ta bayyanar da kyakkyawan tsarin dabi’a na musulunci sannan da isar da shi don jama’a su fahimta kuma su yi aiki da shi.
Adnan Oktar: Tabbas musulmi zai kasance mai nutsuwa, mai zurfin tunani, mai yin afuwa da yafe laifi, mai son jama'a, mai jibintar lamarin wadanda ke tare da shi, wanda ke kokarin kyautata musu, mai tsafta da tarbiyyar hali wanda ke tsaftace muhallinsa. A cikin gida kuma, yana kawata gidansa. Yana kokarin ganin ya kula da jikinsa, da kuma gyara gashi da tufafinsa, mai daddadar magana, mai fara'a da sakin fuska, mai dadin murya, wanda gidansa ke cike da annashuwa, ga lafiyayyen abinci da wakoki, mai tsara komai da komai. Saboda ruhin mai imani yana ta kiran "Aljanna! Aljanna!" Yana bukatar ta. Kuma yana kokarin neman ta a nan duniya. Yayin da mai imani ya so samun wannan, Allah ya kan sanya ko'ina ya zama aljanna gareshi. Manufar musulmi ita ce cikar kamala a koda yaushe. Takalmansa, ga misali, za su kasance a goge suna kyalli. Ba za ka ga kura ko datti akansu ba. Ba za ka ga kasa a wandonsa ba; safarsa fes fes, hakoransa suna sheki. Baki, hanci da kunnuwansa kuwa kullum suna tsaftace. Gashin kansa yana sheki abin sha'awa. Turaren da ya sanyawa za ka ji shi mai dadin kamshi. Ba za ka ji shi yana bugar da kai ba. Amma babban abu mafi muhimmanci shine masu imani su nuna son juna yayin da suka fito waje. Yana garesu su ji dadi a ransu yayin da suka yi duba ga junansu. Wannan ita ce manufa. Sai dai, tabbas, wannan zai faru ne lokacin da Mahdi (AS) ya bayyana. Ban cika ganin wannan yanzu ba, sai dai jefi jefi. Amma wannan zai yi karfi ya yawaita a Karshen Duniya, zamanin bayyanar Mahdi (AS), insha Allah. (Gidan talbijin na Cay, 4 ga Maris 2009)
Akwai wani ra’ayi da dole mu yi nazarinsa tare da ta’addanci; wannan shine al’amarin tsattsauran ra’ayi.
Tsattsauran ra’ayi yana nufin goyon bayan canje canjen tashin hankali na juyin-juya-hali a kowane bigire tare da daukar tsauraran ka’idoji marasa sassauci don tabbatar da wadannan canje canje. Ana gane masu tsattsauran ra’ayi ta hankoran neman canji na juyin-juya-hali da kuma zazzafan ra’ayin tursasawa da suke da shi.
A cikin wannan, kamar yadda yake a kowane bigiren rayuwa, jagoran musulmai shi ne Alkur’ani da kuma rayuwar Manzonmu Muhammad (SAW). Idan muka kalli tsattsauran ra’ayi ta mahangar Alkur’ani, za mu ga cewa ba shi da dangantaka da yadda Allah ya umarci masu imani su tafiyar da rayuwarsu. Duk lokacin da Allah ya ke yin bayanin mai imani a cikin Alkur’ani, Yana fasalta shi ne a matsayin mutum mai son jama’a, mai saukin magana, wanda ba ya son musu da rikici, wanda ke isar da abota har ga mutane masu bakin rai da gaba.
Wani misali da zai yi mana jagora a cikin wannan al'amari shine umarnin da Ubangiji ya maiwa Annabi Musa (AS) da Annabi Haruna (AS) cewa su je ga Fir'auna su fada masa sassanyar magana:
Ku tafi ku biyu zuwa ga Fir'auna. Lalle shi ya ketare haddi (ga girman kai). Sai ku gaya masa magana laushi, ko zai tuna ko kuwa ya ji tsoro. (Alkur'ani, sura ta 20, aya ta 43-44)
Fir’auna ya kasance daya daga cikin mugayen kafirai masu girman kai a lokacinsa. Ya kasance azzalumin shugaba wanda ya kaficewa Ubangiji inda ya rungumi bautar gumaka saboda jahilci; bugu da kari, ya ganawa wadanda suka yi imani (Bani-Isra’ila na lokacin) mummunar azaba da kisa. Amma duk da haka Allah ya umarci annabawanSa su je gurin wannan azzalumin mutum su yi masa magana sassanya.
