Marubucin, wanda yake rubutu a karkashin sunan alkalami HARUN YAHYA, an haife shi a shekara ta 1956.Bayan ya kammala karatunsa na firamare da sakandire a Ankara, sai ya tafi Jami`ar Mimar Sinan a Istanbul yayi digirinsa, sannan ya sake yin wani a fannin falsafa a jami`ar Istanbul.Tun daga 1980, marubucin ya wallafa littattafai akan siyasa, da wadanda suka shafi imani da kuma sha`anin kimiyya. Harun Yahya sanannen marubuci ne wanda ya rubuta muhimman ayyuka dake bayanin yaudarar ma`abota (evolution) juyin halitta, rashin gaskiyar da`awarsu da kuma bakar alaka dake tsakanin Darwin da munanan akidunsa.
Sunansa na alkalami ya kunshi sunaye guda biyu Harun da Yahya, don tunawa da wadannan manyan annabawa, wadanda suka yaki kafirci. Hatimin manzon Allah dake bangon littattafan marubucin yana da ma`ana da take da alaka izuwa abinda yake ciki. Hatimin kansa yana wakiltar Alkur`ani ne a matsayin littafin karshe wanda Allah ya saukar kuma kalmomin karshe daga wurinSa, sannan annabinmu shine cikamakin annabawa. Akan tafarkin shiriyar Alkur`ani da sunnah, marubucin ya sanya wannan ya zama shine nasararsa don karyata dukkanin akidu da fahimtar marasa addini, da kuma daukaka "kalmar karshe", saboda a cika bayanai akan kare martabar addini, da kalubalen da ake yi akan addini. Hatimin annabi, wanda ya kai kololuwar hikima da cikar dabi`a, ya zama shine alamar manufarsa ta fadar wannan kalmar karshe.
Dukkan wadannan ayyuka na marubucin sun tattara ne a cimma manufa guda daya: Isar da sakon Alkur`ani ga mutane, don karfafa musu gwiwar yin tunani akan abubuwan da suka shafi imani, kamarsu samuwar Ubangiji, kadaitakarsa, tashin kiyama, da kuma bayyana illoli ginshikai da watsatstsun ayyukan maguzawa.
Harun Yahya na samun karuwar makaranta littafinsa a kasashe da yawa, daga India zuwa America, England zuwa Indonesia, Poland zuwa Bosnia, daga Spain zuwa Brazil. An fassara wasu daga daga cikin littafinsa zuwa harshen Turanci, Faransanci, Jamusanci, Italiyanci, harshen Portuguese, Urdu, Larabci da Albaniyanci, Rashanci, Serbo-croat (Bosnia), Uygur Turkiyya, da Indonesia, kuma makaranta sun gamsu dashi a duk fadin duniya.
Babbar gamsuwar da aka samu ko`ina a duniya, ya sa mutane da yawa sun bada gaskiya (iman) da Allah kuma wasu da yawa sun zurfafa tunani cikin imaninsu. Hikima, gaskiya da saurin fahimta shine salon da yasa littattafan suka yi fice, wanda shi yake jan hankalin duk wanda ya karantasu ko ya jarraba duba su.Ga su basa samun suka saboda irin tsarin da suka taho dashi don yada gaskiya, tabbataccen sakamako da samun karbuwa. Ba kamar wadanda suka karanta wadannan littattafai kuma suka cusawa kansu wani tunani wanda ba zai taimaka musu wajen yada wannan sako, don rushe falsafar jari-hujja, maguzanci da duk wata akida ko falsafa ba. Koda zasu taimakawa wancan tsari. Duk wata kungiya a yau an kureta, madallah da littattafan Harun Yahya.
Babu shakka wadannan dabi`u sun bayyana ne daga hikimomin Alkur`ani. Marubucin dai bai taba jin wani alfahari akansa ba, yayi nufin wannan aiki ne don neman kusanci izuwa tafarkin Ubangiji. Haka kuma, ba`a nufaci samun wata riba akan wadannan ayyukan buga littattafan ba. La`akari da wadannan dalilai ne yasa muka ga cewa wadanda suke kwadaitar da mutane akan karanta wadannan littattafai, wadanda suke buge idanun zuciya da shiryarwa akan su zama bayin Allah na kwarai, sunyi aiki mara iyakar lada.
Bayan haka, zai zama bata lokaci da lafiya don yada littattafan da suke kawo kokwanto a zukatan mutane, da kai mutum cikin akida ta hayaniya, kuma da rashin karfin dalilan da zasu cire kokwanto a zukatan mutane, wanda ya zama abin sani da irin abinda ya sha faruwa a baya. Koda yake abu ne mawuyaci kaga an rubuta littattafai don kawai a yi ta bayanin kwazon marubuci, maimakon tsamo mutane daga bata ya zama shine muhimmin aikinsa, tare da samun tasiri babba.Wadanda suke kokwanton haka zasu gani a fili cewa littattafan Harun Yahya, suna kawar da bata da shiryarwa izuwa kyawawan dabi`u daga Alkur`ani.Nasara da tasirin dake tattare da wannan aiki ya bayyana daga sha`awa da shakuwar makaranci.
Abu daya da yakamata a kudurce a zuciya shine: Babban dalilin da ya haifar da cigaban rigingimu da kashe-kashe, da duk wahalhalun da musulmi suke fuskanta shine akidar kafirci wadda ta yadu. Za`a iya kawo karshen wadannan akidoji ta hanyar kuresu da dalilai da kuma tabbatarwa cewar kowa ya san abubuwan mamaki daga halitta da tarbiyyar Alkur`ani, don mutane su rayu akanta.Idan ka dubi halin da duniya take ciki a yau, ka ga abubuwan da suka jefa mutane cikin rigingimu, cin hanci da rashawa, ya bayyana cewar dole ne a samar da irin wadannan ayyuka a cikin sauri kuma masu inganci.Idan ba haka ba, to zai zama an makara sosai.
Babu shakka cewar littattafan Harun Yahya sun ja ragamar wannan mukami. Da ikon Allah, sai wadannan littattafai sun zama tafarki wanda ta hanyarsu mutane a karni na ashirin da daya zasu samar da zaman lafiya, albarka, adalci da farin cikin da Allah ya alkawarta.