Za ku lura cewa hanyar da Allah ya nuna ita ce hanyar tattaunawa cikin kyakkyawar mu’amala, amma ba ta rikici tare da zafafan kalmomi, kirarin fushi da nuna rashin amincewa ta wuce-gona-da-iri ba.
Akwai wasu sauran misalan da za su nuna wa musulmai irin halayyar da ake so su yi a cikin muhawarar Annabi Shu'aib (AS) da kafiran lokacinsa. Alkur'ani ya kawo wannan muhawara kamar haka:
Kuma zuwa ga Madyana mun aika dan uwansu Shu'aibu. Ya ce, "Ya mutanena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautawa face Shi, kuma kada ku rage mudu da sikeli. Lalle ni, ina ganinku da wadata. Kuma lalle ina ji muku tsoron azabar yini mai kewayewa. Ya mutanena! Ku cika mudu da sikeli da adalci, kuma kada ku nakasta wa mutane kayansu, kuma kada ku yi barna a cikin kasa kuna masu fasadi. Falalar Allah mai wanzuwa ita ce mafi alheri a gare ku idan kun kasance muminai, kuma ni ba mai tsaro ne a kanku ba." Suka ce, "Ya Shu'aibu! Shin sallarka ce take umartar ka da mu bar abin da iyayenmu suke bautawa, ko kuwa mu bar aikata abin da muke so a cikin dukiyoyinmu? Lalle kai mai hakuri ne, shiryayye!" Ya ce, "Ya mutanena! Mu kuke gani, idan na kasance a kan hujja bayyananniya daga Ubangijina, kuma Ya azurta ni da arziki mai kyawu daga gare Shi? Kuma ba ni nufin in saba muku zuwa ga abin da nake hana ku daga gare shi. Ba ni nufin komai face gyara, gwargwadon iyawa ta. Kuma muwafakata tana ga Allah. Gare Shi na dogara, kuma zuwa gare Shi na wakkala. (Alkur'ani, sura 11, aya ta 84-88)
Allah Yana umartarku da ku mayar da amanoni zuwa ga masu su, kuma idan za ku yi hukunci a tsakanin mutane, ku yi hukunci da adalci. Madalla da abin da Allah yake yi muku wa'azi da shi. Allah Mai ji ne, Mai gani.
(Alkur'ani, sura ta 4, aya ta 58)
Idan muka duba abin da Annabi Shu’aibu (SAW) ya fada, za mu ga cewa ya yi kiran mutane da su yi imani da Allah kuma su yi aiki da madaukakan dabi’un rayuwa inda ya yi hakan ne cikin kaskantar da kai da kyakkyawar mu’amala. Za mu iya bayanin wasu daga cikin dalilan abubuwan da aka fada a wadannan ayoyi:
Lokacin da Annabi Shu'aibu ya ce da mutanensa "Ni ban zama mai tsaro akan ku ba," ba ya son ya nuna yana da iko akansu ne; nufinsa kawai ya isar musu da sakon gaskiya da Allah ya saukar.
"Lalle kai mai hakuri ne, shiryayye!"": Wadannan kalmomi na kafirai ga Annabi Shu'aibu suna nuna saukin kai da sanyin halinsa ne wanda har su kafiran suka tabbatar.
"Ya mutanena! Me ku ke gani?" Wannan salon zance da Annabi Shu'aibu ya yi amfani da shi yana nuna cewa yana kira ne ga kafiran da su yi aiki da tunani da hankalinsu. Ma'ana, bai yi amfani da salon tilastawa ba, amma sai ya tuhumi ra'ayinsu ta fuskar muhawara inda ya nemi da su yi amfani da kwakwalensu don su yanke hukunci akan abin da yake fada musu.
"Kuma ba ni nufin in saba muku zuwa ga abin da nake hana ku daga gare shi." Hanin Annabi Shu'aibu a nan ba hakikanin hani ba ne. Ya yi bayanin cewa wasu ayyukan da suke yi zunubi ne inda ya yi kira garesu da su bar aikata su. Bugu da kari, lokacin da Annabi Shu'aibu ya ce "Ba na nufin in saba muku," ba nufinsa ba ne ya yi jayayya da mutanen sa; ba ya son ya sa su ji sun takura wanda hakan zai iya harzuka su; nufinsa kawai ya kira su zuwa yin imani da Allah da aikata kyawawan dabi'u.
Idan ku ka yi nazarin Alkur’ani za ku ga cewa gaba dayan Annabawan Allah sun yi tarayya akan dabi’ar saukin kai, jin kai da kuma sanyin zuciya. Ubangiji yana fada mana cewa Annabi Ibrahim (AS) ya kasance “mai yawan addu’a ne, Mai hakuri.” (Alkur’ani, sura ta 9, aya ta 114)kuma a wata ayar, an bayyana dabi’a da halayyar Annabi Muhammad (SAW) kamat haka:
Saboda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma da ka kasance mai fushi, mai kaushin zuciya, da sun watse daga gefenka. Sai ka yafe musu laifinsu, kuma ka nema musu gafara, kuma ka yi shawara da su a cikin al'amarin. Sannan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to ka dogara ga Allah, lalle ne Allah Yana son masu tawakkali. (Alkur'ani, sura ta 3, aya ta 159)
Babbar alamar ra’ayin tsattsauran ra’ayi ita ce fushi da saurin hasala. Za a iya ganin wannan halayyar a maganganu, rubuce rubuce da kuma zanga-zangar masu tsattsauran ra’ayi. Sai dai kuma, fushi ba ya cikin halayyar Musulmai. Yayin da Allah ke bayin masu imani a cikin Alkur’ani, ya yi bayanin “Wadanda suke ciyarwa a cikin sauki da tsanani, kuma suke masu hadiyewar fushi, kuma masu yafe wa mutane laifi. Allah Yana son masu kyautatawa. (Alkur’ani, sura ta 3, aya ta 134)
There is no situation in which a Muslim displays anger. The only thing a Muslim wants from other people is that they believe in Allah and live according to moral principles, but this is possible only by the grace of Allah. No matter what we do, no matter how much we try to explain the truth to people, human hearts are in Allah's hands. Allah reminds Muslims of this very important fact in this verse, "... Do those who believe not know that if Allah had wanted to He could have guided all mankind? ..." (Surat ar-Ra'd, 31)
Babu wani hali da zai sa musulmi bayyana fushi. Tabbas, duk wani musulmi yana da burin ganin sauran mutane sun yi imani da Allah kuma sun gudanar da rayuwarsu akan kyakkyawar dabi’a, to amma wannan nufin Allah. Duk abin da mu ke yi, duk iya kokarinmu wajen yi mutane wa’azin gaskiya, Allah ne kadai Ke sarrafa zukatan mutane. Allah yana tunatar da musulmai game da hakan a cikin wannan aya, “Shin wadanda suka yi imani ba su yi tsammani ba cewa, da Allah ya so, da Ya shiryar da mutane gaba daya? …” (Alkur’ani, sura ta 13, aya ta 31) Akwai kuma wata ayar da ta ke jaddadanw wannan magana:
Kuma da Ubangijinka Ya so, da wadanda suke a cikin kasa sun yi imani dukkansu gaba daya. Shin, kai kana tilasta mutane ne har sai sun kasance masu imani? (Alkur'ani, sura ta 10, aya ta 99)
Saboda haka, aikin musulmi ne ya yi bayanin wannan ga mutane sannan ya kira su zuwa yin aiki da su. Amma karba ko rashin karbar gaskiyarnwannan ya rage ga tunanin su mutanen. Allah ya tabbatar da wannan a Alkur’ani a inda ya ke cewa babu dole a cikin addini.
Babu tilastawa a cikin addini, hakika shiriya ta bayyana daga bata: Wanda ya kafirta da Dagutu kuma ya yi imani da Allah, to hakika, ya yi riko da igiya amintacciya, babu yankewa a gare ta. Allah Mai ji ne, Masani. (Alkur'ani, sura ta 2, aya ta 256)
Saboda haka, babu inda aka ce a yi amfani da karfi don sanya mutane su karbi musulunci, ko kuma a sanya musulmai yin sallah ko hana su aikata zunubi. Shawara da jan hankali kawai a yarda a yi. Allah yana fada a cikin wasu inda Yake magana da Manzon Allah (SAW) cewa musulmai ba sa zalunci:
Mu ne mafi sani game da abin da suke fadi, kuma ba za ka zama mai tilasta su ba. Saboda haka ka tunatar game da Alkur'ani ga wanda ke tsoron kyacewaTa. (Alkur'ani, sura ta 50, aya ta 45)
Ka ce, "Ya ku mutane! Lalle ne gaskiya ta zo muku daga Ubangijinku. To, wanda ya shiryu, ya shiryu ne domin kansa kawai, kuma wanda ya bace yana bacewa ne a kansa kawai. Kuma ni ban zama wakili a kanku ba." (Alkur'ani, sura ta 10, aya ta 108)
Ga 'yan ta'adda, kisan mutane da haddasa barna da ta'asa wani bangaren rayuwa ne a gurinsu. Da niyya suke zubar da jini. Sukan harbe mutanen da ba ruwansu, su jefa bam akan yara ko su tarwatsa gida da bam ba tare da jin tausayi a ransu ba. |
Hakkin musulmai kawai shine su yi wa mutane bayanin koyarwar addini, ba a ce su matsanta ko amfani da karfi a kan kowa ba kuma an hore su da su tausasa magana hatta ga manyan kafirai masu girman kai. Irin wadannan mutane ba za a kira su da 'yan tsattsauran ra'ayi ba, ssaboda tsattsauran ra'ayi kishiyar wadannan kyawawan halaye ne da aka lissafa. Kwarai kuwa, tsattsauran ra'ayi wani tsarin tunani ne da kuma ra'ayin siyasa da ya sabawa musulunci wanda kuma ya zo wa musulunci daga waje. Idan muka yi nazarin al'amarin rayuwa da aka bayyana ta bangaren tsattsauran ra'ayi, za a ga cewa kawai wadansu tsarin dabaru da kuma jawabai da 'yan gurguzu ke amfani da su, ko kuma nuna "zafin tsattsauran ra'ayi" wanda ba shi da alaka da musulunci na gaskiya. (Alkur'ani, sura 48, aya 26)
Wajibi ne ga dukkan musulmai su yi watsi da dabi’ar fushi da musu marar amfani wanda ya sabawa ainihin koyarwar Al’kur’ani sannan su maye gurbinta da dabi’ar nuna abota, saukin kai, soyayya da jin kai. Hakkin musulmai ne da su nunawa duniya misali don su birge kowa da dattakonsu, tausayi, saukin hali, kunya da son zaman lafiya. Dole ne ga musulmai su nuna tsatsar musulunci a hali da mu’amalarsu sannan su koyawa duniya kyakkyawar dabi’ar musulunci, ba kawai a cikin wadannan abubuwa ba, haka nan har da kokarinsu a fannonin kimiyya, al’ada, fasaha, da kuma tsarin zamantakewa da sauransu.
A cikin abubuwan da muka lissafa a sama akwai isar da musulunci ga sauran mutane da kuma kare addinin daga tasirin akidun da suka saba masa. A aya ta kasa, Allah Yana bayani karara kan irin halayyar da musulmi zai nuna yayin mu’amala da sauran mutane:
Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa'azi mai kyau kuma ka yi jayayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya bace daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga masu shiryuwa. (Alkur'ani, sura ta 16, aya ta 125)
'Yan ta'adda sun dauki ayyukansu na barna a matsayin hanyar farfaganda ; fatansu su sanya tsoro ta hanyar kashe mutane da barnata dukiyoyi. |
Tsarin ta’addanci yana faffadar ma’ana a harshen wannan zamani. A gaba daya yana nufin rikicin makamai da kungiyoyin masu akidar tsattsauran ra’ayi suke aikatawa. A dunkule, ta’addanci yana nufin tursasawa. Amma wannan matsantawar ta kunshi faffadan sarari da ya hada da baki dayan rayuwakan mutanen da tsananin barazanar tsoro da kashe kashe ta shafa. Ta’addanci ya hada da tsananin tursasawa wadda aka shirya ta da nufin sanya mutane daukar wata hanyar tunani da halayya, haka nan kuma da kowane irin nau’in aikin ta’addanci da aka kaddamar da niyyar tursasawa. Amma a kowane hali, wadanda ta’addanci yake karewa a kansu kai tsaye ko a fakaice sune talakawa.
Kungiyoyin ‘yan ta’adda suna yin amfani da ta’addanci ne don samun goyon baya. Suna amfani da tursasawa ne don su kara karfinsu domin kuma su sami goyon bayan wasu ko na gaba dayan talakawan.
Abin da mutane suke fara tunawa yayin da muka ambaci kalmar “ta’adda” shine nau’in taddanci da aka sani da “ta’addancin ‘yan ra’ayin rikau,” sai dai kuma akwai wani nau’in ta’addanci da ake samu a yankin Kasashe Masu tasowa wanda kuma gwamnatocin kama-karya suke aikatawa. A hakikanin gaskiya lamarin a nan ba wani abu ba ne da ya wuce aiwatar da badarun ta’addancin ‘yan ra’ayin rikau. Shugaban kama-karya ko kungiyar da ke kan mulki suna zalunci ne ta hanyar amfani da karfin mulkinsu don biyan bukatun kansu kadai, wanda sakamakon haka suke fuskantar nau’o’in adawa daban daban. A irin wannan hali, gwamnatin kama-karyar ta kan yi amfani da hanya guda don ta nuna cewa ta fi karfin masu adawa da ita; su kan kaddamar da ta’addanci don tsoratar da talakawa sannan kuma su tabbatar da karfin mulkinsu.
Su kuma kungiyoyin ‘yan ta’adda, a daya bangaren, ta yin biyayya da akidun da suke karewa, sukan yi ikrarin cewa manufarsu ita ce kifar da gwamnati da shugabanninta wadanda suke ganin haramtattu ne kuma azzalumai, sannan wai ta yin haka ne za su cimma burinsu na aiwatar da tsarin rayuwa mai adalci da walwala. Sai dai kuma, wannan ba ne mai yiwuwa ba. A cikin Alkur’ani, a cikin ayoyin farko na Suratul Bakara, Allah yana sanar da masu irin wannan tunani:
Kuma idan aka ce musu: "Kada ku yi barna a cikin kasa," sukan ce: "Mu masu kyautatawa ne kawai!" To lalle su, su ne masu barna, sai dai kuma ba su sani ba. (Alkur'ani, sura ta 2, aya ta 11-12)
A koyarwar Alkur'ani, laifi ne mai girma a kashe mutumin da b ashi da laifin komai. Allah Ya haramta ayyukan ta'addanci kuma Ya la'anci wadanda ke yin su. |
Ga ‘yan ta’adda, daukar rayukan mutane abu ne da ya zama jiki a garesu. Sukan iya harbe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba sannan su wurga bam akan kananan yara. Zubar da jini ya zamar musu abin nishadi. Rayuwarsu ta canja daga ta mutane ta koma ta mugayen dabbobi. In aka sami wani a cikinsu da yake da dan ragowar tausayi tare da shi, sunan kira shi da matsoraci ko ma-ci-amana inda suke rage masa matsayi a cikinsu. A lokuta sukan bude wa junansu wuta da kuma kisan kare-dangi akan bangaren da suka sami sabani a cikin kungiyarsu.
Kamar yadda za a iya gani, ta’addanci ba wani abu ba neda wuce hanyar zubar da jini ta shaidan. Duk wanda yake goyon bayan wannan aiki na dabbanci yana kare tsarin shaidan ne kawai. Kada kowa ya rudu don dan ta’adda ya yi amfani da yare da alamomin addini. ‘yan ta’addan da ke fakewa da rigar addini laifukansu guda biyu ne; na jinin da suka zubar da kuma bata sunan addini da suke yi yayin da suke aikata wadannan laifuka da sunan addini.
... Allah'tan korkup-sakının. Şüphesiz Allah, yapmakta olduklarınızdan haberi olandır.
(Maide Suresi, 8)
Ta’addanci da addini ba sa gamuwa. Ta’addanci na amfani da hanyar nuna karfi, kisa, rikici, mugunta da kuntatawa. Sai dai kamar yadda Alkur’ani ya ke cewa, duk wadannan abubuwan bangare ne na zalunci. Allah Yana umarni da tabbatar da aminci, zaman lafiya, kyakkyawan fata da kuma sassauci. Ya haramta ta’addanci da duk wani nau’in aiki da ba ya kawo zaman lafiya, sannan ya la’anci wadanda suke aikata wadannan ayyuka:
Kuma wadanda suka warware alkawarin Allah bayan sun kulla shi, kuma suke yanke abin da Allah Ya yi umarni don a sadar da shi kuma suna barna a cikin kasa. Wadancan suna da wata la'ana, kuma suna da munin gida. (Alkur'ani, sura ta 13, aya ta 25)
Acts of Violence-One of the Most Important Methods of Terrorist Propoganda
Terrorists regard acts of violence as propaganda for their organisations. For them, killing innocent people, robbing banks, assassinating people, kidnapping and planting bombs all act as propaganda for their struggle. To the terrorist who is bent on wreaking disorder, what publicity a single act of violence can generate in one day is much more publicity than what millions of brochures could do.
This idea is totally foreign to every kind of human feeling of compassion, mercy, concord and affection; it is alien to the moral teaching of the Qur'an and can gain a following only in those societies in which anti-religious ideologies hold sway. For this reason, the only possible solution that can save humanity from this benighted way of thinking is the widespread acceptance of the moral teachings found in the Qur'an and taken as a way of life.
Terrorists see their destructive acts as a means of propaganda; they hope to spread fear by destroying people and property.
Siffa daya da ta’addanci da kuma wadanda suka kamu da muguwar annobarsa suka yi tarayya a ciki ita ce ta rashin tsoro da son Allah a tare da su. Zukatansu sun riga sun bushe don ciwo ya shige su. Allah yana maganar halayyar irin wadannan mutane a cikin Alkur’ani:
Kada ka bi duk mai yawan rantsuwa, wulakantacce. Mai zunde, mai yawo da gulma. Mai hana alheri, mai zalunci, zunubi. Mai girman kai, bayan haka kuma la'imi (ba ya son alheri). (Alkur'ani, sura ta 68, aya ta 10-13)
Allah ya haramta yin tawaye marar dalili da kuma aikata ta’addanci. A musulunci, an haramta irin wadannan ayyuka na ta’addanci da rashin bin doka da muke gani a wannan zamani. Alkur’ani yana cewa:
Ka ce: "Ubangijina Ya hana abubuwan alfasha: abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya boyu, da zunubi, da rarraba jama'a ba da wani hakki ba, kuma da ku yi shirka da Allah ga abin da bai saukar da wani dalili gare shi ba, kuma da ku fadi abin da ba ku sani ba ga Allah." (Alkur'ani, sura ta 7, aya ta 33)
Allah calls to the Abode of Peace and He guides whom He wills to a straight path.
(Surah Yunus, 25)
'Yan ta'adda sun dauki ayyukan ta'addanci a matsayin farfagandar kungiyoyinsu. A gurinsu, kisan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, fashin banki, yi wa muhimman mutane kisan gilla, sace mutane da kuma dana bamabamai duk a matsayin farfaganda suke ga gwagwarmayar su. Ga dan ta'addan da ke hankoron haddasa yamutsi, daga sunansa da harin ta'addanci daya zai iya yi a rana guda na watsuwar labari ya fi wanda miliyoyin littattafai za su yi.
Kwata kwata wannan bakon ra'ayi ne ga duk wani nau'in halayyar mutum ta tausayi, jin kai, zaman lafiya da son juna; ya sabawa dabi'ar da Alkur'ani ya ke koyarwa kuma ba inda zai sami magoya baya face a cikin al'ummun da akidun kin addini suka yi tasiri. Saboda wannan dalili, hanyar mafita kawai wadda za ta tsirar da mutane daga wannan baudaddiyar hanya tunani shine rungumar koyarwar Alkur'ani da kuma dabbaka shi a matsayin hanyar rayuwa.
Duk wani musulmi na gaskiya ya yi Allah-wadai da mummunan harin da 'yan ta'adda suka kai a lokacin wasannin tsere na birnin Boston a kasar Amurka. Da farko dole mu jaddada cewa musulunci ya haramta duk wani aikin ta'addanci da farmaki. Alkur'ani, wanda shine tushe kuma mabubbugar tsarin musulunci, cike yake bayanai akan wannan al'amari.
Wannan hari na 'yan ta'adda, wanda kuma ya jawo salwantar rayukan mutane uku da kuma raunata daruruwa, aiki ne na dabbanci daga batattun mutane jahilai da aka kai da nufin haddasa rikici tsakanin kasashen Turai da kuma al'ummar musulman duniya. Irin wannan aika aika an sha yin ta a kasashe da dama don a nunawa kasashen Turai cewa musulunci addini nd da ya daurewa ta'addanci gindi. Har ila yau, hare haren 11 ga Satumba wanda aka kai a Amurka, sun nunka wannan a muni da tsanani. Jim kadan da kai wadancan hare hare, sai mutane da dama – da suka hada da wasu 'yan siyasa da shugabannin addini – suka fara fitar da jawabai cewa Mulunci addini ne da ke goyon bayan ta'addanci; wasunsu ma har kira suka yi da a daura yaki da kasashen musulmi. Saboda haka za a iya cewa ta wata hanya wadannan hare hare sun yi nasara. A yau muna sauraron jawabai daga masu kin musulunci, 'yan ga-ni-kashe-ni da wasu kafafen watsa labarai a kasar Amurka suna iza wutar kai hari kan Musulmai da kuma ware su daga cikin al'umma. Muna fatan jama'ar Amurka za su nisanta kansu da wadannan jawabai na duhun kai ta hanyar gane cewa yunkuri don tada wutar fitina a tsakanin al;ummun duniya.
Akwai ayoyi da yawa a cikin Alkur’ani da suke karfafa soyayya da son juna. Wannan bayani daga aya ta 159 a cikin Suratu Al ‘Imrana, “…Saboda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su…” tana bayani karara cewa Musulunci ya ginu akan tausayawa da kyautatawa mutane.
Duk wanda ya ke ikrarin musulunci sannan ya zo yana cewa wai addinin ya halatta ta'addanci ko tashin hankali, to ko dai an turo shi ne da nufin ya bata musuluncin ko kuma kungurmin jahili ne da bai san komai a addinin ba. Mutumin da ya yi wadancan kalamai cikin jahilci zai iya tuba ya canja ra'ayinsa idan aka karanta masa ainihin abin da Alkur'ani ya koyar. Z a a iya koyar da mutane addinin musulunci ne kadai matukar ba a maida hankali wajen tunzura jama'a ba. Idan kowa ya san cewa musulunci ya ja layi tsakaninsa da ayyukan tashin hankali da nuna kiyayya to babu wata dama ga masu nufin bata addini ko 'yan ga-ni-kashe-ni da za su fake da ita.
A tsakanin kiristoci da yahudawa akwai mutanen da ke neman haddasa da yaki akan musulmi, haka kuma a tsakanin musulmin akwai masu kokarin haddasa gaba akan Kiristanci da Yahudanci. Wadannan mutane 'yan tsattsauran ra'ayi ne masu tsananin kiyayya da ke fitar da maganganun tunzurawa ba sa jawo aya daga Alkur'ani, sai dai su kawo hadisi wanda shi ma suka yi masa muguwar fassara. Wannan ba karamin al'amari ba ne da ke ci wa duniyar musulunci tuwo a kwarya, don haka ba za mu kauda kai mu kyale shi ba. Duk Musulmai na kwarai suna takaicin ganin yadda ake yi wa wadannan mutane kallon musulmai kuma masu magana da yawun addinin saboda sun san cewa ba abin da ya hada wadannan mutane da koyarwar Musulunci. Sun cire dabi'u irin su soyayya, kyautatawa da kuma tausayi daga zukatansu. Ba abin da ke cikin ransu ban da kiyayya da fushi, ba wai kawai akan mabiya sauran addinai ba, har ma da mafi yawan musulmai daga sauran dariku. Suna tsanar mutumin da ba su taba gani ba kawai saboda ba a cikin kungiyarsu ya ke ba. Wannan baudaddiyar fahimta ce akan Musulunci.
Haddasa gaba tsakanin mabiya addinai ko kabilu daban daban tare da iza wutar rikici a tsakaninsu wata dabara ce da wadanda ke neman tayar da yaki a duniya suke amfani da ita a tsawon tarihi. Sai dai wannan duniya ta kasance yalwatacciya mai albarka da kowa zai iya rayuwa cikin farin ciki, aminci da kuma walwala. Babu wani dalilin haddasa rikici da tayar da hankali. Duk wasu dalilai da ake kawo wa don haddasa yaki da rikici duk karairayin banza ne marasa tushe.
Zaman lafiya da son juna ya fi matukar sauki akan rikici da yaki. Alal misali, ba son Falasdinawa ko Isra'ilawa ba ne su cigaba da zaman dar dar bayan dogwayen katangu kullum cikin tsoron harin bam, roket ko wani nau'in makamin. Halin da wadannan al'ummu biyu suke ciki, daya zuriyar Annabi Isma'ila ce yayin da dayar kuma daga Annabi Ya'kub (amincin Allah ya tabbata garesu), ba karamin abin kunya ba ne akan duk mutanen duniya.
Fatanmu shine wata rana wadannan mutane masu tsattsauran ra'ayi za su gama yayinsu su ba ce cikin sassaukan ra'ayin soyayya da girmama juna na mutane masu hankali da tunani (a tarihi, yawanci kungiyoyin 'yan tsattsauran ra'ayi sukan bace ne ko kuma su rusa kansu da kansu), amma in har ana son faruwar hakan to sai mutane masu hankali a cikin Musulmai, Kiristoci da kuma Yahudawa sun hada kai sun yi aiki tare. Ana bukatar hadin guiwar mutanen kirki. In kuma ba haka ba, Babu yadds za a ga bayan ta'addanci da sauran ayyukan barna a duniya.
Allah Yana kira zuwa ga gidan aminci, kuma Yana shiryar da wanda Ya so zuwa ga tafarki madaidaici. (Alkur'ani, suran10, aya 25)
15. André Miquel, L'Islam et Sa Civilisation VIIe - XXe siècle, Librairie Armand Colin, Paris 1968, p. 244
16. Gesta Francorum, or the Deeds of the Franks and the Other Pilgrims to Jerusalem, translated by Rosalind Hill, London, 1962, p. 91
17. August C. Krey, The First Crusade: The Accounts of Eye-Witnesses and Participants, Princeton & London, 1921, p. 261
18.August C. Krey, The First Crusade: The Accounts of Eye-Witnesses and Participants, p. 262
19.Alan Ereira, David Wallace, Crusades: Terry Jones Tells the Dramatic Story of Battle for Holy Land, BBC World Wide Ltd., 1995.
20.The Pact of Najran, Article 6, http:// www.islamicresources.com/Pact_of_Najran.html